← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 105

Sashe 32

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

taji kunya ba zasu tsaya mata suyi mata komai hawayen da take kokarin boye n suka samu nasarar zubawa tayi saurin saka hannunta ta goge tana kokarin maida sauran dake kokarin zubowa ." A tsakar gidan su Aunty fati sukai cikibis da ummah aunty fati tace "yauwa ga aunty nan ma daman wajenki zan shiga yanzu "ina jinki me zaki shigo yi? tmbyr ya dan bawa aunty mamaki amman dai ta danne tace "muje daga ciki mu zauna muyi mgnr ai kamar zaifi ?A'a muyi anan "nan aunty fati ta zayyane mata komai tana dasa aya umma tace "a'a fati babu mai kamar maryama yayi shaawar bawa muktar aure "meye illarsa aunty ?tayi mgnr tana zaro mata ido itama ummah cikin zaro ido tace "illoli dayawa, na rasa meke damunku ?ta qarasa mgnr da karfi tare da yarfar da hannu ." "Aikuwa tunda har muktar yace yana sonta ko sama da kasa zasu hade sai anyi auren sai duk abinda zai faru ya faru "sama da kasa bazasu hade ba haka zalika babu abinda zai faru aure ne dai bazaa yi shi muddin kika ga anyi wannan auren to maryama ce da kanta taji tana so amman wallahi babu wanda ya isa yayi mata auren dole hayaniyarsu ce ta fito da aunty salma da aunty wani irin asirtaccen murmushi aunty salma tayi tare da karkacewa tana kallonsu .""Bata fada miki akwai wanda suke maganar aure dashi ba ?"ta fad'a amman wannan maganar karya ce babu kowa saboda duk abinda ke faruwa acikin gidan ina sane dashi, dan haka karya ne babu wanda yake sonta idan kuma har akwai ya fito mugansa " tana gama fad'ar haka umma ta juya zuwa bangaren ta, duk suka bi bayanta da kallo". Bayn kamar minti biyu ummah ta fito hannuta rike dana sadam a d'an rikice aunty salma ta maida kallonta sosai garesu "ba kowa bane illa sadam shine wanda suke soyayya da maryama."aunty ta tsura ma ummah ido idanunta na kawo ruwan hawaye."aunty salma zaro idanu tayi tana girgiza kanta bata so saka bakinta cikin maganarsu ba amman ya zama dole tace wani abu dan haka tace "umma yaushe suka fara so.."bata bari ta qarasa ba tace " bakiyi tsammanin faruwar hakan ba ko ? to haka rayuwa take salma sadam shine wanda zai auri maryama da izinin allah "ba aunty da Aunty salma da sauran mutanen dake tsaye ba shi kanshi sadam ya shiga rudani da tashin hankalin jin abinda mahaifiyarsa ta fad'a "taya ummansa zata masa haka ?" yaushe suka yi haka daita ."?yayi wa kanshi tambayar ajere yana had'a zufa . "Gsky wannan had'in yanzu ne ,wallahi a yanzu aka shiryasa ta kalli sadam "da gaske kuna soyayya da maryama ?kasa amsawa yayi dan gbdy ya gama daburcewa kwakwaluwarsa ta toshe kansa ya cunkusheya rasa me zai fad'a mata yayi dan duk abinda aunty salma ta fad'a haka ne a yanzu aka shirya komai kai shi sai da suka fito yasan dalilin da yasa mahaifiyarsa ta fito dashi "kun gani ba ai bazai iya cewa komai ba dan wannan had'in shirin yanzu ne sam sam babu maganar a kasa "Ke salma bana son makirci da shashanci banza d'anki ko d'ana ?" "d'anki ne amman wannan had'in yan.." babu ruwanki had'in yanzu ko akwai maganar a kasa naki ido ne idan kuma kikace zaki bi dare kibi dubu akan maganar nan zaki mutu ." "Kai sadam kalleni nan ya d'ago