← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 83

Sashe 33

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai alamu sun nuna sam bata da niyar tausasawa, ita fa dama so take yarinyar ta ji, bata san a bayan kwarya take zuba ruwa ba, dama ace Husaini ne a wajen da ttsaf zai fadawa mamansa, ama hasan? Sai dai ya kulaceta , ba zai taba kaiwa mamansa maganar ba

A hankali ya ce" Boy, je kofar daki ka yi jirana ka ji?"

Hasan ya gyada kansa ya mike a hankali ya fice a dakin
Hajia ta juyo tana fadin" Waima meye hadinka da yaron nan ne? Meye hadinka da shi a ina ka ganshi ka dauko shi? Ka ga ABDUL ka kiyayi abinda ya shafi yarinyar nan, ba kai ba ita ba ƴaƴanta, ina dalili ka sungumi yaron nan har kirjinka ya amsa?, Naa hanna ka, na rabaka da ita ka ji abinda na fada maka!"

Bakinsa ya tabe yana girgiza kansa, to shi fisabililahi mema ya kawo maganar wani an hada shi da ita ko an raba shi da ita ne? Wannan duka ba matsalarsa bane, matsalarsa daya ne tak a kan wai shi ya je ya nemi izininta dan zai karra aure? Lalle kakansa ya dauko da zafi

A kausashe ya ce" Me yake nufi da ni ne?, Ni zan je na nemi izinin yarinyar cen a kan maganar aurena?, To a fasa auren mana!"

Hajia ta dafe haba tana kallonsa ta ce" Auren za'a fasa? Kennan ta ci galaba a kanmu baki daya, ina fada makaa yarinyar nan isashiya ce ta san abinda ta taka, tunda ta zo gidan nan bata taba takowa ta gaisheni ba dan ta san mai gidan na darajata fiye da ni!, Ka ga za'a yi magana da ita!"

Ido ya zarro yana kallon Hajia, cece kuce dinta shi du ba shine a gabansa ba, idan ya ji ana neman dangantashi da zuwa ya nemi shawarar mace kan auren da zai yi ke kular da shi

Hajia ta ce" ni zan ganta!, Zan bata abinda take kwadayi, wanda na tabata a kansa ta nace babar banza har ta auri kannin bayanta, zata amince ne da kanta, ka bari a yi auren ni na san yadda zan yi da ita!"

Dan karamin tsaki ya yi yana mikewa tsaye ya dauki takardun nan dake ajiye ya dubi kakarsa ya ce" Allah ya bamu alkhairi"

Hajia ta amsa shi tana sake jadada masa fita a harkar yarinyar da ƴaƴanta, sannan ta fada masa kar fa ya yiwa Alkali fushi, yana yin abubuwan nan ne ba a cikin hayacinsa ba, ita ta sani

Shi dai ficewa ya yi a dakin ya shiga saukowa kasa

A kusan hawa na karshe ya same shi a zaune ya jinginar da kansa a jikin karfe

Zama ya yi shiga a wajen bai ko duba suturar jikinsa ba ya yi shirun shima

Sun jima a haka, har sai da ya samu ya ji fushinsa ya ragu sosai sannan ya bude takardar dake ninke ya sake zuba idannuwansa yana nazarta

A bayane ya fahimci dalilin da ya sa mahaifiyar yaron ta dake shi
Shima abin ya dan bashi mamaki, dan haka ya dube shi wannan karron da yaren turanci ya shiga yi masa magana dan yana so ya fara nazartar yaron ya ce" Ama, kana kallon ina kai ka dauki wannan sakamakon, dan uwanka ya dauki na farko?"

Ga mamakinsa, da yaren da ya yi masa magana, da shi yaron ya bashi amsa tamkar yaren shine asalin yaren haihuwarsa
Hasan da ya yi kalar zai fashe da kuka ya watsa hannayensa ya ce" Nima ban sani ba, kulun haka nake kawowa, kuma tare ake koya mana komai, kuma ni da na zo zan yi sai bana gannin komai, kulun kulun haka ne"

"Kamar yaya baka gannin komai?, Wani irin komai? Rubutun ko harda mutanen? Ko kana nufin baka fahimtar komai?"
ABDUL ya sake tambayarsa yana sake kure shi da kallo duda ya fahimci barci ne ke cike da idannuwan yaron

Hasan ya ringa tare kwalar idannuwansa yana ta kokarin fahimtar da ABDUL, domin damuwarsa ce da ta fi komai damunsa, sanadiyar wannan mamansa ke yi masa fada, a kan wannan ta sha yin kuka, ta sha zuwa makarantarsu ta yi ta tambaya, bata da hutu kulun tana koya masa, a gabanta yakan shanye komai ya fahimci komai, ama a aji ba hus ba gaba ba baya, shi yasa ta kasa fahimtarsa, har kuka take yi idan zata dake ahin fa tana dukan nasa tana yin kuka ne hakama dan uwansa
Du irin kwatancen da yake yiwa ABDUL yana kallonsa ne har yaron ya kifa kansa a gefen kafar ABDUL din yana ta shasheka ya ce" nima ban sani ba, nine jakin ajinmu fa, kowa yanada ilimi banda ni? Kuma Mama sai ta yi fushi saboda wannan"

Shiru ne ya biyo baya yana dan shafa sumar kansa mai nuni da rarashinsa yake yi

A hankali ya ce" zaka je aski ne mu tafi ?"

