← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 83

Sashe 12

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dif maganarta ta dauke, sakamakon abinda ya rubtu a idannuwanta, jifan da ta yi bata taba tunanin hannunta zai kai bayan madubin motar ba, dutsen kansa bata taba tunanin ko goshi ya daka zai fashe ba bale motar, itafa a da sai ta jima tana jifan wajen da kadangare yake ama da kyar take iya korarsa bata samunsa, sai gashi a yau wani tashin hankali jifan nan daya kamar ita fin jikar mahalba ce ya sauka a bayan motar nan da ta tabata ko kudinta aka yi ba zata kai kudin motar ba ya fasa madubin bayan motar

Bata ji cikinta na neman hautsinewa ba sai da ta ga motoci biyun sun tsaya, lokaci daya kuma ta ga sun shiga yin baya baya a hankali

A tsayen da take ta yi mutuwar tsaye, bata yi aune ba ta tsinci muryar Gali yana fadin" Kan uba, motar Jikan Mai Shanu kika daka yau Amina? WALAHI na tafi ni kam na yafe watsa kwatar da aka yi min, menenema a su kwata Allah na tuba"

Da sauri ta sado dubanta jin Husaini yana jan hijabinta da karfi , bata yi wani aunen ba hijabin ya janye gaba dayansa ya sauka a wuyanta domin dama wuyan ya mata yawa dabara ta yi da tudun gahinta ta zaunar da hijabin dan ta san babu abinda zai kawo fitar hijabinta daga kanta lafiyar Allah

A kidine, zuciyarta na dokawa ta dago jin innuwar motar da hucin tsayuwarta a gabanta
Walahaula wala kuwata ila bilahil aliyul azim, Hasbunnalahu waniimal wakil, Wannan wani irin tashin hankali ne? Kudin jikinta dududu basu fi naira dubu goma sha hudu ba, a haka jinta take tamkar biloniya kwana biyun nan, ji take yi idan da waye zasu iya karawa domin aljihunta da nauyi, shagwaba ƴaƴanta take yi da kayan dadi dan idan ta laluba ta ji cukus sai ta ji hankalinta ya kara kwonciy, itace shinkafa rabin buhu, makaroni kwali, man kuli da na ja, harda su katihun kayan makulashe na biyu alewa da tuwon madara , sai ga mai samu ta sameta rana tsaka

Motar dake gaba ce aka bude aka fito da sauri aka zagayo wajen motar dake daf da itan
Mutane hudu ne suka fito din, ukun na sanye da suturar dake nuni su din masu ba sauran kariya ne, kamar Bodyguard haka, dayan kuwa na sanye da simple shiga ta malan bahaushe ta kama jikinsa sosai ta amshi jikinsa

"Subahanalah, subahanalah, ashe ruwan tabo ne a wajen nan bamu sani ba? Ya salam baiwar Allah ki yi hakuri mun watsa maki ruwan nan ba da gangan muka yi ba" wannan bawan Allah da ba zata mantashi ba a kampanin siyar da kayan abinci wanda ya biyosu da kayan abincin har waje ya sa suka amsa yake fada yana sake jadada hakurinsa cike da kula

Mutuwar tsaye kawai ta yi, a lokacin ne kuma yake dakatar da masu basu tsaron da suka so nufarta yana mai umartarsu da su koma mota su yi jira, lokaci daya ya shiga dan leka Husaini dake boye a bayanta sai kuma ya kalli hasan dake tsaye ya hade gabas da yama tamkar wanda yake jir a kara taku daya kusa da mamansa ya kifar da mutun

Murmushi ya sauke a sanyaye ya ce" Ashe maman twins ce?, Sorry ina zuwa"
Yadda ya fadi sorry yana zuwa din, da hakurin da ya fito ya ringa bata ya sakata sake daskarewa ta bishi da kallo tana dora hannunta na dama a hankali saman kan Hasan dan so take shima ya dawo jikinta ko hankalinta zai kwonta, idan kashe su ne za'a yi a kashe su tare

Gefen da yake ya bude a hankali ya shiga sannan ya sauke gilas din motar daga baya gaba daya yana kallonsa a hankali ya ce" Me yasa muka tsaya ne? Ka ga fa mune bamu da gaskiya duba ka ga jikinta da yaranta gaba daya datin ruwan kwatar nan ne muka watsa masu"

ABDUL RA'UF ya dan kalle shi a hanzarce ya cire dubansa ya ciro tissu din dake aljihunsa ya dan tare gaban hancinsa kadan da ya ji danshi danshi alamun habon dake masa yoyo du idan gari ana zafi ke son bale masa, kasa kasa sosai ya ce" Allah ya isa ta yi, ka kuma san bana kwonciya da hakin wani in dai na san da shi ko??"