kwayar idanunshi da kyar ya kalli Aunty fati "karka boye min komai sadam kasan matsayinka a wajena ina sonka fiyye da ya'yan cikina nan kuma jikin ummah ya fara yin sanyi ,"nan ji duk abinda mahaifiyarka ta fad'a amman ina son naji gskyar magana daga bakinka ,da gaske ne sadam kana son auren maryama"? ya runtse idanunshi gam yana jin wani sabon tashin hankali na ta'ba zuciyarsa da kwalkwaluwarsa sai data sake tmbyrsa sannan ya bude idanunshi ya kalli mahaifiyarsa dake tsaye cikin tashin hankali tana dubansa ,a yanayin yadda take kallonsa bazai iya kunyatata a bayyanan nasi ba". "kai nake sauraro sadam wallahi da gaske zan iya bar maka maryama na nema muktar wata matukar kana sonta " jikin ummah ya sake yin dan tasan akwai soyayya a tsakaninsu ,"kace wani abu "da gaske ne aunty ?ya fad'a cikin wata irin murya mai cike da tsananin tashin hankali "aunty salma ta zaro ido tana cewa "kai wallahi aunty fati karya ne , babu wata soyayya a tsananinsu "kinga salma magana ta qare sadam nawa ne koda karya ne tunda ya amsa da bakinsa bani da ja domin soyayyar sa dabam ce acikin zuciyata "shiru aunty salma tayi dan ta dade dasanin son da take wa mahaifinsa ne ya juye kanshi .dariyar mugunta aunty salma tayi ta juya ta koma bangarenta abun bai mata dadi ba dan bata son maryama ta riga ya'yanta aure amman zata yi iya yinta taga ya'yanta sun rigata aure ita da take da suruki kamar yusuf me zai dameta da wani sadam gashi ga dukkanin alamun dole akayi wa sadam din zai aureta." aunty fati tace" sadam d'ana ina maka fatan alkhairi suna gama fadar haka suka bar wajen zuwa bangaren aunty hassana suna shiga aunty hassana tace "yanzu ke kin yarda da wannan tsarin"?nasan karya ne dole akayi masa amman tunda ta zabi haka ki zuba ido Kiyi kallon abinda zai biyo baya da wannan maganar suka kawo karshen zance suka shiga wata ."maryama na zaune cikin halin tashin hankali umma ta shigo parlour'n tana ganin ummah ta mike ta rungumeta tana kuka "ummah me nayiwa su aunty fati ?"me zanyi su soni ?wallahi banason muktar ki taimakeni ummah kar a d'aura auren nan laifin me nayi masu ummah ?ina ta bawa zuciyata hakurin rayuwa dasu, amman kullum burinsu suga bayana ."ta karashe mgnr tana kuka." "ki qara hakuri da kowa da komai akan wanda kikeyi maryama rayuwarki qaddara ce zuwa yanzu ya kamata ace kin saba da qaddararki karta dinga baki tsoro "wallahi ummah jarabawa bata bani tsoro saboda na maida alamarina zuwa ga allah "yauwa abinda nake son ji kenan kowa ce rayuwata cike take da lullubali da qaddara kuma sai allah yana sonka yake jarabaka domin yaga karfin imaninka idan kuma akace haka dole sai ka shirya, jarabawa ko ta class ce yaya kike jinta bare jarabawa daga allah? fatana allah ya bamu ikon cinye jarabawa ."ta fad'a tana shafa bayanta tana jin fad'uwar gaba ."tana Tunanin yadda zata shigo mata da zance sadam taji sautin muryar maryama tana cewa "ni dai ummah kisa abar maganar muktar ke kad'ai ce nake da yakinin zata min wannan gatan ." ummah ta zareta ajikinta ta kamo fuskar maryama da hannuwanta duka tana kallon fuskarta tace "babu wani muktar da zaki aura na yanke shawarar zaki auri yayanki sadam, maryama ta zaro idanu tana duban umma cike da matsanamcin