← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 83

Sashe 17

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dayar damuwar itace Hajia,
Walahi Amina na matukar tunanin zama da matar koda na awa daya ne bale na rayuwa tare da ita
Ita dai ba zata ce ga ranar da wani abu marar dadi ya shiga tsakaaninsu ba, ama irin yadda ta san Hajiar da kyamar lamarin talaka tana tsoron zamantowa abar kyama a cikin gidan
Tana tsoron kasancewa a karkashin Hajiar dan bata san wani irin zama zata yi a gidan ba, a kadan ta shekara uku tana yiwa Baba Mai Shanu waina tana kawo masa, ama maganar fatar baki bata hadata da matarsa bale godiya ko kamanta ta dan da zamanta, daidai da yin wainar shinkafa Baban ne yace da ita Hajia na son wainar shinkafa, ita kuma sai take yi dan kara girmama shi, ta fi tsoron zama da matar a cen kasan zuciyarta dan tana tsoron mutuncinta da son kare ratuwar ƴaƴanta
Ama idan ta yi duba da abinda ke neman haye mata fa? Lalle da wata wahalar gwara wata

Tana cikin tunanin nan suka karaso gidan

Hankalinta du ba a jikinta yake ba ashe har Baba ya bada umarnin a kai su Malan Liman gida su kimtsa su karya zai zo zuwa karfe goma su wuce gidan iyayenta

Sai da Hasan ya sake tba fuskarta ta dube shi a zabure , sai kuma ta shiga duban cikin gidan da datijan dake kallonta da tausayawa

Malan Liman ya ce" Idan kin samu masauki, kafin ki kwonta ki tabatar kin rama sallar dake kanki , ki yi addu'a sannan ki kwontar da hankalinki, in sha Allah karshen fargabarki ta zo"

Kai ta gyada a sanyaye sannan ta sauko ta shiga tafia a hankali Biyu na rike da gefe gefen hijabinta

Baba ne a gaba, kadan kadan yana amsa gaisuwar daidaikun ma'aikatan dake aiyukansu na safe har suka shige falonsa

A babar kujera ya mata umarnin zama sannan ya nufi sama cikin tafiyarsa a hankali na baban mutun mai shekaru irinsa

A nutse ya tura kofar dakinta ya shiga da salama

Hajia dake kwonce dan yanzu ta gama doguwar adu'ar da takan zauna ta yi bayan sallar asuba har sai rana ta fito sannan ta sake watsa ruwa ta kwonta dan so take ta fan huta kafin a jima wajen karfe goma ta fita cen wajen taron da suke yi yau dan ba mata masu fama da yoyon fitsari talafi da sunnan kungiyarsu

A hankali ta dago tana kallon mijin nata
Annurin musulunci daban yake, shi annurin musulunci tausasashe ne, ni'imarsa kuwa bata da iyaka, wannan bawa mai yawan sallah da nafila da ambaton Allah ya fi mata kowani namiji kyan kallo a duniya, annurin dake fita a murmushinsa kuwa ya fi mata komai dadina zuciya, gashi dai ya tsufa, fuskarsa du yabar tsufa ta bayana abinka da dogon mutun kuma fari tsufansa na gagawar nunawa, bale shi din ya kai tsufan shekara saba'in a duniya ai an sha ruwa, ama irin yadda yake da kuzari daidai gwargwado da kokari irin nasa na sakata jin nutsuwa a zuciyarta

Murmushi ta sakar masa tana karra jan hular kanta ta rufe gashinta da furfura ta kusan hadewa tana fadin" Alkali yau kai fa kanka? Na so sauka fa sai barci ya ci karfina"

Murmushi ya yi ya karasa bakin gadon ya zauna a ransa yana tunanin yau da gobe kayan Allah, tsufa labari, gashi yanzu shine kusan ba ruwansa da wannan lamari da ya yiwa naci a da, ita dinma da ta kasance cingan sarkin nacin miji a yanzu ba wannan a gabanta , abubuwan dake gabanta sun fi wannan fado mata a rai, kuma ana zaune, ana matukar kaunar junna da kula da junna, idan daya ya ce wash dan uwansa kaan rikice ya susuce

A hankali ya kamo hannunsa tana sake fuskantarsa, duda kwana biyu sun yi yar tsama a kan maganar ABDUL RA'UF ta nuna cewa shine bai yi masa magana ba da tuni ya amshi tayinsu ya masu biyaya, sai a yau take jin ta yafe , kanshin turaran miskinsa mai taushi na mata dadi a hanci ta ce" Fari mai farin gemu ko yinwa ake ji?"

Murmushi ya yi yana kallonta ya ce" kakar Fari bana jin yinwa, zuwa na yi da magana"

Sake fuskantarsa ta yi tana sauraronsa dan ta san ko meye yana da mahimmanci a zuciyarsa

A tausashe ya ce" Magana ce a kan Yarinyar nan, yarinyar nan marainiya ce, tana fama da kanta da neman hanyar da zata kare mutuncin kanta, sai dai hakan na neman gagara, har ya zamto wani marar jin tsoron Allah na dira mata gida da yara, ina so ta dawo gidan nan ta zauna har Allah ya fitar mata da mijin aure"

A tausashe ta ce" Wa kennan?"

Mai Shanu ya ce" Uman biyu nake magana a kai"

Dan jim ta yi tana dan tunani, sai kuma ta sauke Ajiyar zuciya ta ce" Allah shi kyauta, to kuma Kakan Fari sai an nemi shawarata dan wannan? Ta zo mana ga cen bangaren su Nana sai ta zauna tare da su"

Yana kallonta ya ce" Nana kuma?"

