← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 83

Sashe 75

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya dan shafa shi yana sake kallon fuskarta zuciyarsa na dokawa da mugun karfi

Kasa kasa sosai ya furta"u'r sleeping like a baby"

A hankali ya sake shafa fuskarta ya kuma furta " U'r a baby , my baby, Wifey" ya idasa yana dan sakin murmushi kadan yana kallonta

A hankali ya ci gaba da tofa mata Adu'a har ya yi ya gama ya mike ya fice ya rufe mata dakin

Ta baya tmya rufe ya duka ya tura masu ky din ciki sannan ya koma nasa bangaren cike da bege da jin rashi a cikin zuciyarsa, sai dai kamar yadda ya kudurta ba zai takurata ba, idan dai hakan shine burin Amina zai hakura, ko menene ai in sha Allah ya tabata Allah zai sanyaya masa, balema ba wani abu mai karfi da ya wuce tarin kaunar abinda ke cikinta!

Sosai suka raya daren nan, bayan Risala ta yi masa rantse rantsen cewa ba zata kuma bari wani ya ji abinda ya shiga tsakaninsu ba, ta bashi hakuri na wanda ya faru, sun karra tataunawa a kan furucinta na gidan Baba mai shanu sun ganewa junna

Ta sha wahala a yauma , ta sha wahala sosai, domin ya kwana biyu da abin shima, a dole ya barta daga karshe domin irin nishin da take fitarwa kar ta summe masa

Da kyar shima ya samu barcin bayan sun tsaftace jikinsu yana jin yadda mararsa bata sakar masa yadda yake so ba, ama ba halin sake koma mata dan shi ba makaho bane ya gane kwarai ta yi hakuri ta jure kuma ta gaji dole ya tausaya mata ya barta ta huta

___________________________________

Washe gari ta kama asabar, ranar da ya ware ta hutu ce tunda ya tare da matansa, ya kasance yana gida ne tunda safe har wata safiyar, sallah kawai ke fitar da shi sai ko idan ana wani abu mai mahimmanci irin zuwa taaziya, ko zuwa wajen daurin aure, ko zannen sunna, da zarar an gama yake dawowa gida dan ya ware ranar ne dama wa iyalinsa

Kusan karfe goma bayan an kai Biyu wajen aski ta fito a nutse ta nufi bangarensa ba tare da ta yiwa Firdausi salama ba, dama ko da ta tashi a cike ta tashi kamar yadda ta kwonta a kufule, kamar zata tashi sama dan haushi da take ji na kowa da kowa

A nutse ta tsaya bakin kofar tana dan bubugawa kamar yadda ya zame mata jiki, bata fadawa waje ba tare da ta nemi izini ba sannan ta yi salama a amsa mata

A karro na biyu ta sake yin salamar , sannan ta ji muryarsa, duda bata yi tunanin samunsa a falo ba, dama ta tsaya a falon ne da nufin idan ta yi salama uku ba'a amsa ba ta shiga ta haye sama ta same shi a samansa

A hankali ta tura ta shiga tana baza dubanta dan ya lalubo shi a cikin kwayar idannuwanta

A hankali ta karru da kujerar dake gabanta wace bata san ta kawo inda take ba sakamakon kallonsu da ta shagalta da yi dan mamaki dake ciciyar zuciyarta

"Be careful please, don't injured ur ur self " Ya fada yana dan son tashi da dan karfi daga zaunen da yake kan Risala na saman cinyoyinsa yana dan shafa hannayenta dake waje sanadiyar karamar rigar dake jikinta, idannuwansa kuwa tarr a cikin na Amina

A hankali ta dauke idannuwanta ta dan juyar da kanta tana gyara tsayuwarta dan kar ya karaso ya tabata

Shima dan dakatawa ya yi bayan ya tuna da Risala a samansa ya koma ya zauna yana lumshe idannuwansa hadi da lalubo hannunta a hankali ya jimke dan abinda zai rike hakan yake so dan samun kwarin gwuiwar fuskantarta

Yawu mai dacin gaske Amina ta hadiye ta sake juyowa tana dan kallonsa, a ranta tana ayana' Namiji kennan, buhun kaya, watau ga Maina kaya ko? Har ka hau ka jida mata aiki ka sauka ka rike yar shila?, Shine ina fama da ciye ciyen cikin da ka dura min babu ruwanka na rayu ko na mace kana nan ka labe a jikin yar yarinya kamar a karyata dan shegen kasusuwa a wuya ko? Ba damuwa ni ba makashiya bace, zan haife maka na dire maka dan walahi babu wanda zai sakani zawarci da malulun yaro, an jima baa zageni ba!'

A fili kuwa , a dake ta ce" Wajenka na zo, ina son zamu yi magana"

Fuskarta da ta hade da cire kan da take ya saka shi shima a dan hade ya ce" Bismillah"

Juyowa ta sake yi gannin kadangaruwar tasa sai sake dago kai take kamar ta sha rana tana son innuwa kadan ko jin ƙishirwa, sannan ta sake kallonsa ta ga ita yake kallo da idannuwansa dake daf da kasheta dan kaifafan kallonsa sam ba risinawa a ciki

A hankali ta sake juyawa da nufin tafia, dan ta ga soyayar irin mai hawa kan nan ce tanada bukatar a basu waje

A hankali ya dubi Risala kasa kasa ya ce" Bab, dan bamu waje kadan kin ji?"