mamaki "yaya sadam kuma ummah ?"a matukar rikice ummah tace "Eh ko baki sonshi."ahankali ta shiga girgiza mata kai domin dai tasan ko giya ta sha bazata iya furta hakan gareta ba ,bare kuma tasan tayi hakan ne dan yantota daga hannunsu aunty fati ."ai ko bata son yaya sadam ta karba kuma ta amince sai dai fargaban yadda yaya sadam din zai karbeta muryarta a raunane tace "ummah kina tunanin yaya sadam din zai amince "ya ma amince maryama "kuka ta fashe dashi mai karfi "shikenan mafarkinta ya tabbata"ya allah kabani kwarin gwiwar cinye jarabawar da duk zaka min "alhamdulillah alhamdulillah shine kawai abinda umma taji yana fitowa daga bakinta "allah ne abun godiya maryama babu abinda zai biyo bayan wannan auren sai alkhari, karshen wahalarki yazo ta fad'a tana sake rungumeta ajikinta " aunty ta qaraso ta zauna kasa kusa da kafafuwan ummah "ban san da wace irin kalmar godiya zanyi amfani dashi wajen gode miki ba amman zan zabi wannan kalmar allah yay miki sakamakon da gidan aljana "na gode na gode !!sai kuka ya kufce mata daga maryama har Aunty suka saka ummah tsakiya suna mata kuka ." koda habib ya dawo yaji hukuncin ummah abun yayi masa dadi sosai dan gara sadam sau million akan wani muktar fatan alkhairi yayi yana tmbyr aunty maryama .""Tana d'aki !" ta fad'a atakaice tana sauke numfashi a daki ya iske maryama kwance akan katifa tayi kuka har idanunta sun kunbura tana tunanin yadda qaddarori suka yita zuwa mata daki daki akan aurenta a she tana tare da mijinta bata sani ba "ya zauna kusa daita yana kiran sunanta "heartbeat ".ta sauke numfashi tana dubansa da kunburarrun idanunta "bakiji dadin hukuncinsu umma ba ko ?ta langwabar da kanta kawai batare da tace komai ba "heartbeat idan da wani aka baki zance Aa amman yaya sadam dabam ne karki ce aa bazaki samu kamarsa ba " "kai ma ka amince dashi ?sosai kuwa dan mutumin kirki ne kuma yana duk wasu quality's da zaa so shi ta sakar masa murmushi wanda ya bayyana wushiriyarta sama da kasa tana gyara kwanciyarta ta jingina bayanta da abun gado ta janyo pillow ta rungume tana jin wani nauyi a qirjinta"bana jin son yaya sadam ko kad'an acikin raina amman bani option zan rayu dashi muddin rai "yayi shiru kawai yana kallonta cike da tausayawa dan bai san me zai sake cewa ba ,domin farincikinta farincikinsa ne haka zalika damuwarta damuwarsa ne zai sake magana ta katsesa ta hanyar cewa "karka ce komai after dad tunda har ka amince daman kai kawai nake jira naji raayinka tana gama fadar haka ta sauko "muje parlour'n muci abinci ta riko hannunsa binta kawai yake jikinsa a sanyaye ." ******* Tun bayan da ummah ta furta maganar aureta da yaya sadam habib bai zauna ba ya shiga buga bugan neman aiki karfi daga wannan kamfani zuwa wannan duk kuma saboda ita da mahaifiyarsu ne daman da karatu da kwallon kafa ya dogara dan yana d'an samu a buga kwallon kafa amman ba wani samu sosai ba dan kudin ba wani kudin azo agani bane amman babu laifi yana toshe masu wata kafar dan hatta mashin din da yake dashi yanzu da dan kudin da yake samu ya siya ."matslar dai ba koda yaushe ake samu ba sai a dauki alokaci baa daukesa ba shiyasa yaga gara ya had'a da aikin kamfani ranar da'akayi
Chapter 32 · 0% Book details