← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 83

Sashe 58

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Audu ya ce" Kai fa saley kanada matsala, aishi wannan mutumen bama maganar kudin bane inaga, wannan bakin hali nasa sam bai masa rana ba, wai sai ace maza sunnada kishi basa so namiji ya bude masu mace ya amshi haihuwarta, ni fa nan da ka ganni da innar baban gida ta jigata gwara namijin ya amshi haihuwar tata, to Allah na tuba lafiyarta ai ta fi min komai a duniya"

Saley ya amshe da fadin" Kai kace, bale yanzu fa mata ke amsar haihuwar nan,mata ilimi suke yi sun amshe abin fa, maza kuwa su duba maza yan uwansu, dama in ba mai laluwai a hannu ba ina kai namiji kato ina karatun feraye matar wani? In ba so kake yi ka ringa shiga hurumin da ba naka ba"

"Ku dai kun shiga uku da bakinku walahi, kun ga sai maganar nan kuke tunda safe matayenku sun zigo ku kun zubawa kofarsa ido kun kasa aikata komai sai saka da warwara kuke yi, inace yanzu na gama maganar mu kai kara wajen mai gari a fitar da yarinyar cen a kaita asibiti kuka nuna aa aa wannan ba huruminku bane, sai da mutun ya zauna zaku saki baki kunna cakalkalarsa, idanfa dan uwansa ne?" Mubashir ya fada da dan fada fada, domin tunda safiyar juma'ar nan ta waye suke kan maganar nan, ama da Mudin ya fito siyan garin kwakin ashirin hannu hannu suka ringa bashi sunna gaisawa shi kuwa yana wani cire kai kamar wani tsiya, wai shi baya shiga hurumin yan anguwa baya son tsegumi, wani tsegumin kuma, na nawa? Shi kulun kamar zai hadiyi zuciya dan bacin rai

Audu ya kama baki yana yar dariya da jan hakorinsa a bakinsa ya ce" Karan uwan nana kaya, gacin uwanan kayasa, ai da mun shiga uku, to ama ai da wahala a dangin Mudi a samu mai fara'ar wanann, Elhaji ko ba haka ba?"

ABDUL da komai suke fada ke karra dan tunzura jinnin jikinsa , da kara fahimtar wa kanwar matarsa ke aure, da son shiga gidan kai tsaye ke karra shigarsa ya rafka tagumi yana kallonsu har suka dasa Aya ya mike ya yi masu salama ya tsalako ya shiga kai kawo yana duban kofar yana tunanin ba zai iya motsawa ba sai ya ji daga bakin Uman biyu

A cikin gidan fido

Rungume Amina take da Firdausi tana magana hankalinta tashe tana fadin" Tun yaushe kike yashe a tsakar gidan nan haka Fido? Ina makotanki? Fido ina Mudi yake?"

Firdausi dake numfashi da kyar tana sake rike hannun yayarta muryarta cen ciki ta ce" Aunty, wayo Allahna Aunty mutuwa zan yi, Aunty mutuwa zan yi , bana iyawa na gajiya Aunty, dan Allah ki yafe min zan tafi nima na barki da nauyi a kanki Auntyna"

A zabure Amina ta mika hannunta jikin kofar dakin ta shiga bugawa da wani irin karfi tana fadin" Kai Mudi? Mudi? Mudi? Ga takalmanka nan kana jina ga takalmanka nan ka fito Mudi kana jina?"

Wani wawan tsaki ya ja ya taso daga kwoncen da yake yana son yin barci, domin daren nan kwana ta yi tana hailala da kiran Allah shi du ya zatama ba zata waye ba a irin yadda take haukan nan, ta saka makota sai binsa da kallo suke matayensu yan saka ido sun kai masu gulmar gidansa ko? To baki daya daidai yake da uban kowa, inda ubanda ya isa dan Allah ya fito ya fitar da Firdausi daga gidan nan ya gani! Iskancin banza iskancin wofi yanzu yayarta ta zo shine zata wani langwabe ita ga kwalba sarkin shari ko? To ya fisu iya iskanci, wa suke da shi da ya tsaya masu a duniya? Wai wani Amina ta yi aure ta auri mai kudi, ai ko kudin ta aura yana nan a yadda yake zata dawo ne zaman anguwar yana jiranta!

Da tataciyar fuskar rashin mutunci ya bankade labulen tsuman atampa roba robar dake kare kofar ya fito yana jan ido ya kalli Amina ya ce"
Wani numfashi ta ja mai zafi, gaba dayanta ta sake lumshe idannuwanta a saman kafadarsa tana kallon fuskar jaririyar
Jikinta babu karfi ko kadan, muryarta cen ciki ta ce" Ka ga, mamaci sai fuskarsa ta yi fari fat haka, ko baki ne sai ka ga ya kara haske irin hasken rashin jinni"

A hankali ya kalleta, hakama doctors din

A sanyaye ya ce" Haka kamanin mamaci ke yi?"

