Sashe 97
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
allah "to kisa aranki babu abinda zasu iya min ni ban ma yarda akwai wani dan Adam din da zai iya cutar da wani ba fashe da izinin allah ya qaras maganar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "tabbas nasan da haka amman dai fita hanyarsu "shiru yayi mata "kenan bazakayi abinda nace ba ?tayi maganar cikin zafin rai "wallahi da ana canza mutun adamcy da tunin na dade da canzaka kowa ya huta acikin danginka dan kwata kwata baka da kirki "ata dake zaune yayi shiru tare da cigaba da duban mami batare da yace mata komai ba dan ya ma rasa abinda zai ce mata ne yasashi yin shirun sai dai cikin zafin rai ya kamo lips dinsa na kasa ya soma cizawa da karfi "ina sake umartarka da ka sausauta komai idan ba haka ba zaka ruguza gida d'ayan da amafinka ya had'a " " kada kayi Kuskuren ruguza ahli dangin mahaifinka adamcy domin cikar muradinka idan ka aikata haka mahaifinka bazai ji dadi ba dan girman allah ka bar ruhinsa ya samu salama "ta qarasa maganar muryarta na rawa alamun tana son yin kuka "sweetheart zaki fara ko ?ya fad'a yana riko tafukan hannunta cikin nashi "kai din ne adamcy baka da kirki wallahi ban san wani irin zuciya gareka ba sam sam baka da tausayi "sweetheart ba haka bane kema kinsan adamcy dinki na iyakar kokarinsa akan ahlin mahaifinsa yana yin komai dan jin dadinsu ne ,babu abinda bana masu suna jin dadi ta koina tare da qoqarin sanyasu farinciki burina mu amafana da wannan kamafanin gabdayanmu nayi qarin kudi ne domin suji dadi ba dan mugunta ko dan jin dadina ba amman sweetheart ki duba kiga abinda baba qarami yayi ,wallahi banyi haka dan zalinci ko son rai ba kayanmu suna da ingancin da ko nawa muka saka farashinsu zaa siya idan baa siya ba wallahi tabbas zaa dawo daga baya saboda ingancinsu ."ya qarasa maganar zuciyarsa cike da rauni ." jikin mami yayi mugu mugun sanyi da gane da jin abinda ya fad'a ta matso sosai kusa dashi tare da d'aura hannuwanta duka ta riko fuskarsa dashi tana kallonsa wani irin matsanancin tausayi ne mai tattare da qaunar d'an nata taji ya sake nunkuwa acikin zuciyarta yayinda taji kuka from no where ya kufce mata, kawai ta rungumesa ajikinta tana wani irin kuka mai ban tausayi "wallahi nasani adamcy duk abinda zakayi akan agc babu mugunta acikinsa amman bana jin dadin furuncin babanka akanka haka zalika bana jin dadin yadda kake masa ko babu komai uba ne agareka kanin mahaifi ne albarkarsa albarka mahaifinka ne haka zalika tsinuwarsa tsinuwar mahaifinka ce ,ina neman alfarma agareka ,na rokeka dan allah kada ka sake fad'a masa bakar magna akan komai shi din ubanka ne halak malak duk duniya baka da kamrsa ka cigaba da hakuri da yanayinsa haka halinsa yake tmkr naka duk da dai yace bai san inda na samoka ba bayan ya manta cewar duk wannna halin naka shi ka d'auko amman in sha allahu zaka canza ,zaka canza da izinin Allah,allah yayi maka albarka ina maka addua allah ya baka abinda kake so duniya da lahira wannan yarinyar mafarkinka da kake so ina maka addua Allah yasa gaskiya ce. wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki mai wuyar misaltuwa wanda bai ta'ba jin irinsa ba babu alokaci d'aya