Sashe 26
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
,allah ka sanyaya zuciyarsa akaina ,allah ka juyo min da hankalinsa gareni ka bamu zaman lafiya tana kuka wayarta na ringing wanda kuma tasan nana hauwa'u ce amman ta kasa d'auka domin dai kota dauka daga mata hankali zatayi kawai da kyar ta mike ta nufi dakinta ta kwanta lamo tana neman mafuta akan zamansu . Sosai zuciyarta da kwalkwaluwarta suka shiga tunani Ya kamata yaya Adam ya dandani zafin so ko dan yasan martaba da kimar son da take masa, to me ya kamata nayi ? ta tambayi kanta dan dole akwai bukatar na tashi tsaye na kwatarwa kaina yanci a wajensa shiru tayi tana son mijinta bazata iya rabuwa dashi ba ,dan ko da wasa bazata iya furta masa ya saketa ba sannan bazata iya ta ba bashi damar ya had ata da kowace mace ba taya kenan zai d andani zafin so bare yasan darajanta ."? Zumbur ta mike zaune dawa ya kamata nayi wannan shawara ?nan take kwalkwaluwarta ta bata amsa da sister mana ita kad ai ce zata baza baki shawarar yadda zaki yi ta mike ta isa inda ta ajiye wayarta ta soma kirata alokacin tana zaune a parlour n tare da yaya hisham tana shirin mikewa domin ta shiga dakinta ta amsa wayar yaya hisham ya zame ya kwanta akan cinyarta yana d auka remut dole tasa wayar a silet dan karta damesa ta cusa hannunta cikin sumar kanshi tana jin sanyi aranta dan batayi tunanin zai kwanta a saman cinyarta ba duk tunaninta barin gidan zaayi yaje gurin nuzla . Ahankali ta cigaba da shafa sumar kanshi ta d an kai bakinta daidai kunnensa sai da ta sakar masa murmushinta sannan tace abinci fa ?wani zazzafan numfashi ya sauke yana qara narkewa akan cinyoyinta masu laushi da kyar ya fixgo magana zanci sai na gama kallon new yayinda maryam sai faman kira take baa dagawa oh my goodness wai me yasa sister bata daukar waya ne ?ita kanta nana hauwa u tana son ta d auka amman bata son ta damu mijinta kuma bata son yaji abinda zata fad a sai dai hankalinta ya rabu gida biyu wani yana tare da mijinta wani kuma na wajen maryam bini sai ta kalli screen din wayar taga kira na cigaba da shigowa a karshe dai yaya hisham yace lafiya ? Me ka gani ?kamar baki da natsuwa wake kiranki ? maryam ce! ta bashi amsa atakaice ya d ago idanushi ya tsura mata ki d auka mana kika san damuwar da yayanki ya qunsa mata take son tayi magana dake shiru tayi dan ita kanta tasan haka ne amman dan kawar da maganar tace kai yanzu tunaninka kenan amman lafiya lau suke zaune taya za a zauna lafiya da wannan yayan naki mai shegen taurin kai kamar na kafuran farko . A firgice nana hauwa ta kallesa kina kallona karya na fad a ?tasan gsky ya fad a amman meye na sake fad a mata ?ta sake duba wayar zata mayar ta ajiye ya karba ya d aga tare da sakata a hands free nan take muryar maryam ta bayyana cikin fashewa da kuka sister ina kika shiga ne tun d azu nake kiranki ina cikin damuwa wallahi zuciyata kamar ta fashe ki bani shaawara ya zanyi da yaya Adam wallahi idan aka cigaba ahaka komai zai iya faruwa dani Sister ! nana hauwa ta kira sunanta ina jinki sister ina bukatar ki bani shawara sister yaya zanyi da yaya Adam ya zaayi ya dan dani zafi so ?ina son yaji zafi da ciwo kamar yadda nake ji ,sonshi yayi min yawa murmushi nana hauwa tayi wannan kuma ai abinda muka dade dasan ne kece daman kika kasa yarda da hakan maryam bata san sanda hawaye ya zubo mata ba tace amman kisan cewa yayi kar na kuskura na kamu da soyayyarsa domin muddin mayi haka na d'aukarwa zuciyata wahala dan kuwa mummunar ciwo ne zai kamani a karshe na rasa rayuwata gabad'aya ,gara na cigaba da rayuwata haka batare dashi ba domin ni a kowani lokaci zai iya rabuwa dani saboda yayi matukar tsanata ." Yaya hisham yayi saurin runtse idanunshi yaji zafin kalmar ahankali yaji zuciyarsa na yi masa zafi kamar zata fito waje tausayin maryam ya kamashi Yayinda nana hauwa tace subhallah gsky yaya Adam bai kyauta ba sam abinda yake baya kyautawa amman ki bari zamuyi waya zuwa gobe yanzu bani kadai bace tana gama fadar haka ta katse wayar gbdy kinga irin muguntarsa ba wallahil azim adam mugu ne sam sam zuciyarsa babu imani bare tausayi babu imani acikin zuciyarsa yana gama fad ar haka yaja tsaki ya mike tsaye ya shige d akinsa . Nana hauwa tabi bayansa da kallo tasan yayanta bai da kirki amman me zasu iya yi akai ? yayyunta ma baya jin maganarsu bare ita da ko kusa da inda yake bata isa taje ba matsawar bashi ne ya bukata ba . tana zaune yaya hisham ya fito da key din motarsa ya nufi kofar fita ta mike da sauri tana cewa ina zuwa kuma ?fita zanyi baka ci abinci ba fa?ya juyo ya tsaya tare da tsura mata ido kawai yana qare mata kallo batare da yace mata komai