← Book details Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 83

Sashe 18

Ni Zan Ladabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A nutse Mai Shanu ya shiga bayanin abinda ke tafe da su, a tausashe da kalar fahimtarwa ya ringa fahimtar da shi abinda yake dauke da maganar , har ya dire aya da fadin" Wannan lamari na damuna Malan, yarinyar nan tana da bukatar taimako sosai, da ace zata samu da hankalinta zai fi kwonciya, ga rainon ya'ya bayan ita dinma yarinya ce"

Malan dan iya da kansa ke sade yana sauraronsu har Mai Shanu ya gama maganar yana ta dannar harshensa da irin magangannun da yake tufka masa mararsa dadi a zuciyarsa, yana kwabar kansa cewa ya bi a hankali dan ya ci ribar zaman ya fuslanci mai Dambu a yannayin da yake tunanin maganarsa mai ma'ana ce ya ce" Haka ne, Allah gafarta malan da Elhaji gaba daya na ji maganar nan, kuma idan na fahimta da kyau so kuke ta dawo gidan nan ta zauna?"
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️
_*NI ZAN LADABI*_
🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️🙇‍♀️

*NA*

*SAJIDA NIGER*

Asalamu alaikum wa rahamatullah, makaranta novel dina gani na dawo da sabon takarda, sabuwar tafia, sabon salo mai dauke da darusan rayuwa, da karfin ikon sunnah, da gwagwarmaya da kula kula, rayuwa ce irin ta talaka bawan Allah dake gannin hawa da sauka dan ya rayu da mutuncinsa, rayuwa ce ta Mace mai dauke da hatsari, sadaukarwa, Biyaya da karfi.......zai zo maku da shafuka na gyara tun daga kan fatar jiki, ppart, sirika irin na cikin kurya a gangaro kan sabulai na sana'a da kuma turaran HUMURA wace kowace mace zata iya yiwa kanta tsumamen hadin tada hankalin mai gida

Wannan Novel na kudi ne ba free bane

Yan Nigeria jama'ata ga naku : 500 Naira
account number: 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ka turo shedar biyanka ta numberta kamar haka +227 93811618 SAJIDA NIGER

Gareku wa'inda suke son turo kati ko yin POS, kunna iya turo katinku ta numberta kamar haka 93811618 idan ka turon hoton katin sai na saka ka a grup, katin MTN ne, na gode sosai

Jama'ata yan NIGER ga naku : Dala dari , 500 francs cefa ta katin AIRTEL ko SAHELCOM ka turo ta numberna kamar haka 93811618 sai na saka ka

*NA gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, sai kun zo🥰🥰🥰*

*Page 1️⃣1️⃣*

Furucinsa, har zuwa kafiyarsa da yannayinsa, da suturar dake jikinsa , kai harta da kalar fatar jikinsa sai da ta shiga aunawa da idan yana cikin hayacinsa, a hankali da mugun kula ta karra dubansa kasa kasa sosai ta ce" NA'AM?"

dukkan yannayinta yana kula, yana kuma hankalta, murmushi ya yi mata wanda ke tabatar mata da kwarai abinda ta ji shi yake nufi, ba gizo kunnenta ke yi mata ba, ba kuma a cikin hali na fitar hayaci ya yi bayani ba

Da sauri ta saka hannayenta ta dauke farantin dake ajiye a gabanta ta kawar gefe ta zauna tana tataro dukan nutsuwarta da hankalinta ta ce" Alkali, wasa kake yi da furucin nan ama ko? Ka kuwa ji me ka fada? My big son , My hero, Uban gidan yan siyasa! Uban gidan masu mulkin! Dan yanada baban kowa a banki, shine zaka dauko auren fari kace zaka hada da macen da ta girme shi, macen da ta gama yawonta, macen dake fama da ya'ya, macen da bata waye ba, macen da take tuyar waina da kosai tana siyarwa, macen da bakin fatarta sai ya makanta mutun idan ya matsawa kallonta? Plz ka fada min cewa wasa kake yi da furucinka!"

Mamakin abinda bai taba kawowa kansa cewa zai ji daga bakinta bane ya saka shi dora yan yatsunsa biyu saman lebensa, kwana uku da suka shige wanda ya yi maganar nan ya yi masa uzuri ya ajiye shi a matsayin wanda bai yi dogon karatu ba, yana fama da jahilci ya da ya yi aikin dana sani, a yanzu kuwa a wani bigiri zai ajiye iyalinsa? Shi dai sheda ne a kan irin karatun da matar gidansa ta yi, na bokon da na islamiya, shin jahilci shine sani a take sanin ko kuwa wannan din son kai zai kire shi da shi?

Turw komai ya yi daga cikin zuciyarsa ya ce" Shin haramun ne aikata hakan?"

