Sashe 85
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ATA kusan mintuna goma sha ya d'auka sai gashi ya fito tare da furta "kika ce kice kika zana ni? Kamar tace masa a'a dan taga abun nasa akwai rainin hankali ciki .amman sai ta tsinci kanta da jin tsoro dan haka ta maida kwayar idanunta ta lumshe masa tana wasa da agogon tsarka hannunta wanda ya qara wa zanen lallenta kyau ,lallen yabi da wani shu'umin kallo tun da yake bai ta'ba ganin zanen lallen da yayi masa kyau har ya d'auki hankalinsa ba sai nata yaji kamar ya kamo yatsun hannunta ,ya d'ago idanunshi a natse ya kalli fuskarta nan da nan idanunsu ya tsarke cikin juna wannan karon sauri cire kwayar idanunta cikin nashi tayi tana mai kawar da fuskarta gefe tare da danne bugun zuciyarta "shi kuwa wani yanayi ya tsinci kanshi ciki mai sarkakkiya da wuyar misaltuwa sakamakon idanunsu da suka sake tsarkewa cikin juna abinda ya lura atattare daita itama tana da jin kai da miskilanci"a natse ya sake bin zanen lallenta da kallo wani irin kallo ta watsa masa gabanta na fad'uwa wanda ta rasa dalilin jin haka ." Ahankali ya samu waje akan kujerun kushin dake office din ya zauna batare daya bata umarnin zama ba "bata zauna ba sai ma idanunta data tsura masa tana kallonsa tana sauke numfashi dan itama taci alwashin bazata yi mgn ba har sai yagaji dan kansa yayi . abinda batasani ba shi ko ajikin ATA da zasu kwana a haka ma bazai damu ba abinda yasani ne ba zai barta taje koina ba har sai tayi masa abinda yake buqata daga gareta ."ya lumshe tsumammun idanunshi yana jijiga kafarsa d'aya yana jira daga gareta ."a qalla sun kusan minti talatin yana zaune ita da segun suna tsaye ta kalli agogon dake d'aure a hannunta a karo na kusan biyar a kasan ranta taja qaramin tsaki bata san me ya janyota zuwa wannan aiki ba nan take kwakwaluwarta ta shiga aikin neman mata mafuta ."kafin ahankali ta samo zance zuci"maryama dole ki ajiye komai ki qarasa gabansa Kiyi masa magana idan aikin nan zai yuwu ayi idan bazai yuwu ba ya sallameki ki kama gabanki tun kafin hakurin mijinki ya qare"da sanyi jiki take qarasowa zuwa inda yake ahankali ahankali har ta iso ta zauna a kujerar dake facing dinsa "wani irin zane zanyi "? tayi tmbyr cike da sanyi murya "ahankali ya motsa lip's dinsa "ina kayan aikinki ?da hanzari ta bud'e jakar kayan aikinta ta fito da kayan aikinta tare da janyo kujerar gabanta zata ajiye ta jiyo sautin muryarsa "ba'a nan zakiyi ba ya fad'a tare da mikewa tsaye "biyoni ! " fitowa sukai daga office din yana gaba tana biye dashi haka ma segun yayinda gbdy hankalinta ya rabu gida biyu wani yana gurin mijinta wani yana gurin ATA ."wani office ya shiga daita kai tsaye gaban wani farin baod yaja ya tsaya tare da jingina jikinsa da bango segun yayi saurin janyo kujeru guda biyu daya a gaban baod din dazaayi zane d'aya kuma a inda ATA zai zauna "sir ka zauna ! ya zauna tare da daura kafarsa d'aya akan d'aya jiki a sanyaye maryama ta zauna tana jiransa sai daya gama shan kamshinsa sannna ya sallami segu ya fara mata bayani tana jin ya fara magana ta d'aura hannunta akan boad ta fara fidda kyakkyawar shep din jikin zanen da yake buqata , yana mata bayani tana zanawa lokacin data zana karan hancinta taji wani mummunar tsoro ya shigeta cak ta tsaya ta kasa cigaba da zanen da take ta tsurawa baod din gabanta ido kwaayr idanunta ta zana da hancinta har ma da yanayin jikinta babu abinda yazo zuciyarta kamar zanenta data gani a office din m . malik nan da nan gumi ya shiga tsatsafo mata a goshi da karan hancinta.shi kuwa gyara zamansa yayi sosai yana kallon zanen lallen hannunta da yadda take tafiyar da aikinta bai san ya'akayi ba yaji saukar hannunsa akan hannunta yana shafawa ." Cikin gigita gangan jikinta ya kama rawa wanda yasa ATA ya dawo haiyacinsa sai dai ya kasa d'auke hannunsa ajikinta da kwayar idanunshi wani irin tsoro da matsanancin firgici ATA yaga ya bayyana afuskar maryama ,yayinda zuciyarta ta shiga bugawa da karfi numfashinta ya soma barazanar d'aukewa, cikin sanyin jiki ta sabule hannunta cikin bacin rai tace "meye haka ?"dan allah aiki nazo yi banason irin wannan wasan iskanci mai barazana ga rayuwata wannan ya zamo karo na farko da qarshe karka sake kuskuren sake kai hannunka jikinta "ta fad a tana jan tsaki" ajiyar zuciya ya sauke tare da kafa mata tsumammun idanunsa cikin sayin murya yace "look at me ta kallesa Kmr yadda ya buqata babu wasa acikin kwayar idanunshi "Kinga nayi miki kama da dan iska ?sosai kuwa dan gashi naga alama daga zuwa aiki sai ka bige da kai hannunka jikina batare da kayi laakari da ni din matar aure bace ko kuwa budurwa bace ".hakan nan yaji ya tsinci kanshi da adduar allah yasa single ce ba matar aure ba ya sake kai