Sashe 38
Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shirye shirye ake yi ba kama hannun yaro
Tunda maganar nan ta zauna har aka je aka kai lefe Hajia ta yi gadarar nan yan siyasarsu suka dauka garima ya dauka, saitin akwatunnan kayan ke yawo ta ko'ina, da hoton screen shot na transfer millioyin kudaden da aka dora wai na dinkin Amarya, kudin da sai a bude shagon dinkin na kasa da kasa da shi
Daga kowani bangare fa aka mike kowane ya shiga shirye shirye
Bangaren amarya kaya ake shirin zuba mata na garari, mahaifinta da mahaifiyarta da dangi sun hadu taf sunna bada himma
Ta bangaren Hajia kuwa ta je da kanta gidan da za'a saka amaryar ta ga tsarin gidan , da kanta wannan karron ta ware bangaren da ya fi kyau din ma ABDUL din, ta gwamace hakan dan a yadda ta ga take taken mijinta idan har ta zabi nan ma Risala zata kwashi bakin ciki ne
A event din auren diner daya jal ce za'a yi ta amaryar da ango bayan daurin aure da wunin biki
Diner ce ta garari ta taron manya wace harda su davido mawakan yan gayu da manya manyan mawakan hausa aka gayata, tuni takardar gayar ta samu kowa harta da gagarumin Hl din da za'a gabatar da bikin Hajia ta tura kudinsa
Kan Madame fa ya dau caji, bata da lokacin kowa, jikanta dake spain kawai take tabowa a kai a kai dan yan cenji, shima a gobe take sa ran zuwansa kasar domin daurin auren bai fi da saura kwana hudu ba a yau
Happy juma'at yan uwa
*NZL PAGE2️⃣4️⃣*
Bangaren Amina, a lamarin yau da gobe na rayuwarta ta mayar da komai a kan tsari
A cikin akwatunnanta tsararun hijabai irin na yadikan turkish kuka dinkin cen har kasa masu samfari kala daban daban da tsari na gayu take cakarewa da mora hankali kwonce
Bata taba dinkunnan atampopin da sauran manyan kayan masu shegen kudi ba, ama ta taba irin dogwayan rigunna masu laushi da tsararen kyau
A haka ta samu gyaran wata amarya wace take a tsohuwar anguwarsu, yarinyar a cen yar gayu ce kuma yar gata ce, ko a yanzu ta yarda Aminar ta gyarata ne dan ta ganewa idannuwanta idan har da gaske wai zaman da Amina ke yi a gidan nan a matsayin matar Hon ABDUL RA'UF ne? Domin maganar na zaga layi, yan mata kai ya dauki caji, kowace so take ta gazkata maganar nan dan ABDUL RA'UF din ba boyayen mutun bane, bale yawancin yan matan sunna jin maganar sunnansa ne a bakunnan samarinsu irin yadda suke koda shi da halayensa da kyautarsa da daukan wankansa da ajinsa tamkar wani saraki
A yau sansanyar safiyar Alhamis, ya rage saura kwana uku a daura auren mutumen dake amsa sunnan miji a gareta, hakan ya sa gidan ya dinke da jama'a dangi da yan uwan dangi, wa'inda aka gayata da kuma Mu (😌😌😌😌 ni da kwate ai mun kusa wata a gidan)
Bakin manyan mutanen sun rinjayi ya mu ya mu din , domin kuwa gidan kansa ya dauki motoci har ya zamto an cike wajen ajiyar motocin an fara ajiyewa a balbalin gidan
Dafe dafe ake yi ta ko'ina ana ci ana wanke kwanoni, wata tukunyar na sauka wata take hawa
Kayan aikinta ta kai cen baya wajen gardin din nan, hasalima itama tunda gidan ya fara daukan haramar mutane take guduwa domin har daki ake tardota ace an zo a gaisa ne a ringa kare mata kallo, ita kuwa hakan na damunta ainun, ga gyaran nata jikin da karara ta fadawa Baba Lauratu cewa ya isa haka in na so take yi fatarta ta cenza kala gaba daya ba, yanzu haka kunshin nan na gargajiya irin na gam din nan da aka yi mata ya hudo ya yi maroon sosai sai daukan ido yake yi a kan fatarta da ta dawo milk color tsabar gyara da anfani da su ruwan kwai da madarar ruwa, ita da kanta takan ji wani iri idan ta kalli fatarta , dan Husaini cewa yayi Mama ashe kema fara ce ba'a sanu ba?, Hasan kuwa sai ya kalleta ya yi murmushi irin ta birge shin nan
Murmushi ta yi lokacin da Suraya ta ce" Oh Aunty Amina baki ga yadda hutu ya kamaki ba, ni kam dan Allah ki min irin gyaran fatarki Aunty, subahanalah dubi da kika cire hijabi, wai aunty harda gyaran Mama kina yi ba?"
