← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 83

Sashe 29

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kadan sai da ya dauki kwana uku, hankalinsa ya kwonta, tunaninsa ya fiafaita waje daya, zuciyarsa ta dan samu nutsuwa, ya ji eh lalle yanzun yana iya zama da kowa su zanta a kan lamarin sannan ya turawa Risala sakon cewa zai zo gidansu a yau, dama su Hajia yana samun sakwaninsu ne daga wajen Mansur, domin summa daina kiransu ya yi

Tunda ya fada mata ta tayar da tashin hankalin shirye shiryen tarbansa
Du ta hargitsa ma'aikatan gidansu da basu umarnin a dafa wannan, a sauke wancen, har abin ya kular da mahaifiyarta dake binta da kallo

Rai bace ta ce" RISALAH, ba zaki yiwa kanki da kyau a lamarin Yaron nan ba ko?, Ba zaki daina rawar kafar nan ba ko? Ke anya kinada zuciya a kirjinki? To walahi bari ki ji ni a kan y'ayana ba ruwana da maganar dukiya ko mulki!, Ko mahaifinku na ga zai sakaku a matsalar da ba itakenan ba zan nema maku mafita mai kyau, sakarcin banza sakarcin wofi"

Har RISALAH zata tafi kicin dan ta karra masu maganar idan ya zo yana zama mutun biyu su kawo masa abin tabawa su gaishe shi kafin su tafi su basu waje ta ja ta tsaya

A hankali ta dawo ta zauna a gaban mahaifiyarta ta sha kwaliya har ta gaji

Hannayen mahaifiyarta ta kamo tana kallonta a hankali ta zauna gabanta ta ce" Mama, dan Allah ki yi hakuri, Mama na san kudinsa, kyansa ko sunnansa ke baya gabanki, na fi maki komai, Abane ke son tarayarmu ko dan sunnansa, Mama ni kuma.......ni kuma ina son shi, yanada halin girma, Mama a samarina kafin na tsayar da shi na jima ina bincike, kin ga yanzu da na tsayar da shi ina mai tabatar maki ya isa da hakan..... Please Mama idan ya zo kar kice zaki yi masa wulakanci a kan maganar aureb naj nasa, ki barni mu yi magana da shi, dan Allah kar ki shiga, idan baki manta ba mun taba yin fada da shi kika yi kiransa kika yi masa fada, Mama tsakanina da shi ne, ama kika shiga kika fatatakeshi, kin ga sanadiyar wannan da kyar ya dawo ya saurareni, har cewa ya yi dan shi bashida iyayen ne zai fuskanci haka? Shi bai maki rashin kunya ba ama sai ya shafa min lafiya.... Please Mama ki bani dama ni na san lagonsa, idan har na sada kaina zai turo a yi maganar aurenmu, ni kuwa na maki alkawarin ba dai ya zauna da wata mace ba ina raye! Mama ba zan je gidan da niyar zaman lafiya da kowace shegiyar dake tsakanina da ABDUL ba!, ABDUL nawa ne, idan ta min shigar sauri sunnanta kishiya uwar gida mai shishigi!, Ni na fi kowa sannin ABDUL dina, ni zan yaki abina.... plz Mama zaki yi min haka?"

Sosai uwar ke tausayawa yarinyarta, ba komai ya sa take jin tausayinta ba sai idan ta duba ta ga zazafar soyayar da y'ar ke yiwa yaron nan, a bayane yake ta fi sonsa fiye da son da yake yi mata, a bayane take nuna masa zazafar soyayar da har take ikirarin tana iya mutuwa a kansa, wannan abu shi ya fi komai bata mata rai, idan ta kalli santaleliyar y'arta takan ji damuwa ta lulube zuciyarta, shin wace riba yarinyar zata ci da take kokarin wulakantar da kanta a kan Da namiji? Itafa inda ta rako mata kennan, itafa ba zata dauki irin abubuwan nan ba, shi yasa ko ubansu idan ya zo maraba, in ya tafi ya gaishe su walahi,

Mikewa ta yi ta haye sama domin ba zata iya daukan takaici ba, dakinta ta fada ta dauki wayarta ta zauna a bakin gado ta shiga lalubar number HAJIA Hauwau wace rabonta da ita kusan kwana hudu kennan, ta yi kiranta sau kusan bakwai bata daga ba dan kwarai ta ji haushin abin nan,

Tana ji lokacin da motoci ke shigowa, dan haka ta mike ta daga window tana hangowa daga sama

Cikin rantsatsiyar shada yake sai walwali take ruwan baka sidik da dan zubi na bakin zare da dan rastsin ash color mai haske kadan ba da yawa ba
Kafarsa sanye da takalmi kafa ciki ba mai tsini ba, mai daidaituwa da kafar mutun ruwan ash color, sai hularsa mai duhu da dan ash kadan

Kayan sun matukar amsarsa, kuma duda shada ce haka ake gannin irin yadda wajen hannayen suka rike hannun taf suka kuma kama wajen kirjinsa kadan

Irin tsayuwar da ya yi a jikik mota ya dan harde hannunda daya yana duban agogo ya sakata ayyana magana kamar haka' A kulun idan ya kawo mata ziyara yana gagawa ne '

Kwarai itama ta san sirikin nata ba dai a yi maganar haduwa ba, classs, gayu, uwa uba yan cenji, matsalarsa daya ce da bata tunanin in zai cenza mumunar akida da isa

Tana hangen irin yadda Kyakyawar y'arta mai ji fa kyau da isa ke yi masa magiyar shiga ciki, da wani zumbulelen hijabin da ta zumbula a kan mahaukacin lesh din da ta sha, du dan kar ransa ya baci ya mata fadan ya zo da maza ta fito ba hijab, hum, ita gani take yi yarinyar tata ta cika azarbabi a kan lamarin yaron nan, tun bai zama mijinta ba yana dora mata dokoki haka ina da ya aureta?

