Sashe 51
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a tashe ki koma ki zauan nace. ya fad a a tsawace adaidai lokacin da kiran mami ya shigo wayarsa ko da bai duba wayar ba zuciyarsa ta sheida masa mami ce ya ciro wayar yana dubawa cikin fushi yace ga sweetheart zatayi magana dake na rantse da girman allah idan kika sake ta fahimci wani abu sai gana miki azabar data fi ta kwanaki hud u da kikayi ciki, kuma sanin kanki ne Adam zai aikata fiyye da haka akanki . zuba masa ido kawai tayi hawaye na gangarowa akan kuncinta ki d auke wad an nan banzayen idanun naki akaina ai tunda kika nacewa aurena ni ne zanyi sanadin mutuwarki dan tun tuni naji rashin alkhairi akan aurenki ,kinga idan kin mutu ni kuma na tsinci kaina a prison hankalin ke da sweetheart zai kwanta amman tabbas ina ji ajikina idan baki kasheni ba ni zan kasheki ya fad a yana nuna ta da d an yatsansa. Batace komai ba illa kanta data dukar qasa kamar yadda ya bukata tana sauraron bakaken maganga nusa akanta ,yayinda jikinta Ke karkarwa saboda tsananin yunwar da take ji yadda bana son auren nan ko sau d aya ki fito kema kice bakya so amman kinki furtawa sai ma nuna alamun son zama dani wanda hakan babu abinda zai janyo miki sai bala i da tashin hankali , wallahi wallahi kinji na rantse dana zauna dake har qarshen rayuwata gara na kasheki na qarar da sauran rayuwata a prison. cike da tarin damuwa ta d ago idanunta duk sun cika da kwalla tasan tunda ya rantse tabbas zai aikata abinda ya fad a indai bata bar rayuwarsa ba wallahi sweetheart bata min adalci ba kuma ta cutar dani domin tayi min abinda yasa na qasa mata biyayya , maryam ta sake kallonsa cike da mamaki wallahi sweetheart bata min adalci ba kuma ta cutar dani ta maimaita abinda ya fad a afili yes haka nace shima ki kwashe ki fad a mata dan kin iya munafurci har kingaji ,ko da yake ai siffar munafukai gareki ,ahankali muryarta ta fito yaya adam kayi hakuri dan allah karka bata ranka bazan fad a mata komai ba tana kaiwa nan sai wasu hawaye Dan allah malama bana s n munafurci ki daidaita natsuwarki ga waya kuyi magana daita da sauri ta goge hawayenta da hannuwanta duka tana shafa qirjinta dan dawo da natsuwarta sannan ta mika masa hannunta wai kallon banza yayi mata yasa wayar a speaker yana rike da wayar hello tajiyo sautin muryar mami zuciyarta cike da rauni tace hello mami ina yini yauwa maryam lafiya qalau daman dake nake son magana lafiya naji muryarki haka ?ta kalli inda ATA yake ,mugun kallon daya dauketa dashi ne yasa ta dauke kwayar idanunta akanshi , ta kalli cikin wayar lafiya qalau mami to mai ya samu wayarki an kiraki bai shiga ?maryam tayi shiru tana jin rauni atare daita mahaifiyarki tun shekaranjiya take neman layinki ni kuma tun jiya nake kiranki haka ma auta idan akwai damuwa ki fad a min ta waiga ta kalli ATA dake binta da mugayen idanunshi adamcy na wajen ne ? uhm !ta bata amsa atakaice,okay kina jina zan miki tmby idan gsky ne kice eh! idan karya ne a Tun daga ranar da abun nan ya faru a tsakaninki da adamcy ya kwana a gidan ? muryarta na rawa tace eh !mami tayi shiru can tace mikawa adamcy wayar ai wayar tana hannunsa mami ta furta aa ! cike da tsananin mamaki mami tace wayar ma bazaka iya bata ba kamar wata mugun abu ?aransa yace ai ta zarce haka acikin zuciyata amman a fili cewa yayi ina jinki sweetheart muje what sapp tana gama fadar haka ta katse kiran ta kirasa vedio call ido cikin ido suke kallon juna tace ina maryam take ? ya haska mata fuskarta dake kode alamun wahala maryam natsu ki fad a min gsky babu abinda zai iya miki me ya sameki duk naga kin dawo wani iri haka me kuwa zai sameta ? wai sweetheart mai yasa bakya son zaman lafiya ne ? kin tmbyi yarinyar tace babu komai ,kina son lallai sai ta kirkiro karya ta fad a miki akaina Ke dan ubanki meke damunki ? ya fad a a tsawace maryam tayi saurin girgiza kai tana cewa mami babu komai ! adamcy karka nemi ka raina min hankali maryam fad a min gsky gani nan zuwa yanzu a mami dan girman allah karki zo wallahi babu abinda yake min kawai dai kwana biyu bana jin dadi ne wato adamcy dai ka raina ni da gsky me kuma nayi sweetheart ? taya yarinya bata da lafiya har tsawon kwanakin nan amman kai daka ajiyeta baka sani ba ? wa kenan ya ajiyeta sweetheart ? inna lillahi! mami ta furta ai maganar gsky ne sweetheart ni ban ajiyeta ba ba kuma zamana take acikin gidan ba, zamanki take dan Ke kike aurenta bani ba okay haka ma zaka fad a min ? am sorry sweetheart amman kin dade dasani zamanki take