Dagowa Hasan ya yi ya zuba masa ido, Aski? Wani daban zai kaishi aski ba mamansa ba? Kulun kulun mamansu ke kaisu wajen aski , sai su tarda maza cike a wajen kowa babansa ko yayansa ya rako shi, ama su mamansu ce ke raka su

Abinka da yaro, da kuma abinda ya bashi sha'awa sai murmushi ya nemi kubce masa, a hankali ya ce" Ama idan Mamana ta yarda, kuma da Hasan zamu je ko?"

Shima murmushin ya yi yana dan kama kuncinsa kubulbul ya gyada masa kai

Hasan ya ringa gyada kansa , a hankali sai gashi harda nuna irin askin da za'a yi masu yana murmushi da kada kai ya ce" Nima a makaranta sai na cewa Huzaifa Muma dai Elhajin gidan Papy ne ya kaimu aski ba mamanmu ba ko?"

ABDUL ya sake sakar masa murmushi yana sake nazartar yaron
A bayane yake yaron yanada ilimi, sai dai shima yana son sannin dalilin da ya sa yaron ke dauko irin sakamakon nan har uwar ke dukansa kamar jaki!

Mikewa ya yi yana fadin" Mu je ko?"

Hasan shima ya mike din ya sauko sai dai ya ja ya tsaya yana kallon kofar dakinsu ya kasa bin Abdul din

ABDUL ya juyo yana kallonsa ya ce" Mu tafi mana?"

Hasan ya takwakwabe fuska a hankali ya nuna masa dakin ya ce" mamana, da Husainin fa?"

Hannunsa ya kai wajen habarsa ya kama yana kallonsa

Dawowa ya yi ya dan rage tsayinsa ya ce" Baka tsoro ta sake dukanka ne zaka koma wajenta?"

Hasan ya sada kansa , a sanyaye ya ce" Bata dukanmu fa, kuma wannanma da ta yi sai ta rarasheni ba zata kara min ba fa"

Haka kawai ABDUL ya ringa kallonsa yana nazartarsa

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Mu je na raka ka toh"

Kai Hasan ya gyada yana murmushi ya shige gaba ABDUL ya bi bayansa

Sake bude kofar ya yi a hankali Hasan din ya shige sannan shima ya bi bayansa

Gannin wayam basa dakin ya saka shi juyowa, sai ya gansu gefen kofar a zaune a kasa sun yi barci su dukansu,, Husaini a nanike da ita, ita kuma ta wani lankwashe har hijab din ya yaye gana barci da abin nan na fuskarta bata wanke ba

'ikon Allah ita kuma kawai kazama ce?' ya ayana a ransa

Wajen bed din ya nunawa Hasan , ya kuwa je ya kwonta yana hangensu

Dan gyarawa ya yi ya duka da nufin dauke husaini ya mayar da shi shima saman gadon idan ya so ita ta shekara a nan
Sai dai yana kama yaron da nufin dauke shi Husainin ya rukunkume Amina, wanda hakan ya farkar da ita a gigice kuma a tsorace ta saka ihun tsoro tana dadamke hannunsa hadi da cakumarsa lokaci daya tana fadin" Kwartttttttt

😂🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️😌 kwar me? Mun shiga uku mu dai😂😂😂😂😂😂

Salam alaikum😍😍😍😍😍
*NZL PAGE2️⃣0️⃣*

Hajia ta dora da fadim" Ki duba kayan nan, suturunki ne da na saka aka hado maki aka kawo min, zan dora da makudan kudi da kuma mota dan ki rarashi mijina a yi auren nan, ina so daga yanzu har a gama maganar auren kar ki zamo matsala a ciki, ki bada hadin kai a yi komai da ke, idan ya so daga baya ko menene sai a sake zama a warware abinda yake cikin duhu"

A sanyaye Amina da ta kasa kanta furta wannan furucin a yanzu ta dubi Hajia ta ce" Hajia, zai salameni ne?"

Hajia ta yi mata duban bata fahimta ba?

Sai a yanzu Amina ta fahimci abinda ta fada, dan haka ta ji nauyi da kunya na son lulubeta, harma ta kasa katabus

Muryar Hajia ta sakata dagowa a hankali tana kallon Hajia
Hajia ta ce" Ban fahimci maganarki ba"

Amina ta sake sada kanta, ta riga ta furta, dole ta bayana ma'anar furucinta,
A sanyaye ta sake dagowa , bata ko jin tsoron dakewar hajiar ta sake dubanya, ta kuma duban akwatunnan da suka firgitata, tarin alwatunnan da robobi manya dauke da takalma, a haka an yi abin ne irin jeka na yikan nan, ama ita gani take yi ta je ina da kayan nan? A sanyaye ta ce" Hajia, ni Uwa ce, na saba fita na kai yarana makaranta sannan na koma na dauko su, kafin na dauko su nakan zo na yi yan sana'a'o'ina irin gyaran amare da tuyar kosaina, na dakatar da karatuna dan jarabawar da zan zana a lokacin ban cike abinda ake da bukata ba, Hajia, kika ce za'a warware abinda yake cikin duhu, shine nake son sannin kina nufin idan aka gama maganar auren nasa, ni zai bani takardata ne? Dan na je na ci gaba fa tawa rayuwar kamar yadda na saba?"

A hankali ta ajiye maganar, sai kuma ta sake duban wajen kayan ta ce" Hajia, bama sai an bani kayan nan ba, walahi zan yi ba sai an bani komai ba, in dai zai bani takardar shikenan, a lokacin da Baban ya yi furucin sama min miji da ya alakanta haka da na nuna masa cewa ya bani datijo, ko dan yan yarana"
Chapter 33 · 0% Book details