← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 105

Sashe 99

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

dan kwanta amman bata wani cin abinci yadda ya kamata haka ne ma yasa jikinta yaki dawowa daidai umma da granny suka zo suka sakata a tsakiya "maryam taso muje kici abinci ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana girgiza kai "bana jin yunwa "haba maryama ina lura dake tun jiya baki sakawa cikin komai ba karki cutar da kanki domin rayuwa babu ci babu sha akwai matsala idan wani ciwo ya kamaki yaya kike son muyi da rayuwarmu . tayi murmushi kawai tana duban umma idan ma bazaki tausayawa kowa ba ki tausayawa ummanki cewar granny umma bata ce komai ba ta koma hannunta daya fuskarta dauke da murmushi granny ta riko dayan hannunta suka nufi kan kujera mai zaman mutun uku daita atare suka zaunar daita "umma da kun barni wallahi bana jin cin komai Aa bazai fa yuwu ba ko bakya jin cin komai ya zama dole ki sakawa cikinki wani abu kafin ta sake yin magan granny ta kai spoon din abinci bakinta murmushi kawai maryama tayi ta karba ta soma ci granny na bata umma na bata ."ta kai hannu ta karbi spoon din hannun umma nasan kema baki ciki komai ba ta dibi abinci ta kai bakinta "umma nah kici abinci ta girgiza kai tana shafa fuskar maryama sannna ta bud'e bakinta fuskarta dauke da murmushi. **** Maryama zaune a parlour'n ummah sanye take cikin wondo da riga yan kanti kanta babu dankwali yayinda gashin kanta ya zubo gadon bayanta gabanta qaramin table ne wanda ta daura farar takardar zane kasancewar ta samu aiki ta hanyar wata abokiyar aikinta yusira ,gefenta kuma tarin fararen takardu ne datai zane bata samu abinda take so ba ,sosai ta dukufa gurin ganin ta zana abinda ake bukata ,tana nan zaune umma tazo ta wuceta ta shiga kitchen byn wani lokaci ta fito ta dan tsaya tana dubanta kafin daga bisani ta koma ta cigaba da abinda take duk maryama bata dago ba dan sosai tayi nisa sai dai har zuwa wanna lokacin bata samu nasara ba ."har yanzu banga kinyi abun arziki ba keda zane baya baki wuya ta dago a galabaice tamkar zatai kuka "wallahi umma bansan dalili ba na kasa samun abinda nake so ni ma rasa abinda Ke damuna gabadaya na manta komai umma ta qaraso ta dafa kafadarta karki damu yarinyarta ki ajiye ki huta zuwa wani lokaci zaki samu abinda kike so Suna Cikin haka kawarta yusira ta shigo bakinta dauke da sallama sam maryama bata dago ba , ta dai amsa sallamar ta cigaba da abinda take umm ta fito daga kitchen tana murmushi "yusira ce agidanmu ? . "Nice umma ina yini ?Lafiya lau yusira ya mamanki ? tana lafiya ta fad'a tana zama kusa da maryama maryama kardai har yanzun baki qarasa ba gashi dashi nake son na wuce ?ta fad'a tana leka zane jirgin sama ne " uhm wallahi gashin nan fa yusura har yanzu ta kusan awa daya kenan banga alamun zata gamasa ba, kai tunda nake daita ma ban taba ganin zane data bata lokaci irin wannan ba . cewar umma tana gama fada ta nufi hanyar kitchen . Yusira ta biyota abaya "umma me zai hana da zaman nan da maryama take ta nemi aiki tunda ta gama tabarta,banki maganrki ba yusura amman maryama ce wani lokacin akwai taurin kai cewar umma da kuwa datayi kokari ta sake applied din aiki daya fi, kinga akwai wani compaing AGC dake bukatar ma'aikata nima zanyi applied kinga da sai munje tare abinda ma ya kawo kenan amman sanin yanzu bata bukatar yin aiki yasa nace na fara miki magana dan kinsan yadda zaki shawo kanta ciki sauki ta amince da zata amince hakika da naji dadi tunda zaman hk bashi da wani amfani banda tunani dake sa mutun amman Kinsan halinta idan tace bazatai abu ba to fa sai ahankali "Allah ya kyauta cewar yusura "amman Kinsan wani abu zan tura masu applications batare da saninta ba sai dai taji ankirata idan sun dauketa shikenan . gaskiya umma hakan yayi kuma naji dadi sosai ina son duk inda zan kasance muje mu kasance tare ai kwanaki yayi min ciwo data bawa subai,a aikinta wallahi umma da ina gari bazai yiwu ba "to Ke kuma banda abunki ai taimako tayi kinga tafi maryama bukatar aikin duk halin tsananin dasu maryama suke ciki sunfi subaia tunda su ko babu komai muna nan kuma bazamu bari su rayu cikin kunci ba amman subaia da abinda zasu ci ma wahala yake masu ?." "Haka ne kuma allah yasa mu dace mu samu aikin nan dan aikin a kafanin AGC ba karamin albashi ake samu ba ,samun aiki ma awurin yana daga darajan mutun shiyasa kullum cikin addaua nake akan na samu aiki a wajen , bari na baki mail dinsu da zaki tura masu sako tayi maganar tana kokarin ciro wayarta "to shikenan yusira na gode amman me zai hana ki tura min ta Kan waya kawai kamar zai fi sauki ? .""Eh ! Haka ne kuma bari idan na koma gida sai na turo miki duk wannna maganar da suke babu wanda maryama taji domin tayi busy akan zane Mmn Sudais MAR'ADAMS
Chapter 99 · 0% Book details