Amina ta dago tana kallonsa, a sanninta shima ai nasa iyayen sun rasu ko?, Gaba dayansu

Idannuwansa ya lumshe yana sake duban fuskar namijin ya ce" Kin san ni ban samu gannin haka ba.....ban ga komai ba"

Sai da wani irin abu ya soki zuciyarta, a hankali ta kai dubanta kan fuskarsa tana janye hannunta daga jikin abin rufar yaran
A saman lebenta ta furta" Allah ya rahamcesu"

Shima a saman nasa leben ya amsa da "Amen summa amen "

Da kansa ya rakata dakin da aka kai Firdausi
Idannuwanta biyu, dama ba na dogon barci akai mata ba ta tsurawa waje daya ido tana kallo tamkar kurma , idannuwanta a soye tass babu hawaye, ciwon dake cikin zuciyarta da na jikinta ji take yi idan ta bude baki da nufin yin kuka tana iya yin aman jini......bata tunanin idan har zata iya yin kuka normal irin na mai fama da wani miki a zuciyarsa

Hannunta ya saki ya juya ba tare da ya cewa Firdausi komai ba ya tafi......itama a hankali ta karasa kusan Firdausin ta zauna tana kallonta

Sun dauki kusan minti biyar a haka , muryarta cen ciki ta iya budat bakinta ta ce " Aunty, gidansa zan koma ko?"

A hankali Amina ta girgiza kanta hawaye na zubo mata kamar ruwa , muryarta na rawa ta ce" Koda zan rasa raina a kan yaki da dukkanin ahalinsa, ba zan yarda a mayar da ke gidansa ba......kuma Abdulma ya ce ba zaki koma ba Fido"

Firdausi ta gyada kanta tana sake mayarwa ta dora a hankali saman matashin da aka saka mata mai laushi tana kallon sama, kennan yanzu mutun biyar ta birne a rayuwarta..............
A cen kasan zuciyarta ta ringa maimaita adu'ar da Amina ke karanta mata kasa kasa sosai tana lumshe idannuwanta hawaye na diga a gefe da gefen kumatunta

Tsayuwa ya yi ya yi kiran gida , ya samu Baba na sanar masa yanzu zai taho da suka zo ya dan fita ne

Baba na kashe kiran ya kai dubansa saman kular da Hajia ta kawo masa waina mai sunnan waina, waina irin ta yan gayu ta sha su yankakiyar albasa da komai da komai , a kala yau an yi sati da take wannan abin dan ya kulata, bata san cewa bashida lokacin haukanta bane, a garin da take dakawa ta kara kaimi ta daka sama da shi, tsaf ya shirya mata ko me take takama da shi

Mikewa ya yi bai ce komai ba ya ja hannun biyu zasu tafi

Jiki a sanyaye ta ce" Alkali, ina zaka je kuma baka ci wainar da na yi ba?"

Gannin da yara dole ya dakata ya juyo yana kallonta ya ce" Zamu tafi asibiti ne, uman biyu ke cen da kanwarta an mata aiki"

Hajia dake neman shiri harda dan mikewa tana fadin" To ko na zo mu je ne?"

Sosai ya ji sasauci a guguwar fushin da yake yi da ita a zuciyarsa, sai dai ba zai yarda da ita haka kai tsaye ba , dan haka ya ce" Aa, ki yi zamanki, idan tsoro ya fita tsakaninku kwa yi zumunci"

Daga haka ya fice da biyu yana tunanin sai sun biya an dauki Baba Lauratu su je tare ko dan ta kula da biyu , domin asibitin ba'a barin yan jinyama sam, ko kwana nawa zata yi ba zasu yarda da yan jinya ba, zadai a ringa zuwa ganninta ana dawowa har a sake su

Kofar ta zubawa ido na lokaci da dama a tsaye
Ta rasa ta inda zata kamo tunanin mijinta
Koda yake, ta fi kowa sannin waye Alkali a kan kafiya kan abinda ya nacewa

Zama ta yi tana maida kiran Maman Risala a ranta tanaa ayana ' matar nan kiran wace jarabar kuma take min tun jiya da yama!'

Gaisawa suka yi a mutunce, maman Risala tana basarwa ta ce" Na ji shiru ne Hajia tun jiya na zatama zan ganki?"

Hajia ta dafe goshinta dan ta tabata wata jarabar aka yi ta ce" Lafia dai ko?"

Maman Risala ta ce" Lafia kalau hajia, na ga abin alkhairi ya samu haka kuma na ji shiru?"

"Hajia ni du ban fahimta ba, wani abu ya faru ne na alkhairi bani da labari?" Hajia Hauwau ta fada a dan kagauce dan dama zuciyarta du a cinkushe, yanzu du irin yadda ta sa aka koya mata tuyar waina ta siyo tanda irin ta jonawa da wutar lantarki ta sa aka yi mata hadin waina naa karshe na manyan yan gayu ama Alkali ko budawa bai yi ba ya tafi wai asibiti ko kanwar uman biyu ko me? Ashe har kanwa gareta yarinyar!

Maman Risala ta yi murmushi ta ce" Au, na san kunya ta hanna masa sanar maki ne Hajia, ai jiya raga raga muka daukota mun kusa kai isha'i a asibitima, sai da muka ga likita baba, ai lamarin kai budurci kan zo da salo daban daban , ita kam ta jigata baiwar Allah, kin san abu da wace bata saba ba, a kilace a tsaftace shi yasama na dawo da ita nan dan ta yi jinya"

Tsuru tsuru HAJIA ta yi da mahaukacin mamakin maman Risala, du wayewarta bata kai cen ba walahi
Yanzu dama wannan maganar matar nan zata fada mata ta saka ta nutsu take sauraronta?, Wata irin kunya ta kama Hajia, harma ta rasa amsar da ya dace ace ta bada

A hankali Hajia ta iya furta " Uhum"

Maman Risala bata dauki hanya ba, bata gane ba, ta ci gaba da yamadidi da maganar tana karra jadadata, har ya zamto Hajiar ta fahimci inda ta dosa, watau kyauta da ake yiwa amare idan sun kawo daki, shi matar ke son nunawa

A nutse ta ce" Allah ya bata lafiya, zan hau sama "
Chapter 58 · 0% Book details