Sai da ta dan dago yana kallon idannuwansa ta mana masa kisss wanda tsaf a idannuwan Amina sannan ta mike taa nufi ciki firki firki tamkar zata karye biyu
Ita amina Al'ajabinema ke neman kasheta, oh yaren zamani jarabace cike da cikinsu, yanzi wannan yar ita kuma halin da ta saka kanta kennan a rayuwa? Jarabar maza? To Allah ya sanyaya

Zamansa ya gyara yana nuna mata wajen zama dan nesa da shi, a tsare ya ce" Bismillah"

Kujerar ta kalla, tana nesa da shi ainun, sannan ta kalli ta dan kusa da shi
Haka kawai sai ta ga harda rashin adalci a lamarinsa
Ama sai ta kyale shi ta barshi da halinsa ta je ta zauna a kujerar, itama ai gani take ta fi mata alkhairi fiye da kowace

A nutse ta ce" Dama, dama dangane da maganar makaranta ne, jiya twins ke ce min ashe ka cire su a wancen makarantar tasu, ni ban sani ba, kuma har ka saka su wata ta kudi duka ni ban sani ba, shine nace dama zan zo na ganka a kan hakan"

Sai da ta dire aya yana kallonta, shima a hankali ya ce" Eh an yi haka, ashe ban nemi izininki ba Amina, na cire su ne baki yarda ba?"

Idannuwanta ta dago cike da jin wani irin abu marar dadi, tana kallonsa a hankali ta ce" Aa ba haka nake nufi ba fa"

Gannin ya yi shiru ya sakata ci gaba da fadin" Dama na zo mu yi maganar ne, saboda na ji wace makarantar ce suka koma, saboda halin rayuwa idan bata yi mugun tsada ba, kuma na yi godiya"

Yanzunma jin shirun ya yi yawa a dole ta dago idannuwanta dake sade ta zuba masa ido

Sai ta ga ita yake kallo, ama ba da kallon nan na kamar zai cinyeta danya ba, kallo ne normal kawai wanda zaka yiwa irin wani wanda baka sani ba haka

Basarwa ya yi yana kauda kansa ya ce" Allah zai badaa yadda za'a yi in sha Allah"

Amsar tasa a dunkule, kuma yua ja ya tsaya, kamar ya gama maganar yake nufi
Ta dan jima tana cicira maganar, har dai ta rasa abin bilowa a kan maganar sai ta ce" Kuma, Kuma fido yau take ce min an ce ta shirya gobe ta fara zuwa, ta fara tafiya makaranta da kuma koyon girki da.........."

"Amina, abinda ya Kawo ki kennan?" Ya fada yana katseta

Tsuru ta masa da ido

ABDUL ya ce" Idan shine kina iya tafia it's ok"

Sake zuba masa ido ta yi zuciyarta na kunna da tafarfasa, watau ta tafi ta basu waje su dora daga inda suka tsaya ko?

Rai bace ta mike ta juya zata yi tafiyarta tana dana sannin zuwa yi masa godiyar nan, farin cikin da ta tsinta a fuskar kanwarta ya sakata nufo dakinsa, sai gashi yana wulakantata

"Zaki fara awo gobe, dan ya kai wata daya da sati biyu , zaki je wajen Mansur ya hadaki da doctern da zara ringa maki awo in sha Allah" ya fada yana kallonta

Rai bace ta juyo ta ce" Awon me zan je?

A dake ya ce" Awon ajiyar dake tare da ke "

"Ni babu awon da zan je, kuma da kake fadin adadin lokacinsa wani ya fada maka ne?" Ta fada cike da neman a yita ta kare

ABDUL ya tabe bakinsa yana gyara zamansa ya ce" Anya wani ya isa ya fada min bayan ni kadai na diga abina?, Sai dai na fadi ranar da lokacin da tsayin lokacin da ya dauka, Allah dai ya fido shi lafiya"

Kukan da yake ta so ya ganin ne aka fashe da shi, ta nuna kanta, sannan ta nuna shi ta ce" ABDUL, ni kake wulakantawa ko? Ba damuwa Ai damarka ce, ka wulakantani son ranka, ni ga banza ko? Ai na laifi samu ka yi ABDUL, kuma babu inda zani!"

ABDUL yana kallon fuskarta da kukan da ba hawaye ya yi dan murmushi kasa kasa ya ce" Ai ba damuwa idan baki je ba ni sai na aunaki a gida,sai an jima Amina"

Tsuru ta masa kukanta na daukewa, jama'a ga mari ha tsinka jaka? Itace ke gannin haka a wajen ABDUL dan ya gama da ita?
A guje ta juya ta fice a dakinta tana sakin kukanta bilhaki
Hajia ta tabe baki tana gyada kanta ta ce" Ni fa kwata kwata ban fahimci inda kika dosa ba, me kike nufi ne?"

A hankali ABDUL ya ce" Hajia ki saka yarinyar a nonon mana kar ta mayar?"

Hajia ta ce" Ok, ina zuwa"

Ta sake gyara Amina da kyau ta ciro nonon duka biyu ta talaba hannunta ta nuna mata ta saka macen a hannun dama, sannan ta saka namijin a hannun hagu ta saka Fido talabe mata shi kafin ta iya da kanta tana fadin " sai kin jure fa, akoy zafi*

Amina ta gyada kanta tana rintse idannuwanta, domin namijin kamar jira yake ya yi raf da shi, macen cema ake ta koya mata a hankali a hankali
Chapter 75 · 0% Book details