zuciyarsa ta tsunduma cikin tunanin princess dinsa nan da nan kuma yarinyar data zanashi ta fad'o masa tun daga ranar farko daya soma ganinta har zuwa had'uwarsu a ogun, shiru yayi zaune tare da rungume hannuwansa duka a qirjinsa yana tunaninta, muryarta sak irin muryar yarinyar da yake mafarki, yaso kwarai yaga fuskarta a wancan ranar sai dai cewar ita din matar aure ce yasa ya hakura amman wasu wurare ajikinta duk irin na princess dinsa ne hatta yatsun hannunta irin na princess ne haka ma yatsun kafafunta kawai fuskarta ce ta rage masa ya gani ya tabbatar da ko ita ce. oh my godness god ! allah karka sa yarinyar nan tazo min amatsayin matar aure dan ban san yadda zanyi da rayuwata ba"kayi shiru ." bai motsa ba dan bai ji abinda ta fad'a ba "ka daina zurfafa tunani ni dai a kullum ina maka adduar idan mutunce kuma alkhairi ce arayuwarka Allah ya gaugauta had'aku idan ba gaskiya bace Allah ya kawar maka da tunaninta ka huta " Agogon tsarka hannuta daya zamo hannusa lokacin daya matso kusa daita yana shafa zanen lallen hannunta tayi baya da sauri sauran kadan ta kai kasa yayi sauri riko tsintsiyar hannuta sosai alokacin suke kallon juna ido cikin ido suke kallon cikin kwayar idanun juna nan ma sai da yayi kokarin bude nikaf din tayi saurin kawar da fuskarta ."ahankali ya mike tsaye ya shiga bedroom dinsa ya d'auko agogon tsarka ya fito ya tsaya yana qarewa agogon tsarkan kallo mai cike tsananin sheki yana jin kamar suna tare daita ne a lokacin a hankali ya shiga kai kawo acikin dakin yana cikin wannan halin mami ta mike ganin kamar ma ya manta da zamanta acikin parlour'n "Adamcy ta kira sunansa ya dan gigice ya waigo yana dubanta "meye damuwarka ?daga magana ka fita haiyacinka "ya girgiza mata kai alamun babu komai "ta sauke numfashi tace "ya babu komai daga magana ka shiga tunani daga tunani ka bazama ka d'auko agogo kana kallo agogon waye kamar na mata ?"bai ce mata uffan ba illa ya samu waje akan three siter ya kwanta tare da lumshe tsumammun idanunshi "ka fad'a min agogon wacece a hannunka ?kwanciya sosai yayi ya mike akan kujera batare daya bata amsar tambayar data masa ba ya damke agogon sosai ahankali ahankali ya qara runtse idanunshi yayi pretending like kamar yana jin bacci "adamcy me ya kawo agogon mace hannunka neman mata ka fara ko me ?" "sweetheart I'm feeling sleepy ""Feeling sleeping?"ta maimaita abinda ya fad'a "yes sweetheart bacci ".mami taja numfashi ta sauke ahankali sannan tace "alright !amman karkayi dogon bacci dan laasar ta kusa idanunta akanshi ta fice daga parlour'n sai dai zuciyarta cike take fal da mamaki da zarginsa ." ******** "Maryama taso kizo gareni maryama ta mike da kyar dan gbdy jikinta babu laka ta dawo kusa da granny wacce ta kawo masu ziyara a safiyar yau din ta zauna granny ta kamo hannunta daya ta rike gam cikin nata cike da matsanancin tashin hankali ta soma magana "wai meke faruwa da rayuwar yarinyar nan ne ?gabadaya na kasa fahimtar abinda ke faruwa daita duk lokacin da zaayi mgnr aureta ko tayi saurayi sai wani mummunar abu ya samesa? yanzu kuma gashi wanda ya aureta shima ya mutu ya barta , maryama tai saurin girgiza mata kai " granny bai mutu ya barni ba fa an dai binnesa