Hajia ta gyada kai tana kallonsa

Mai shanu ya girgiza kansa ya ce" Duda suma bana zaune da su a matsayin bayi ko wasu da na fi a duniya, ama su din masu aikina ne, ita kuma jikata ce, yarinyar nan na mutuntani tamkar ni na haifi mahaifinta, a nan tare da mu zata zauna "

Naman goshinta ke dan tatarewa tana kallonsa, ta jima kadan a haka tana nazartarsa, sai kuma ta tabe bakinta tana kawar da kanta gefe ta ce" Ba damuwa, ama sai dai ta zauna a dakin kasa ba nan sama ba!"

Murmushi ya yi a bayane ya mike ya kama hanyar fita , sai kuma ya dakata ya juyo yana kallonta ya ce" Idan kina da fita yau ki ajiyeta gefe ki kula da ita, zan so ki rarasheta dan kin san me ake nufi da abinda aka so yi mata"

A tausashe ya yi maganar, sai dai wani irin gundumemiyar guduma da ta daki kirjinta ta hanna mata kyakyawan motsi ta raka kofar da ya ja mata da kallo

A hargitse ta so mikewa dan bin bayansa, kwata kwatama ta manta shekarun yanzu da na da ba daya ba , sai daa ta ji kafafuwanta sun wani irin rike mata ta saka hannunta tana rike abin gadon hadi da rintse idannuwanta a bayane ta shiga karanta dukkan adu'ar da ta zo bakinta sannan ta koma ta zauna a bakin gadon

Ido rufe ta shiga tunani a cen kasan zuciyarta da tarin takaici, ta zauna? Kar ta fita? Sabon salo kiran sallah da usur, yaushe rabonta da irin haka da shi? Me zata yiwa yarinyar da shekara ashirin da biyar kadai ta bata a duniya? Menene yarinyar bata sani ba? Yanzu shi dan ance an dira mata har wani daga masa hankali zai yi? A tunaninsa zata zauna har wannan shekarun bata san hanyar kashe kishirwarta bane? Itace MAI SHANU zai ringa jerawa wulakanci kala kala dan kawai an santa fa hakuri (🧐), walahi ba zai yiwu ba, bafa zai yiwu ba, bara kafarta ta saki ta sauka ta tarda shi a yi wace za'a yi! Ina dalili wai zai ringa caza mata kwakwaluwa ? Kiri kiri ya ki tankwasa fitinanen jikansa da ya yi gadon halinsa! To daga shi har shi din ba zai yiwu ba, gashinan yarinyar da yake nema ko jiya sai da ta mata maganar daga ce masa kwana biyu bai leka gidansu ba ya daina dan kiran da yake yi mata , gashi ya hannata kiransa kowani time yace baya so yana cikin aiki ko cikin jama'a ko ibada ta shagaltar da shi, wai a haka yana son yarinyar be kowama ya sani? Ita kam ta gaji da fitinarsu walahi!

Baba bai sauko daga dama da wuri ba, sunna nan zaune dai Babar ma'aikaciyar gidan ta zo ta wuce baban dakin kasa da yan mata biyu a bayanta bayan sun gaisa duka shiga gyaran dakin, domin babu mutane ciki ba zai rasa kura ba,
Sai kuma dakin kusa da shi nanma aka gyara tsaf har bayi aka wanke tasss
Sunna gamawa suka bata kys din dakunnan biyu suka ce in ji baba , baban nata ne dayan kuwa na ƴaƴanta

Ita dai amsa ta yi tana shafa kan Hasan da har yanzu fushinsa bai sauka ba sai cije lebe yake yi baya kula kowa
A haka aka kuma kawo masu abinci shake da plate baba da cokula, ga jus da ruwan sanyi aka ajiye masu cike da kula da mutuntawa

Da kyar ta samu Hasan ya yarda ya sauka dan cin abincin, shima dai sai da yace sai dai idan tare zasu ci, a dole ta ringa fan tsakura tana kaiwa bakinta , su kuma sunna ci sunna korawa da Jus

A haka Baba ya sauko, cikin shigar manyan kaya na daraja a jikinsa, sai kanshi yake yi ga hula ya kafa a kansa

Sosai ya ji dadin gannin sunna cin abinci, da kula sosai ya ce" Idan kun gama ku shige ciki ku huta kin ji Uman biyu?"

Amina ta amsa kanta a kasa , biyu kuwa suka ringa yi masa adu'ar a dawo lafiya har ya fice a falon yana amsawa

Gurin Man Liman suka je suka dauke shi da motar suka wuce gidan Iyayenta, watau yayan mahaifinta, wanda yake da dan teburinsa a kofar gidansa, sun tabata ko yayane zasu same shi a gida warhaka, sai dai idan rasuwa ko wajen daurin aure ya tafi, koma ina ne in sha Allah ya yi niyar sai ya hadu da shi a yau

Sun taki Sa'a, sun samu Malan dan iya a gida , a kofar gida yan kukula kayan sana'arsa saman tabarmarsa

A mutunce suka gaisa da junna, domin ya san waye MAI SHANU farin sanni, bai taba zuwa gaishe shi bai masa alheri mai girma ba

A saman tabarmar suka zauna, Mai Shanu na tsokanarsa cewa yaya haka ya tsufa? Shima yana yar dariya da fadin to yaua za'a yi neman na gero kadai ya isa ya tsufar da talaka
Mai shanu ya ce Allah ya dafa mana, suka amsa da amen
Chapter 17 · 0% Book details