← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 83

Sashe 62

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai ya gamsu da komai ya ajiye yana sake zama yana ta cicira tunanin dake zuciyarsa, sai dai ba zai fadawa kowa yanzu ba, zai bari ne har ya tabatar sannan ya san abin yi, shin yaya zasu rayu bayan bata son rayuwa da shi? Idan kuwa har furen dake tare da ita ya yi tsiro har ya yabanya wace irin gagarumar rigima ke gabansaM

"Hum" yace har sai da Mansur ya dube shi yana ajiye masa jus yana fadin" Man kayanka sun baci gashi an kusa shiga masalaci, ya dace ka je ka kimtsa"

Ajiyar zuciya ya sauke ya mike yana masa salama da nufin sai sun hadu da yama idan ya dawo daukan Uman biyu

Tafiyarsa ya yi ya bar Baba da biyu dan ya san sa wuce masalacin tare , shi kuma ya koma gida

A cikin dakin kuwa Baba ke yiwa Amina nasiha kasa kasa, Firdausi kuwa ta samu barcin wahala tunda ta saka hannunta cikin na yayarta sai da barcin ya kwashetama Amina ta janye a hankali ta zauna aa gefenta tana kallonta

Kasa kasa Baba ya ce" Haka nata salon kadarar yake, kuma kin sam cewa Allah baya dorawa bawa abinda ya fi karfinsa, ki daina kuka ki bata kwaron gwuiwa, ta haka sai ta shanye dukkan wahalar har ki ga ta mike kamar ba ita ba kin ji Uman biyu?"

Amina ta gyada kanta tana sake share hawayen nata, idannuwanta har sun kumburo dan kuka, bata taba jin maraici har cikin kirjintaba irin na yau, kafin Abdul ya fito da Firdausi babu irin abinda bata tuna ba a duniyarta, ta yi kuka da boda kamar zata fasa motar

Shigowar Baba tana rike da bokici da yan kayayakin dake ciki , Husaini na yi mata surutu ya saka Baba sakin murmushi yana kallon Hasan ya ce" Yau sam ba fara'a a fuskar mai tsuntsaye, Allah dai ya sanyaya fushinsa"

Baba ta yi murmushi itama tana sake gyaraa matashin kan Firdausi ta zauna tana kyatu ta kama Hassan ta zaunar ta ce" Allah ubangiji yaa sa karshen wahalar kennan"

Da amen suka amsa, du suka ci gaba da zama har karfe goma sha biyu ta yi suka fice tare da Muhammat da ya dawo daukansu dan kaisu masalaci

Da yama da kyar Uman biyu ta fito , har zuwa lokacin Firdausi bata farka ba, kuma ance idan ta farka ba za'a bata abinci ba , sai dai ta sha jus

Ji take abin nan sam bai dace ba ace za'a rabata da kanwarta, shi dai a bayan motar a zaune waya yake amsawa , yau sam bai leka nema ba, gashi da zafin nema, suka nufi gidan Baba domin yau bai je ba, rabonsa da Hajia kwana biyar ciffffffffff

A asibiti

Tsaye suke a kanta, docter da Mansur sunna bata baki a kan kin amsar koda bakin ruwa ne ta sha, ta nuna Alhamdulilah bata jin cin komai

Docter ta janyo kujera ta zauna tana kallonta ta ringa yi mata nasiha da bada baki da nuna mata mahinmancin lafiyarta
Ama Firdausi sam ta nuna bata jin yinwa ne

Da kula Docter ta dubi Docter Mansur ta ce" Likita, inaga sai an tabo makusancinta, ka san ba zai yiwu ta ki shan jus din nan ba, shi zai taimaka mata samun karfin jikinta kafin ta samu iska ta fara cin dan salak da dai wani abin marar nauyi ko?"

Kai MANSUR ya gyada, cike da tausayi yana kallonta ya ce" Na gode sosai Docter da kika zo, zan dubata....."

Docter ta amsa ta mike ta tafi,

Mansur ya amshi jus din dake hannun Nurse din da ta shiyata da komai , itama ta fita , ya maida dubanta kan Fido da kanta ke sade tana kallon waje daya

Aa sanyaye ya ce"baki dangana ba Firdausi?"

Fido ta dago a hankali ta yi masa kallo daya ta sake sada kanta, muryarta a sanyaye ta ce" Dangana da me likita?"

Mansur ya ce" Da rashin da muka samu, ko kuma aban yaren ne mai baban laifin?"

Sake dagowa ta yi tana kallonsa, ta sake soke kaanta

Mansur ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Akoy ciwo Firdausi, akoy ciwo matuka, ama ya dace ki yi duba da jama'ar dake zagaye da ke masu zubar da hawayensu dominki, a kan laifin daya tak, kar ki hukunta kanki da hukuncin da zai damu masoyanki, kin ga wace zata fara jigata yayarki ce, a gangaro kan biyunki, mu da kanmu sai hankakinmu yaa tashi Firdausi, karma ki saka damuwar wani a ranki ki kasa nutsuwa kin ji?"