ba kafin daga baya yasa kai ya fice daga parlour n ya barta tsaye cikin tashin hankali dan tasan wajen nuzla zashi zama tayi tare da zabga tagumi . ******* Tashin hankalin da ba'a sa masa rana wayewar gari yau din nan subaia suka tashi da mutuwar mahaifinta sosai suka shiga tashin hankali ita da kannenta wanda baki bazai fad'a ba tabbas rayuwarsu zata sake shiga cikin matsala babba yanzu saura abinda ya rage masu mahaifiyarsu ce itama kuma ba wani isashen lafiya gareta ba lallai suna cikin tsaka mai wuya basu da mataimaki sai allah shiyasa sunyi kuka kamar me maryama taje ta kuma ta tausaya mata matuka dan tana tausayin kanta amman idan ta tuna rayuwar subai'a sai taga gara ita akanta from rich to poor is not easy . a bayan can mahaifinsu mai arziki ne sai dai bai yiwa kanshi tanadin komai ba har zuwa lokacin da yayi accident ya samu matsala a bayanshi ."alokacin da yake tsaka da jinya sai yayi tunanin da zaman da yake na rashin sanin ranar warkewarsa mai zai hana bazai hada kwssamominsa da abokansa guda biyu ba tunda shi bazai iya komai ba su kuma daman ba wani samu suke ba kusan a karkashinsa suke samu alhj sani da alhj dan umma ,tofa tun daga wannan lokacin daya hadasu komai ya sauya agareshi domin kuwa babu abinda ya biyo baya sai danasani dan kuwa tunda suka fara samun kudi suka juya masa baya basuyi tunanin su taimaka masa ba. tun suna masa naci har yazo ya gagaresu sai rufin asiri allah mahaifinsu na cikin wannan halin mahaifiyarsa ta kamu da hawan jini ga diebites daman tana dashi , shekaru biyar yayi yana jinyar sai yau rai yayi halinsa aunty tazo da ummah zaune su subai da kanneta suke wajan gaisuwa amman da ka kalli fusk'okinsu kasan suna cikin rud'u da tashin hankali ."sai dai fatan samu sausauci daga Allah. Ranar asabar da misalin karfe tara na safiya bayan an shirya komai na bangaren umma tsaf yayinda aunty salma tayi duk wani shiri domin janye zuciyar yusif ta hanyar malaminta ya koma kan soyayyar daya daga cikin yayanta , kausar data gama gaisawa da umma ta fito neman maryama tana kwance acikin kalubalin rayuwa da yake zuwan mata lokaci lokaci ita gbdy ma data sanin girmanta take domin gara tana yarinya radadin rashin mahaifi ne kawai Ke damunta da kuma cin zarafin yan gidansu amman bata taba kwana da abinda Ke daga mata hankali har ya hanata runtsawa ba ." Da gudu kausar ta fado kanta tana cewa masoyiya I miss you a lot duk da halin qunci da take ciki bai hanata nuna mata itama tayi farinciki da zuwanta ba "wallahi gidanmu kullum zanceki muke kowa mamaki yake wai yaya yusif yaga mace Kuma yana sonta har kuma ya kasa samun sukuni saboda ita tayi shiru kawai domin neman take ta daurawa zuciyarta damuwa acikin kahon zuciyarta domin dai ita tuni ta rufe babinsa da komai rayuwarta kawai take "dan Allah masoyiya ki tashi ki shirya yana parlour'n umma nasan ke kadai yake jira ." Maganarta ta bata mamaki to idan haka ne ina batun baba gali da yace yusif din ya amince da auren shikura abbanau ya yarda da batun da baba yaje masa dashi maryama batayi nauyin baki ba kamar yadda ta saba tace ai ina ganin Ke akwai abinda bakisani ba kausar ta kalleta cikin rashin fahimta tace "kamar me fa ?bayan tafiyarku baba yace sunyi magana da abbanku an maida wa yusif shukura amatsayina kausar ta zaro ido tace "saboda ana hauka Ke waya ya fad'a miki wannna" baba !" Sakina da shikura kuwa duk wani abinda ya Kamata aunty salma tayi masu wanda zasu jewa yusif dashi dan hK suka shirya cikin hadaddiyar kwaliya mai daukar hankali suka dauki abinda aka tanada domin shi suka nufi bangaren umma yana zaune jin tafiya yasashi fad'a da murmushinsa har wani mikewa yayi amman ganin sabanin abinda zuciyrsa Ke mararin gani ya dauke idanunshi daga kallonsu sukai sallama cikin siririyar murya tare da durkusawa suka ajiye mishi farati gabanshi suka zauna "ina kwana ya kuma hanya ? ya dan kallesu "sannna ya tsaida kallonsa akan sakina yana cewa "kece sakina ?" "Eh nice tayi mgnr tana sunkuyar da kanta "sannuku da kokari atare suka sakar masa wani kayataccen murmushi "me mukayi na Godiya batare da ya kalleta ba yace ya cancanta na gode tunda kunyi aikin da baku ya kamata kuyi ba maryama ta baku wahala domin wannan aikinta ne tazo gareni da abinda zan saka abakina idan ma da hali ta ciyar dani gbdy jikinsu yayi sanyi ta gyara zama "ai ya cancata muyi maka haka ya dan gyara zama sannna ya fuskancesu da wani iyayi da suke masa "akan me kenan ?sukai shiru hankalinsu ya soma tashi "tabbas wannan mutumin mai wuyar shaani ne idan da hali ma suce masa dan wulakanci, akace daya daga cikinmu zata iya maye gurbin maryama a wajenka ko baa fad a maka bane .