Hajia kam abinda nema yake yi ya girmami tunaninta, har so yake ya ji idan haramun ne? Kennan so yake yi ya zauna a kan bakansa?
Dan kwalin kanta ta cire ta ajiye gefe , lalausan gashin kanta mai dauke da furfura ya bayana a tufke a bayan keyarta da dan karamin ribom ta ce" Ba maganar haramun, shin ina hadi a nan? Idan miji kake son yi mata ka sama mata daya daga cikin ma'aikatan gidan nan mana, in ka raina su ka duba cikin ma'aikatan ka masu takardar gwamnati ka bata mana, ama sai ka dauko jirgi ka hada da mota? Ai ya fi karfinta walahi! Ita kuma ta girme masa a shekaru ai hadin sam bai yi ba, a cenza shi!"

Kai ya gyada yana murmushi da tunanin lalle ya yi sake katon raini ya riga ya shiga tsakaninsa da iyalinsa, yana wanzar da rayuwar yanci da ita da shawara a dukkan abinda ya taso masu dan yana girmamata da darajata a rayuwa domin shi a ganninsa mace tana da damar zabi itama a tata rayuwar ba wai sai dai a ringa yanke mata hukunci da an yi niya ba, sai gashi tana neman maida hakan iko da isarta? Tana so ta manta yana raye kuma bai shirufce ba? Tana son take komai ta murje komai ta manta nata usulin?, Koda yake tana iya mantawa, domin halin rashin na dan lokaci ne suka yi kafin Allah ya warware, sai dai zai ji mamaki ainun idan ta ci gaba da nunawa talaka haka , takan manta Allah ya haliceta da ita da wanda bashi da shi, yana iya amshe dukkan abinda take gannin ta malaka ciki jarda jikan nata a lokaci daya kuma ya barta da ranta da hankalinta ta gani da idannuwanta?
Kai Allah ya wadaran naka ya lalace!

A tausashensa ya ce" To tunda dai ba haram bane ai an wuce wajen, nima da na aureki ai tserayar shekarun dake tsakaninmu nu har kunya na ringa ji a lokacin kar ace na auri yar cikina, gamu kuwa an yi tsayin rai du kanmu ya cika da furfura muna tare, wannanma ai aya ce Hauwau"

"Alkali" Hajia ta fada tana tsareshi da manyan idannuwanta gannin ya mike tsaye yana shirin yin gaba ya bar mata dakinsa da itace ta tardo shi

Juyowa ya yi fuskarsa a hade sosai ya ce" Look, ki saurara abinda kike shirin yi ko menene! Ki tausasa muryarki a kan tawa, ki saurareni da kunnen basira, Ni Alkali na ce na yanke hukunci Daura auren jikana da Maman Biyu nan da kwana hudu, na baki dama idan kina gagawar a hade da wace yaron ke kulawa matsayin soyaya ba damuwa, idan baki gagawa kuwa lokacin da kila shirya sai a daura masa ita, shi din ai mijin mace hudu ne a sanina, so bana son yawan surutu a kan lamarin nan, kuma na hanneki tarda yarinyar nan da wata maganar da zata zubar da mutuncinki a idaannuwanta, ki sani ya zama wajibi *KI YI MIN LADABIHHHH* , Idan ba haka ba lalle zamu bar abin kunya mai girma a duniya kafin kasa ta birni idannuwanmu!"

Yana gama fada ya fice ya rufe dakin ya sauka kasa

Hajia kam sai da ta yi summan hucin gadi kafin ta zabura tana sallalami da dora hannunta a saman kanta tana fadain" Walahi talahi ba zai yiwu ba, ni zaka wulakanta? Walahi ba zai yiwu ba, in ni ka fi karfina ai akoy masu yi maka magana, haka kawai dan tsufa ya zo maka sai ka hada yaro da abinda ba shikenan ba? Wani irin zaman aure ne zai iya yi da yarinyar nan? Ko hannunta zai iya tabawa ne? Kuma walahi ba za'a daura auren yar gidan honorable da gagawar nan ba, ni da nake shirya wannan rana ta yadda zan gayaci manyan yan siyasa su zo mu hadu a kashe koren arziki? Ba zaka taba sakani a jarida da yamadidin abin kunya ba, sauran titin zaka ba yarona? Haka kawai marayan Allah zaka wulakanta? Ba zai yiwu ba!"

Tana fadan ne kuka na neman kubce mata tana dadana numbobi

ABDUL RA'UF din ta fara kira, har sau biyu kafin ya kashe ya maido mata kiran

Tana dagawa kuka ta fashe masa da shi tana fadin " ABDUL ko me kake yi ka zo gidan nan a yau yau, walahi Alkali ba zai kasheni ba, walahi ba zai kashe ni ba, bai isa ba, *Ba zan yi masa ladabin ba!*, A kan wannan bukatar tasa ba zan taba sada kaina kasa ba!"
Chapter 18 · 0% Book details