hannunsa tsintsiyar hannunta tayi saurin zare hannunta har agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta ya zame cikin nashi wai meye haka dan allah nifa matar aure ce kuma tare da mijina nazo aikin nan ta fad'a hankalinta a matukar tashe shiru yayi yana qare mata kallo qirjinsa na wani irin bugawa da matsanancin karfi wanda baya jin haka akan kowace mace sai akan mafarkinsa. ahankali ya motsa labbansa "ko zan iya ganin fuskarki ?"ya tmbyeta yana qara gyara zamansa "no !ta bashi amsa a matukar tsorace ya sauke numfashi tare da mikewa tsaye ta sake ja baya tana cewa "karka matso kusa dani domin bazan ta'ba kasancewa cikin wawayen mata masu cin amanar mazajensu ba ganin tana nema ta fice daga hayyacinta ya sanyashi kamota hadi da zaunar da ita "lokacin daya kamota wani irin socking ne ya ziyarci zuciya dama gangar jikinsa nan take bugawar da zuciyarsa take ta qaru fiyye da kaida sai dai ya kasa magana a fili sai a zuci "ki natsu wallahi babu abinda zan miki ni kaina bansan meke damuna ba yau , tun da kika kasance tare dani naji komai nawa ya sauya . Yayi shiru tare da tsura mata ido ita kuwa banda bugawa babu abinda zuciyarta keyi, neman hanyar guduwa take daga garesa ."yayinda wasu irin hawayene masu azabar zafi suka taru a kurmin idanunta "wallahi ka cuceni tun da nake babu wani nmj daya ta'ba kai hannunsa jikina tun ina matsayin budurwa sai yau dana kasance mallakin wani tana gama fad ar haka ta fashe da wani irin kuka "okay ki zauna ki qarasa min aikina na sallameki and ki yafe min bisa kuskurena kafin ya gama mgnrsa har ta soma tattara kayan aikinta ta zuba cikin jaka ta fice da sauri ."da sauri ya fito ya biyota yana kiranta "ke!!! "ita kuwa da sauri sauri gudu gudu ta shiga lift ta danna grand segun ne ya fito da sauri sakamakon jin sautin muryar mai gidansa , cikin gigita segun yace sir meke faruwa ne ?"karka bari yarinyar nan ta wuce ka tsayar min daita !ka tsayarda ita segun amman ina cikin kankani lokaci maryama ta sauka kasa tana goge hawayen fuskarta cike da tashin hankali ta nufi inda motar yaya sadam yake a pake jikinta na wani irin kyarma ta bud'e ta shiga ta zauna kallo d'aya yayi mata ya fahimci tana tattare da damuwa nan da nan ya rud'e ya shiga jera mata tambayoyi "ka taimakeni yaya sadam ka bar garin nan dani akwai matsala "wacce irin matsala ?zan maka bayanin komai idan mun isa gida daga haka bai sake cewa komai ba yaja motarsa a guje suka fara qoqarin ficewa koda segun ya fito har motarsu ta fice daga ma'aikatan ." Wani irin gudu yaya sadam ke falfalawa akan titi yana cikin gudu ya hango wasu motoci gudu uku abayansu suna biye dashi idan ya rage gudu suma sai su rage gudu haka idan ya qara gudun motar zasu qara "maryama kamar ana binmu ki fad a min meke faruwa ? ta kasa magana kawai ta fashe masa da kuka dan bazata iya fad'a masa abinda mai kamfanin creation yayi mata ba ,ya zama abun kunya gareta ace ta fad'a masa wani kato ya ta'ba mata jiki ya zai dauketa ina yarda da yayi mata ?"kuka ta cigaba da yi shi kuma yana falfala gudu akan titi shi kansa kana kallonsa kasan a matukar tsorace yake sun yi tafiya mai dan nesa sannan suka nemi motocin uku dake biye dasu suka rasa sai daf daa zasu fita daga ogun state kawai sai ga motocin guda uku sun sha gabansu."cak yaya sadam yaja burki ya tsaya cikin tsananin fargaba wasu tika tikan murd'ad'd'un mutane suka shiga firfitowa daga cikin motar d'aya bayan d'aya har suka fito gaba d'ayansu sanye da kaki wanda ke nuna alamun sojojin nigeria ne wani irin matsanancin tsoro da firgici ne ya kama marayam tayi saurin riko hannun yaya sadam gam cikin nata jikinta na kyarma shima ya riketa gam bai yi tunanin ko yan fashi da makami bane sakamakon kakin dake sanye ajikinsu zuciyarsa tafi bashi wani abu dabam ,mutun uku daga cikin sojojin suka qaraso da sauri suka bugi kofar motar da karfi batare da 'bata lokaci ba kofar ta bude basu tsaya wata wata ba suka fito da yaya sadam tare da buga masa bakin bindiga nan take ya zube kasa . maryama ta saki qara mai sauti ta fito ta durkushe gabansa cike da matsanancin tsoro yaya sadam ya janyota zuwa jikinsa ai kuwa ta kamkamesa dan gabad'aya a tsorace take hawaye n ya soma bin kuncin maryama cikin sheshekar kuka maryama ta soma magana "bayin Allah laifin me mukayi maku ?dan Allah karku cutar da ni da mijina ,dan allah ku barmu mu wuce tunda nasan bamuyi maku laifin komai ba "ke ce bakiyi mana laifin komai ba amman shi wannan bakin munafikin yasan abinda yayi mana "inji cewar daya daga cikinsu da sauri maryama ta tsurawa yaya sadam idanunta tana kallonsa "wai kai dan rainin wayo ko ?mu zaka rainawa hankali ?".a d'an rud'e yaya sadam yace "Nifa duk ban fahimceku ba hasalima ban san laifin da nayi