← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 83

Sashe 31

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A sanyaye ta ce" Baba, banfa samu isashen barci ba jiya"

Baba ta yi murmushi ta ce" Ai rabonki da barci tunda aka aura maki Mala"

Kanta ta dago tana kallon Baba ta ce" Baba jiya fa Hajia tace yau tana son ganina karfe goma na safe, kina tunanin takardar sakina ne zata bani?"

"Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallama ke wannan ya, wani irin takardar saki kuma?"

Amina ta yi tsuru tana kifta idaannuwanta

Baba Lauratu da takaici ta ce" ta isa ta baki takardar taki ne kike zaune a gidanta har yanzu? , Ke bakinki yaushe ya fara furta alkaba'inema ban sani ba?, Auren nan du ya mayar da ke wata shashasha bayan abu ne ya same ki sai dai in mutuwa kika yi zai sauka a wuyanki da izinin mai duka bayan mijin nan da kika raina ya saka ki a kabarinki, Ke Amina ki fa kiyayeni fa, walahi ki ji da kyau du wani wanda zai ja da ikon Allah sai dai a yi ba shi, kin ga auren nan da aka tashi daura shi irin yadda ya kawo rigingimj kuma Allah ya tsaya a daura shi ko? To du wanda yace ba zai gani ba sai dai kasa ta birni idannuwansa, wai wani takarda aa ranki zata baki a hannunki karshen kiyaya!"

Amina kam sai ta ja bakinta ta yi gumm, yanzun har dungurinta Baba ke yi, bayan a da bata daga mata muryama da rarashi da komai take binta

Abinda ta fi tsana ne ta hada mata watau ruwan lipton mai zafi aka kada masa kwai da madarar peak ra miko mata tana hade fuska ta mata tsaye a kai, sai da ta shanye ta yi bayi da gudu dan kuskure baki zuciyarta na tashi, takaici n cikata Babar ta bita da kallo tana tabe baki ta ci gaba da hade haden abinda ya dace tana ajiyewa dan haka take yi mata yau kwana hudu kennan ba ji ba gani kayan gyara da na sanyi dibgarsu take kamar ba gobe

Tana dawowa ta tarar da sauran kayan ta zauna ta sha , domin ta dan ciwon da ba zai barka bane gwara ya kasheka ka huta, uwa uba ita ta san aikin banza ake yi, wannan shaye shayen na banza ne, dan ta san ko gawarta abar kunya ce a gaban Abdul bale ita da ranta, ai baba sai baba walahi!

Baba Lauratu ta ajiye mata hijabinta sabo mai tsafta, dudu bai fi sakawa biyar da ta yi masa ba tana kallonta ta ce" Ki kimtsa ki je, goman ta wuce ina nan ina jiranki"

Jiki a sanyaye ta dauka ta saka kayan ta dan fesa turare kadan a hamatarta dan ta ji dadin zama

Baba Lauratu ta ambaci sunnanta

Dakatawa ta yi ta dawo daga nufin fitar Baba ta ce" ki sani, farkon fara mu'amalarki da kakar mijinki ne, dama ban sanki da raini ba, ama a yadda abin nan ke bin keyarki komai kina iya aikatawa........dan haka nake gargadinki da ki kula, idan me zata ce da ke ki tauna amsar da ta dace da ita kafin li bata, ba hakan na nufin ki je a wulakanta ki ba!, Komai talaucin bawa idan ya bada dama za'a wulakantashi, baki zo gidan nan dan roko ba, hasalima baki taba takowa kika zo dan a baki gero ba, a yau da kuke zaune da daraja a kanki mafi girma a cikin darajoji, yin biyaya wajibi ne, haka kuma kare mutuncin kanki wajibi ne a gareki, ki kula Amina"

Amina ta gyada kanta a sanyaye ta fita din

Ashe mai aiki na zaune tun karfe goma tana jiran fitowarta, bata yi gigin shiga bane dab tunda aka daura aurenta Baba ya fada masu wacece ita yanzun a gidan, matsayinta yana da girman da basu isa su shige dakinta kai tsaye ba, Hajia ta turota tunda safe ita kuma sai ta zauna take jira har ta fito sai ta sanar mata sakon

A mutunce suka gaisa, ta mike ta yi gaba fan nuna mata dakin domin hakan ne umarnin Hajiar

Sun jima a kofar dakin sunna jira bayan sun buga an masu gyaran murya, har sai da aka basu damar shiga sannan suka shiga

Gaba daya kanta so ya yi ya rikice a lokacin da suka dakin da yake ainahin na barcin Hajiar ne
Daki kamar ba'a shiga cikinsa? Tsafta, kanshi, tsari abin ba'a magana

Hajiar na zaune saman kujera ne cikin shiga ta shada ta kafa daurinta irin na manyan mata , ba kwaliya ko diz a fuskarta ama sai walwali fatarta mai hasken duhu take yi tsabar gyara da hutu ga shan madara (😌)

A hankali Amina ta raka mai aikin da ta rakota tamkar zata bi bayanta da gudu ta rukunkumeta su juya tare

A sanyaye ta sake juyo dubanta a lokacin da Hajia ke kare mata kallo tun daga sama har kasa, ba zaka taba gane yaya yarinyar take ba dan wannan jarababen hijabin dake janta tamkar zai kayar da ita, kulun a cikinsa tale, ba dare ba rana, ko a cikin gida ko a waje!, Shirmen banza wannan abar ce za'a hada jikanta da ita? Ai ba gami sam