Dama ya san rigima ce ta dawo da ABDUL RA'UF wajen nan, ya san ba dai dan ya bata hakuri ya ja ya tsaya ba, dan haka ya shiga kokarin ganin sun bar wajen ba tare da ya nuna hali a anguwar nan ba, dama duba jikin Hajia zasu je, jiya tace idannuwanta dai sunna gannin biyu biyu kuma kaffafuwanta sunna daukan mijirya, tun a jiyan ya so su zo sai Allah bai yi ba dole sai yau, sai gashi sun sake haduwa da maman yaren nan , haka kawai yake jin yaren a ransa, bai san dalili ba, yaren na matukar shiga zuciyarsa, ko dan shi bai samu haihuwar ba har yanzu ne? Ko a wancen ranar sai da kyar aka bashi hakuri ya bar maganar a cire ma'aikaciyar nan a cenza da wada ta san darajar dan Adam, sosai ya ji zafin abin a zuciyarsa, a nutse ya shiga fadin " Ban san a kan me direbobinka suke irin tukin nan ba ABDUL RA'UF, ka ga fa ai an shiga hakinta shi yasa ta yi magana fa"

Yanzun kam a kausashe ya dube shi , zai kuma yi masa magana sai kawai ya daina ya saka hannunsa ya bale marfin motar ta gefen da ba'a fita , watau hanyar da wasu ababen hawan ke wucewa bai tsaya ya duba masu wucewar ba ya fito ya rufe hankali kwonce ya zagayo ta dayan barin

Da sauri Docter Mansur ya bale gefensa shima ya fito ya karaso wajen da ABDUL RA'UF ya karaso ya ja ya tsaya kikam a kanta

A hankali yake son kwatanta masa cewa mutane fa sun fara tsayuwa kallonsu, a hankali sosai ya ce" Calm down Man, plz let's go, kar ka yi wani abin a wajen da ake gannin mutuncinka"

Amina dake rike taf da hannun Husain da ya fara kuma yana fadin" Wayo Allahna za'a zane mu"
Hasan kuwa sai huci yake zuciyarsa na yin sama tana yin kasa irin kirjinsa na daguwa yana yin kasa shima yana kallon Tsayin Docter mai kirki ko kafadar wannan mutumen bai kai ba
A hankali ta dan matsa kadan, gaba daya ji take ya yi mata innuwa haka kuma hancinsa har kamar mura zata kamata sanadiyar matsewa kanshin turaransa guri da ta yi

Bata idasa ajiye kafarta ta baya ba ta ji muryarsa for the first time a dake, sannan a rarabe, haka kuma a ajiye daidaya ya ce" *KE? BAKI DA KUNYA KO?* "

A haukace ta dago dubanta ta sauke idannuwanta cikin nasa, da matsanancin mamaki ta budi baki zata yi magana, sai dai bata kai ga yin ba ya katse mata abinda ta yi niyar fadan yana fadin" Ki tauna harshenki, ban san idan har zan iya cinye shirme yau ba!"

Ya Allah, innalilahi, ita? Yanzu yaron nan ya dubeta ya dubi tsabar idannuwanta da girmanta, da darajarta, da mutuncinta, da ƴaƴanta yace da ita bata da kunya? Lamarin sangartatun yayan masu kudi abin sake hauhawa yake yi, idan ba rashin kunya da karancin tarbiya ba ya dubeta ya ce da ita bata da kunya? Ai yau idan me yake takama sai dai ya yi, walahi sai ta nuna masa ita bata daukan raini!

"Kai kana da ita kunyar ne da zaka dubi idannuwan wanda ya girmeka ka ce da shi baya jin kunya? " Ta fada a tsitsikare, sannan a rarabe tana fada tana sake cire dubanta a kansa da matsawa domin tunda ta budi bakinta ya yi taku daya ya sake matse mata waje

" Dan Allah, kar ka yi, ka duba yarenta sun rikice, duba wannan yana ta kuka, kuma idan matar aure ce yau matar aure zaka biya? Plz freind" Docter Mansur ya fada da sauri yana taro shi a lokacin da ya dago hannunsa da nufin yin abinda shi kadai ya san ko menene yake shirin yi
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️

*NA*

*SAJIDA NIGER*

Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida

Wannan Novel na kudi ne ba free bane

Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER

Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai

Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka

*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*

*Page 0️⃣8️⃣*

A hankali ya sauke dubansa a kan Hasan
Irin yadda yaron yake yi sai ya saka shi sake kura masa ido
A hankali ya damu kansa da jin kamar zai yi murmushi da yannayin yaron a cen kasan zuciyarsa, irin kallon da Hasab ke yi masa tamkar zaki yana jira ya taba masa uwa ne ya far masa
Sake kallonsa ya yi da kyau ya ga idannuwansa sun cika da kwala sosai fa, ama ya cije ya ki bari su zuba
Wannan din shine mafarkinsa, shine burinsa, idan ya haihu yayansa su zamto jarumai ba akoki ba
Yan so ya'yansa su ringa dukan yara ba wai a ringa dukansu ba
Chapter 12 · 0% Book details