Kunya ce ta kama Amina, domin rigar dake jikinta ba wata mai dogon hannu bace, kuma ta cire hijabinta ne dan yanada haske domin kalar ash color ne mai haske idan har ruwan hadin gyaran nan ya taba shi zai lalace ne da kalar, gashi ko kanta babu wani abin kirki da ya rufe kan, batada kitso a kan dab kwalin wani mai sara sara ne ta dan yafa shi ta lauyo shi haka kadan a jikinta
Dan murmushi kawai ta yi ta kasa bata amsar gyaran mamar da ta tambayeta ta shiga fadin" Surayah, kin ga hadin nan da na maki na hada kurkum ne da man ja da lalle na gargajiya, ana kwaba su a waje daya ne a shafe jiki gaba daya da shi sai a hau kujerar nan ta tsuguno mai kofa a zuba garwashi isashe a rufa wannan abin rufaf mai nauyi a bar fuska a waje ya yi ta bugun jiki, a kadan zaki dauki minti talatin a sama, dan haka dole ki jure , shi ake kira da DUKHAN, idan muka yi shi na kwana goma sai kin yi mamakin yadda zai kama maki fata, da farko fayar taki zata dauki duhu ne, a hankali muna murjewa da su dilka ana yin na kurkum da madara zai washe ki fara daukan annuri irin na amare, Yanzun sai kin mike tsaye na saka hannayena na shafe maki hadin sai ki zauna"
Suraya ta yi murmushi ta ce" To aunty, ai in dai zan yi annuri irin naki ko meye zan jure walahi
Mikewa ta yi tsayen ta juya ita kuma da dabara ta ringa shafe mata jikinta da hadin ko'ina da inanta harta da cinyoyinta dan koina ake shafawa, sannan ta zauna ita kuma ta yi wani shegen dukawa irin ka bada baya sosai din nan ta dan gantsarar da kugunta ba da gangan ba sai dan ya kama dole ta yi hakan a hankali ta sake debowa dan ta murje mata fuskarta da hadin da kuma kunnayenta da bayan kunnayen
Shine a gaba, sai daya daga cikin masu bashi tsaro rike da wata akwatinsa sai babar rigarsa da ya cire a cikin mota ya bar na cikin , watau riga da wandon kayan suka biyo ta bayan ko zai samu saukin gaishe gaishen mutane da ya hadu da su tunda ya shigo
Shi mamakima ya kashe shi gannin taron gidan nan, mamakinsa ta yaya suke iya jure wannan hayaniyar ne? Wai mema ya sa aka tara mutane ne har haka tun yau?
A hankali ya ja birki daga karasawa ta kofar da yake da niyar yi daj ya shige ta kofar kicin
Muryarta a sanyayen nan nata idan zata yiwa kowa magana a duniya banda shi ya ganar da shi itace a wajen a lokacin da ya kawar da kansa daga inda idannuwansa suka sauka kunnayensa suka jiyo magana kamar haka" Suraya ki gumtse bakinki kar ya shigar maki baki, kuma muna maganar turaren wuta, hajiyarki tace n dubu arba'in take so a hada maki, to ama baku yi maganar na ruwan ba, kin san fa babu wanda bana hadawa harda su humura duka kaf ina siyarwa"
Sumaya dake son bude idannuwanta Aminar ta ce" Ki fa kula kar ki bude idannuwan nan ki bari har ki sauko saboda shi kwabin na fuskar harda kwai na saka ki bar idannuwanki a lunshe haka kar ki rintse su kuma kar ki bude su kar sikin namu ya koma baya"
"Aunty?" Sumaya ta furta
Gefen da yake kallo yana ta tunanin abinda ya dace ya yi, shin komawa ya dace ya yi ya bi ta tarin dumbin jama'ar cen dake iya hadasa masa zazabi, ko wucewa zai yi ba sai ya shiga harkar wannan fitsarariyar y'ar ba?,
Wata zuciya ce tace masa'to idan ka koma a kan wani dalili?, Karewarta dai ace ka ga mace ba rufar kirki ka shigo ko?, Idan ta wani ka shigo ka tarar?, Ka je abinka'
Juyowa ya yi ya fara kara takawa daidai Suraya na cewa" Shi na gyaran nonon fa?"
Amina ta dafe goshinta ta ce" To wai ke ina hadinki da abin gyaran noni fisabililahi bayan ba auren kika taba yi ba, ba kuma shayarwa kika yi ba?, Ni dai kin ga nima ban yiwa kaina ba kuma gaskiya bana fadawa budurwa sirrin gyaran mama, idan har kinma ciko har wanda zai aureki ya zama ila a gareshi ai akoy matsala sai ki yi gagawar gyarawa, inma ba maza da iya wani abin daban ba ina idannuwansu ina zarce kallo?, Koda yake laifinku ne yan matan zamani, ko dinki kuma tashi yi sai a yi maku mai gidan mama ta yadda hakan zai dauki hankalin mai kallonku......ni kam mu yi maganar humurar dai bana son wancen"
Sake ja ya yi yana juyawa ya mika hannu ya amshi jakar dake hannun wanda yake biye da shi kamar jela, domin da zarar ya tsaya shima yakan tsaya din ne har ya daga kafarsa
Yana kallonsa har ya bar wajen kwata kwata sannan ya juyo daidai Amina ta juyo itama tana murmushin maganar Suraya
Kwanon dake hannunta ta saki ya fadi kasa, lokaci daya kuma ta duka ta rarumo shi gabanta na yankewa ya fadi
Daga duken ta rarume shi ta kusan kifa shi a kanta jikinta na rawa sosai ta hade kanta da cinyoyinta hankalinta a matukar tashe, bata taba hasashen cewa za'a iya biyowa ta nan haka kai tsaye ba, bata taba kawowa wani namiji zai zo nan haka kansa tsaye ba, ta manta dan masu gidab ya taba hadewa da ita ta nan din, sai dai ai rabonta da shi kusan sati fa ita tama manta da shi in ba jama'a ta gani ba ta tuna da taronsa ake yi