A nutse ta zauna a wajen da ta nuna matan, watau saman cafet, ya zamto ita Hajiar tana sama ne saman kujera kafarta daya kan daya, fuskarta a hade, ita kuma tana saman lalausan cafet din falon dan nesa kadan fa wasu tarin akwatunna kanta a sade a kasa

Hannayenta dake fili Hajia kw kallo, wa'inda take dan murza su a hankali wanda hakan ya nuna mata cewa lalle tana dauke da strss wanda take son controlng a zaunen da take

Bakinta ta tabe , a kadan ta dauki mintunna biyar tana sake karantar Amina

A bayane yake Amina mahaukaciyar Black beauty ce, bama irin hancinta da ya tafi a mike zuwat ya sauka dan daidai kusa da labanta, manyan idaannuwanta masu hasken fari da duhun baki sidik na ciki, sai habarta mai dan tsayi kadan sannan daga tsakiyarta ta dana bile kadan
Batada cikar kumatu irin kubulbul din nan, kuma batada ramar fuska, gaban goshinta kuwa kan iya sheda maka da ba zata rasa gashi mai kyau ba dan gayanan yana nuna kansa duda kindime shi da ake yi

Sakw tabe baki ta yi a hankali, cike da iya sarafa harshe da basarwa ta ce" Wace fuska kika ba wannan hadi ne?"

Sai da ta sake maimaitawa kanta tambayar har ta fahimta sosai , sannan ta dago a sanyaye ta dubi Hajiar cikin ido a sanyaye ta ce" Bakuwar fuska ce "

Hajia ta dan kawar da kantan nan ta sake juyowa tana kallonta ta ce" Wace kike maraba da ita ? Ko kike hangen rashin dacewarta?"

Yanzun sai da ta ji kamar ta bada amsar a zake, watau da zakuwa, sai dai ta dab kiyaye yanzunma ta bada amsar kamar yadda akai mata tambayar, a hankali ta ce" Ba cencenta, sam abin boyewa ne a wajena Hajia"

Da mamaki Hajia ke kallonta, so take ta fahimci iya gaskiyarta kennan ko bariki zata nuna mata?

"Idan hakan ya zamto tarihi ne, ina nufin abinda bai dauki lokaci ba ya shude zai dame ki kuwa?" Hajia ta fada ta a karra dubanta sosai da son idasa gane nufinta

Sosai ta yi yaki da dukan abinda yake tare da ita dan hanna kanta sakin murmushin dake ciyota na farin cikin gannin adu'arta ce zata karbu, watau dai Hajia zata salameta ne?
Da kyar ta iya hanna kan nata yin dariyar ko sakin kayatacen murmushin a hankali tace" Idan har hakan ne zabin da na barwa Allah, farin ciki ne in sha Allah Hajia"

Tap, lalle a bayane Hajia ke karantar kamar yarinyar nan itama bata son auren nan, sai dai wani bari na zuciyarta ya shiga fada mata magana kamar haka' ta yaya kike tunanin zata fito maki a mutun ta nuna maki bata son abinda ta bi wani tudu ko wani gangare ta same shi bayan ta san bakya son hakan?, Ai dole zata boye maki dan a zauna lafiya, sai dai ta makaro, ita dinta ba'a so ba komai ba!'

Hajia ta basar, ta dubi agogon hannunta na azurfa mai kyau dan karami ta sake fuskantar Amina ta ce" Na saka ki zi ne dan ina so mu yi magana da ke, ina so ki samu alkali ki nuna masa amincewarki da auren jikana, watau kin yarda ya auri yarinyar da yake so, ina so ki nuna masa cewa shi ya maki maganar ke kuma kin amince da hakan, "

Kallon da Amina ke yi mata ya dakata itama kureta da kallo, kallon take son fahimta ko na menene? Sai dai bata gane ba, dan haka ta ci gaba da magana kamar haka" Amina, ke kin san ke din ba zabinsa bace, haka kuma ba zaki taba amsa abubuwan da ake da bukatar ki amsa dan huce takaicin zama matar gwamna ba, ABDUL RA'UF yanada yarinyar da suke soyaya, sun shirya kansu ana shirin aurensu maganarki ta bilo, a yanzu da kika samu hakan ina tunanin zaki yi masa adalci shima ya samu tasa wace yake so"

'waye ya ce maki jikanki shine abinda yake gabana?, Waye yace maki aurensa ko rashin aurwnsa ya dameni ne? An fada maki inada casss da abinda ya tsarawa rayuwarsa ne? Ko an fada maki ni din macen siyasa ce?, Hajia, dama zaki dubi maraicina, ki dubi karamin karfina, ki saka jikanki ya salameni, da kin rufan asiri duniya da kiyama kin kuma samu lada, domin bana tunanin zan taba yiwa kannin bayana *LADABAIH!*' wannan furuci shine Amina ke kokowa da shi a cikin zuciyarta da kuma kirjinta, sosai ya danne mata kirji yana son falasa kansa ama ta ki bashi dama ta rike shi da dukkan karfinta, bata so ya tonata ya saka ta raina baba, bata so ta yi abinda Baba Lauratu ta hanneta duda tunda ta zauna a wajen bayan ciwa kanta mutinci babu abinda ake yi

Hajia ta dora da fadin"
*NZL PAGE1️⃣8️⃣*

Tunda ya shigo gabanta ya kwonci kwonci ya fadi sakamakon abinda ta gani a rungume a jikinsa
Chapter 31 · 0% Book details