Firdausi ta sauke numfashi yinwar fa na cinta, a sanyaye ta ce" Docter, dama wata sharaar ai sai a kiyama......., Luuuu luuuuuuuuuu
Nake gani kar aje nima mutuwar zan yi na shagalta da kurbar juss, shi yasa nake ta Adu'a a zuciyata......ka ga kuma biyu ba nawa bane ba fa, na uman biyu ne"

Tausayinta, madaukakin tausayinta, shi ya fi komai rinjayarsa,
Da dabaru irin na likitoci ya samu ta amshi juss din har ta yi masa sha na mamaki

Tana gama sha ta koma barci domin akoy allurorin barci a lamarin dole sai da hutu

Ido ya zuba mata yana kallonta, kallon da shi kansa bai san ya zarce a kallon ba
Gata dai a cikin hali na rama, duhun fata du hasken fatarta wahala ta rinar da ita, rashin walwala, girman ciki irin na wanda ya sauke ciki yanzu, tarin tausayinta ya sakashi zuba mata ido yana mai cike da madaukakin tausayinta a zuciyarsa

Ajiyar zuciya ya sauke ya mike domin a lokacin tuni har isha'i ce ke shirin kawo kai ya sake duba komai na dakin sannan ya tafi ya kimtsa ya nufi gidansa dan tun karfe shida yau rabonsa da gidan nasa

___________________________________

Daga gidan Baba suke, fuskar Amina tamkar an saka balan balan , ita kafai ke hauhawa tana hucisakamakon abinda biyu suka yi mata, wai ba zasu zo ba yau a gidan baba zasu kwana a cen zasu yi weekend
Tana ji tana ganni akace wai ta bar ƴaƴanta ta dawo gida ita kadai, ita lamarinsu ya fara bata tsoro, tana janye shakuwarta da ahalin gidan Mai Shanu yaran nan na makalata

Sai da ta bacewa ganninsa ya dawo da dubansa wajen Muhammat, ya ga ya tsareshi da ido yana wani murmushi irin na saman leben nan

A kausashe ya dage girarsa daya ya ce" menene?"

Muhammat ya dora yan yatsunsa biyu daidai bakinsa ya ja irin ya yi zif din nan sannan ya sake mayar da kansa gefe yana murmushi

ABDUL ya bude ya fice yana dan mimike kafafuwansa fa fadin" Sai gobe idan A'lah ya kaimu"

Muhammat ya ce" Allah ya tashemu lafia Oga, a huta lafia"

Bangarensa ya shige ya haura sama
Ko'ina fes fes an gyara ko'ina sai kanshi yake yi, masu gyara harta da dakin barcinsa su suke gyarawa

Wanka ya yi ya dauro alwallah ya dawo saman salaya yana sake dafe cikinsa da suka sake cin wainar Uman biyu shi da yara da baba gaba daya, cikin nasa ya yi nauyi da yawa bayan baya cika kulunsa har haka da dare, a dole zai dan motsa jikinsa idan ba haka ba , ba zai iya samun barci mai dadi ba

Yana gama sallah ya dan buda computernsa ya dadana ya gama aikin da zai yi sannan ya mije ya sake fesa turare ya sauko yana kallon table din abincinsa an shake da kuloli kala kala ya yi gaba , yau ba zai leka komai ba ai ya koshi sosai ne

A Hankali yake takawa, da fara kar din jalabiyarsa a jikinsa ya shiga dan tafia a tsakar gidan, nufinsa ya fita haka ya zagaya anguwar a kafa ko zai ji cikinsa ya sauka kadan

Idannuwansa ne suka sauka a kanta, ta cenza shigar jikinta ama da hijabinta tana tsaye ta dan dafa jikin garu a balbalin kofar bangarenta tana kalle kalle

"An mata" ya fada a hankali yana kallonta a tsaye

Itama tunda ya fito ta ganshi, shi yasama ta cire dubanta a kansa take kallon wani wajen daban, da yace an mata, a dole ta juyo tana kallonsa da mamakinsa

Murmushi ya sakar mata yana kallonta ya ce" Me ake yi a waje da dare?"

Amina ta dan sadda kanta , sai kuma ta cuno baki tana fadin" to ba twins bane ba zasu zo ba, su ba ruwansu idan na ji tsoro ko?"

"Da ruwansu mana" ya fada a hankali
Sai kuma ya sake kallonta ya ce" Tsoro kike ji?"

Mazewa ta yi ta ki bashi amsa

Dan murmushi ya yi ya ce" To zo mu fita yawo a cikin anguwa"

Samun kanta ta yi da son fitar, domin ita kadai du wani kadaici ke damunta na ba gaira babu dalili

A sanyaye ta sauko suka shiga tafia, kadan kadan da dabara sai ta saba jerawar da suka yi, shima da dabarar sai ya daidaita

A hankali suke takawar har suka fita a makeken get din suka shiga tafia a anguwar dake dauke da fitillu manya a kofar gidaje, ya zamto ba duhu sosai, sannan akoy mutane jifa jifa sunna dan tafiyarsu, wasun kuwa a zaune zaka gansu nesa sosai sunna dan zantawa, harda mata kuwa, domin anguwa ce ta gayu mai dauke da yayan yan gayu da jikakun yan gayu masu son yannayi mai dan sanyi na dare haka kafin dare ya dan tsala su shige gida

"Me yasa kake son shiga tsakanina da nemana?" Amina ta fada a hankali tana kallon hannunsa daya dake saman kirjinsa a rungume

Dan juyowa ya yi ya kalleta, sai kuma ya dauke kansa ya shiga nuna mata wata shuka yana fadin" Kim ga wannan shukar, a shekara daya take girma, kuma ita bata son mai dati ya tabata, idan kanada dauda irin haramtaciya ka tabata mutuwa take yi, Aunty kin ga tanada kyau ko?"

Amina ta kalli shukar, ba shukar komai bace sai ta zogale, zogale dai zogale , ta ce" Uhum"

Takawar suke yi har suka kusa kaiwa wata kwana ,
Dan daga kafarta ta yi ta je ta gabansa tana kallonsa ta ce" ABDUL, me yasa kake son shiga tsakanina da nemana?"

"Bani da nutsuwa a kan neman ki" ya fada a takaice
Chapter 62 · 0% Book details