amman nayi imani bai mutu ba zai dawo domin ina cikin son yaya sadam dan duk cikin wad'an da suka nemi aurena babu wanda zuciyata ta yarda ta kuma amince dashi kamar yaya sadam ni kaina na kan zauna nayiwa kaina wannan tunani granny "why abubuwa suke faruwa dani haka ? daga wannan sai wannan tayiwa kakar sadam tambayar tana sheshekar kuka ya allah laifin me nayi haka da wannan jarabawa tamin yawa ?yanzu ni nasan haka zan qare rayuwata matukar na rasa yaya sadam babu mai kuma Kuskuren sake zuwa neman aurena ". tayi shiru hawaye na zuba daga cikin idanunta "me yasa kuka min haka ? me yasa kuka nisanta da mijina wallahi zuciyata bazata iya d'aukar wannan tashin hankalin ba?me yasa ? Why why !!! ta qarasa mgnr tana wani irin kuka nan take suka rufa akanta har mahaifiyarta suna bata hakuri ". ahankali zuciyarta ta tsaidaita daga kukan da take tare da bata kwarin gwiwa "sadam dinki bai mutu ba sannan bai barki ba zai dawo gareki ki bawa zuciyarki kwarin gwiwa ki kwantar da hankalinki domin kwanciyar hankalinki shine kwanciyar hankalin duk wani masoyinki Kiyi masa addua da yarda allah zai dawo gareki ."tun lokacin da granny ta kirata zuwa gareta ya qaraso bakin kofar shigowa parlour'n da fuskarta ya sama cin qaro tana zubar da hawaye wanda ke fita daga kasan zuciyarta kamar ance ta d'aga idanunta dan daman tana fuskatar kofar shigowa ne idanunta ya sauka akanshi ."shiru tayi tana dubansa tana ganin tamkar a mafarki ne kallon juna suke ido cikin ido kafin a hankali ta motsa bakinta ahankali tace "kai ne a gidanmu sir !?bai ce komai ba haka zalika bai shigo ba ya cigaba da tsayuwa "maryama! umma ta kira sunanta ta sauke numfashi tana duban umma "Kina bukatar wani abu ne ?batace komai ba ta sake yunkurin maida idanunta inda ta gansa sai dai wayam tagani babu shi babu alamun sa byn kmr minti goma ta sake ganinsa wannan karon mikewa tayi da sauri ta nufi kofar d'akin wanda hakan ya maida hankalinsu gurin cike da tsananin tashin hankali aunty hassana da aunty suka biyo bayanata haka umma tayi kokarin danne damuwarta ta biyosu "sannu da zuwa oga ammar ka shigo daga ciki mana ." yayi shiru yana kallonta dan gabadaya bata haiyacinta yaso ya wuce a tun ganin farko da yayi mata amman ya kasa "waye shi maryama ?umma ta tmbyeta "shine wanda ya taimaka ya bani aikin dana barwa subaia a Z&A nan take murmushi ya dan bayyana akan fuskar umma "Ke ki rufewa mutane baki da shegen karyar tsiyar "wannna ai mai gidan sadam ne " umma ta dubi aunty hassana cike sa mamaki a ina tasan ogan sadam ?amman dai tayi mata alamun tai shiru sai dai aunty hasana taki shiru ta cigaba da zuba magana " mai gidansa ne dan haka naji anata fada ranar sadakar bakwai hatta kayayyakin daakaita amfani dashi shine ya kawo yanzu nasan da wani abun arzikin yazo ,fuskar maryama bayyane da murmushi tun bayan rashin sadam datai sai yau annuri ya bayyana akan fuskarta kuma tayi imani na ganin oga ammar ne dan bata ta'ba expecting zai zo gareta ba to me ma ya kawosa ?ta jefawa wankakki yar kwakwaluwarta kafin ahankali ta mayar da kanta Ta sunkuyar a kasa "yallabai amar sannu da zuwa dan allah ka shigo daga ciki bai dace ka tsaya a bakin kofa ba cewar umma da kyar ya ra'ba