acikin gidan nan okay har kana sake jaddada min? to wallahi bazaka qara jin dadina ba haka kawai ka dinga ganawa yarinyar mutane azaba laifi ne dan ta rufa maka asiri ta aureka ? wace azaba kuma sweetheart yarinyar da babu abinda Ke hadani daita, ya kalli maryam Kiyi mata bayani mana kinyi shiru kina kallona da wata munafukar fuskarki ?maryam kam shiru tayi ta tsaya tana kallon fuska mami ,ya sake mata alamar tayi magana akaro na biyu a matukar fusace Ke kina hauka ne ya buga mata tsawa ki bud e baki mata bayani Allah babu abinda yake min karki sake ki min karya maryam wai sweetheart me nene haka ne ?ya kalli maryam yana cewa wallahi idan baki bari ta yarda babu komai ba sai na canza miki kamani, ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali tace mami dan girman allah ki bar maganar nan ni babu abinda yake min kawai zazzabi dare nake fama dashi kuma walalhi laifina ne ban fad a masa ba nasan dana fad a masa zai kai ni hospital ko ya kira min doctor tana gama fadar haka ta juya kafin mami ta sake cewa wani abu . mami tayi shiru tana dubansa ta cikin waya sweetheart kinyi shiru me zance adamcy tunda kafi karfina ka rainani ka nuna min ban isa da kai ba duk lokacin da nace ga abinda zakayi bazakayi ba amman wallahi bazanyi kaffara ba muddin ba cigaba da zaman lafiya da maryam a cikin gidan nan ba na rantse da girman allah babu ni babu kai ki kwantar da hankalinki sweetheart kin ma kusan rasani gabad aya bangane na kusan rasaka gabad aya ba ? eh mana na zabi mutuwa akan cigaba da rayuwa da wannan munafakar yarinyar akowani lokaci zaki bud e idanunki baki ki daina ganin adamcynki bazaka iya aikatawa kanka komai ba kai fa muslimi ne kuma kasan hukunci haka addininance dan haka ka bar maganar nan bana son na sake jin ka fad a kazo gobe akwai maganar da nake son nayi da kai mai mahimanci,amman dan allah na roki arziki ka bar yarinyar maryam ta samu natsuwa acikin gidan nan naji !iya abinda ya fad a kenan sukai sallama. Maryam na shiga dakinta ta rushe da kuka tana cikin kuka wutan gidan ya kama sai datayi kuka mai isarta sannna ta janyo wayarta ta jona caji ta fito lokacin baya parlour n kitchen ta nufa direct aiko taga key makale naunayen ajiyar zuciya ta sauke tana godewa allah cike da rawar jiki ta kai hannunta tana waigen bayanta babu alamunsa ta zare key daya ta tura cikin rigar nononta sannan ta murd a kofar ta shiga ta bud e fridge duk abinda Ke ciki da d an sanyin amman da zai sake d aukar time zasu tashi aiki ire iren abincin data saba ci tana ajiyewa a firdge shi ta dauko tasa a microviw cikin mintunan da basu wuce uku ba yayi zafi jikinta har rawa yake wajen fito dashi . a kitchen ta zauna taci nan da nan zufa ya rufe ta da kyar ta mike ta ajiye plet acikin zink ta sake bud e frdge ta d auki vatermilk ta kafa abakinta bata ajiye kwalbar ba sai data shanye tass sannna ta ciro apple da inibi ta daura akan plet ta yayyaka kanana ta dawo d akinta koda ta shigo wayarta ta kunna kanta ta kulle dakinta ta zauan ta dauki wayarta ta hau what s app tana duba sakwanin kawayenta suna ta tambayata ina ta shige kwana biyu wasu kuma suce wai dadin aure yasa yanzu ta rage hawa online ita dai dariya kawai take musu tana fad a masu yadda tayi mugu kewarsu bayn ta gama dasu ta kira mahaifiyar ta sun jima suna waya inda take jaddada mata lallai taje airport gobe ta karbo sakonta tun washegarin ranar da sukai magana ta aiko . Washegar da ATA zai fita bai bada umarnin cire wutan gidan ba sai dai ya zare key kitchen ya wuce dashi koda ta sauko taga babu key ta fashe da dariya har da tafa hannu ta koma d akinta ta d auki waya ta turawa auta sako akan abinda yayanta yayi tana dariya nan take nana hauwa u ta kira suna masa dariya maryam tace ga keyn dana sace zanyi amfani dashi wallahi sister wannan yayan naki mugu a duniya babu kamarsa ,ki dai bi ahankali kar ya gane azabtar min dake kunnenta makale da waya ta sauko ta bud e kitchen lafiyayyen breakfast tayi mai kyau tana ci suna waya da nana hauwa u bayan gama ta sallami nana hauwa u ta bar gidan batare da izinin ATA ba zuwa airport ta karbo sakonta a parlour n gidan ta tsaya tana bud e bakar jakar dake rike a hannunta wata yar qaramar tukunya ta gani ta sauke numfashi tare da maida tukun yar cikin jakar ta mike ta shige d akinta tayi masa kyakkyawan ajiya acikin duro dinta har zata rufe durowar idanunta ya sauka akan littafin addu oin da mami ta bata lokacin da zata tare ,ta dauka tana dubawa ko sau d aya batayi tunanin ta duba tayi amfani da