Lebe ta ciza kadan tana amda salamar Hajia Hauwau fa ta yi mata a nutse, a hankali kamar yadda ta saba magana idan zata yi in ba bali za'a yiwa dan tsoho mijin arziki ba

Bakin gadon ta koma ta zauna itama cike da nata ajin ta ce" Kwana biyu Hajia?"

Hajia Hauwau ta dan yatsina fuskarta daga ringeshen da take tana mamakin isa da raini irin na matar nan, in ba dan abinda take hangowa na harkar siyasar jikanta ba har ta isa ta ringa kiranta har sau bakwai bata amsata ba?, Shi yasa itama yanzu ta ki amsata sai da ta mata kira na biyar tukunnan

A takaice ta ce" Fine " ta ja bakints ta rufe

Wayar ta sake kallo, ta tabata hajiar ce sai dai irin yadda take bata amsa ya tabatar mata ko yayane hajiarma ta shaka

Dan haka wannan karron sai ta dan sasauta ita mahaifiyar Risalar din a hankali ta ce" Hajia kennan, sai labari ya zo min na auren HONORABLE ko?"

Hajia ta dan mike zaune daga ringeshen da take tana duban agogo, har karfe shida na yama ya shige dare na son sanyo kai ta ce" Uhum " ta kuma jan bakinta ta kyale
To in ba rashin mutunci irin na uwar RISALA ba ita har ta isa ta wulakantata? Me take takama da shi ne wanda ita bata malaka ba? Kai idan bincike ko bibiyar asusu za'a yi ta dameta ta shanye a ya'yan banki da kuma hawa manyan motocin, dan ana wani lalabata saboda y'arta sai ta ni rainawa mutane wayo? Maganar siyasarma ba wai ana tare da su bane dan su din zasu bada wani abin, an hada karfi da karfe ne dan a cimma matsaya guda, mijinta shine dan siyasarsu shi ya kawo maganar ABDUL RA'UF din da nufin da zai amince da shi suka tsayar a takara, ABDUL din da har yanzu bai zauna sun zanta a kan maganar ba ya dai saurara ya yi shiru ne, shine zata wani dauki kanta ta kai inda Allah bai kaita ba? Ita yau mace ko ita ke ciyar da ita ai na zata dauki salon wulakanci ba, ta kama kanta dilla tun kafin ya gudu ya barta!

Hajia ta sake gyara zamanta ta ce" Hajia sai nake gannin kamar ranki ya bace bayan ni aka wulakanta ni ya dace raina ya bace na yi dogon fushi a kan lamarin?, Kina gani fa irin wahalar soyayar da RISALA ke yiwa ABDUL, ama fisabililahi sai dai mu ji a duniya wai ya yi aure? Wannan wani irin tashin hankali ne, a kan maganar summar Risala biyu Hajia, yanzu haka bata cikin hayacinta, baban damuwarta maganar aurensu da kuma sakin yarinyar dan ba zata iya zama da ita ba a matsayin kishiya ba Hajia"

Hajia ta mike tana bude kofarta ta dan shiga takawa kafarta sanye da takalmin bakin bed wanda take dan yawatawa da shi a cikin samanta bangarenta zuwa na mijinta ta ce " Ai a ranar da nake kiranki mun yi maganar da mijinki ne, yanzu haka mun gama maganar da shi kawai, kunna iya zantawa idan hakan ya yi fine, idan bai yi ba sai a hakura kawai dan bana ciki da abinda zai taba mutuncina da girmana !"

Tana dasa aya ta katse kiran tana jan tsaki hadi da fadin" dan ubanki nada kudi sai me? Mijin naki da kike takama da shi yaron jikana ne, kuma ke din a kadan na baki shekara goma a duniya! Shine sai ki ba kanki damar raina ni? Ko mijinki karya yake ya san wacece ni kuma yana min *LADABIHHHH* dan ya samu abinda yake so a duniyar siyasarmu, da ake mutuntaki dan ana tunanin yar mutuncin kike, bayan wannan ABDUL yana iya daukan yar gidan ubanda yake so ba za'a hanna shi ba, kin yi kadan mu yi maganar cikin gidana da ke, duma abinda aka je aka fada maki hakan ne! Nonsence kawai!"

Tana yi ne tana saka hannunta da nufin tarda Mai Shanu a yau, dan ta tabata ko meye ya kwontar masa yanzun

A bangaren Hajiar kuwa sakalau ta yi da waya a hannunta cike da mamaki

Da sauri ta shiga lalubar number mijinta
Tana fara ringin ya daga dan shi din baya wasa da lamarin matar tasa,
Hankalinta a dan tashe ta shiga labarta masa komai, har kiran da hajiar ta yi mata kwanaki bata daga ba, da zuwan ABDUL, da kuma yadda suka kwashe da hajiar
Chapter 29 · 0% Book details