Sashe 60
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ga Allah ne yasa kika aikata wannan kuskure kin hada aure dan kawo kwanciyar hankali a zuriarki gashi hakan bata kasance ba sai zallar damuwa a boye mami take goge hawayen dake bin kuncinta domin tana matukar tausayawa maryam da bata hada wannan auren ba maryam da bata kamu da son danta ba Ahankali maryam ta shanye kukanta sakamakon tunowa datayi akan cinyar mami take da goge hawayen idanunta ta mike zaune ta riko hannunta cikin nata dan girman allah mami karki masa magana zan miki list din komai ki aiko min dashi kina ganin rayuwarki haka shine mafuta ?to ya zanyi mami bani da zabin da wuce zamana acikin gidan nan kina son na kashe auren nan maryam ? Mmn sudai MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Dan allah Ina son masu karatu su san wani abu ,bana son yanke wani abu daya danganci abinda yake cikin labarin nan domin duk abinda aka rubuta akanshi yana da matukar amfani ga makaramci kuma kowani bangaren yana buqatar a ta'ba shi domin idan an zo hukunci ,s ina son masu karatu su bani hadin kai domin samun damar cigaba da rubutu kamar yadda aka bani a kasin haka kuwa babu abinda zai haifar sai zuwa hutun rubutu ko kuma abun ya koma sai randa naji nishadi nayi typing kuma kad'an domin ina iyakar qoqarina na ganin na kawo maku komai daki daki kamar yadda yake aciki amman kamar ku bakwa gani ko kuma nace kamr kunfini hanzarin son ya had'u da mafarkinsa ko kuma son a gama rubuta labarin nan to wallahi na fiku son naga na kammala na huta shiyasa tun farko nace arewabooks zan kai wasu daga cikinku suka nemi alfarma na kawo what'sapp sannnan sunji kuma sun amince ko sau d'aya ne na dinga basu a wata amman adalci nawa yasa nake baku kullum dan abini a sannu dan nesa tazo kusa Page 18 Kan maryam yayi wani irin mugun sarawa da karfin gaske sakamakon jin abinda ya fito daga bakin mami ,yayinda qirjinta ya dinga bugawa fiye da kaida kina son na kashe auren nan maryam ? kwakwaluwarta ta sake maimaita mata kalmar da take daf da tarwatsa rayuwarta ahankali ta zame ta zauna a qasa cikin tsananin tahain hankali mara misaltuwa tayi shiru tana jin yadda magnr mami ke yawo acikin kwakwaluwarta da zuciyarta, haka ne ma yasa jikinta ya kama rawa gashi mami taki d'auke kwayar idanunta akanta tana jiran taji abinda zata ce akan hukuncinta . gano yanayin cewar maryam ta shiga cikin tsananin damuwa yasa mami kiran sunanta .." maryam.. "ta d'ago kanta da kyar ta zubawa mami idanunta da suka sauya kala tsabar tashin hankalin data tsinci kanta "kinji abinda na fad'a kuwa ? maryam ta lumshe mata ido kawai dan bazata iya magana ba a halin da take ciki wanda take jin yafi duk wani tashin hankali har ma da qiyayyar yaya Adam gareta ."ki bud'e baki kiyi min magana domin kawo qarshen wannan matsalar ,nice da kaina na had'a auren nan naku ,idan kina ganin bazaki iya cigaba da zama dashi ba wallahi a bud e take bazan cigaba da takura miki ba ko kuma na ji haushinki dan kinyi min qoqari fiyye da tunanina ,dan zama da adamcy sai mai katoton hakuri zai iya, dashi kuma daman yana cikin dalilin da yasa zuciyata ta tsallake kowa acikin yan uwansa da yan uwana ta za'beki amatsayin matarsa ,amman yanzu ni kaina na gaji kuma nasan kema kin gaji maryam hakuri kawai kikeyi Ruwan hawaye ya cika idanun maryam me yasa mami zatayi wannan tunanin ?ita dake cikin taskon wahala ba tace ta gaji ba me yasa ita zata gaji har da yunkurin rabata da muradin zuciyarta ?ta yiwa kanta tambayar tana qoqarin danne kukanta idan dai har kina ganin babu damuwa maryam zan rabaku kuma a yau domin bazan juri ganinki cikin wannan tashin hankali ba. kije ki auri wanda zai soki ya kula da rayuwarki shi kuma ya cigaba da zama haka tunda rayuwar daya za ba wa kansa kenan ."zuciyarta maryam kamar zata tarwatse tsabar tashin hankalin data sake tsinci kanta ciki tayi shiru tana kallon mami tana assessing maganarta fuskarta d'auke da tarin damuwa tana lissafa idan ace wani ne ya fad'a mata haka da ita kad'ai tasan irin matakin da zata d'auka akanshi ,amman mami ce babu abinda zata iya "zazzafan numfashi kawai ta sauke tare da dukar da kanta qasa jikinta na wani irin karkarwa tana son boyewa mami damuwarta ." mami ta kai hannu ta d ago ha'barta tasanya kwayar idanunta cikin nata ido cikin ido suke kallon juna ruwan hawaye ne taf acikin idanunta "kinyi shiru maryam banason shirin nan naki ,banason kiji aranki kamar nice silar shiga damuwarki domin ni karon kaina ina jin haka araina cewar duk nice silar shigarki cikin wannan tashin hankalin ,kina zaman zamanki lafiya tare da masoyanki masu sonki da qaunarki na shigo miki da abinda ya zame miki damuwa ,banason ganin tashin hankali shiyasa nake neman izininki ."wannan buqata ta mami ba abu bane mai sauki ko yuwuwa agareta "idan zaki d'auki sharawata maryam ki rabu da adamcy ki huta nima zuciyata ta huta "anya zan iya kuwa mami ?na rabu dashi wanda rabuwa dashi din yana nufin har abada bayan a yanzu ne ma nake jin bazan iya daidai da kwana d'aya batare dana yi masa magana ko sanya shi acikin kwayar idanuna . Maryam mami tafiki gaskiya rabuwa da yaya Adam shine mafuta agareki amman kuma tashin hankali ne mai tsanani ga rayuwarki wanda baki san ranar fita acikinsa ba .ta sake d'agowa taga har lokacin ita mami take kallo tana nazarinta "ki rabu dashi maryam !mami ta sake bata umarni a karo na biyu "amman mami kina ganin rabuwar mu itace qarshen komai "?tayi maganar muryarta da jikinta na rawa "zaman da kuke a tskaninku maryam bashi da wani amfani a yanzu ni kaina ina nadama had'a wannan auren, na d'auka komai zai samu sauyi a samu cigaba ashe damuwa akan damuwa kawai za'a haifar. murmushin 'bacin rai ya bayyana akan fuskar maryam kana ta girgiza kanta "please maryam Kiyi tunani mai kyau kamar yadda nayi bana son ki bata shekaru cikin wannan halin, still dai shiru maryam tayi wanda hakan yake nuna alamun shawarar mami bata mata dadi ba maryam ba kya tausayawa kanki ?ki tausayawa kanki maryam nasan kina yin komai saboda ni ne na kuma gode da biyayyarki gareni allah yayi miki albarka ." Zuciyar maryam wani irin zafi take mata da tuttukin bakinciki tana jin wata irin tsantsar soyayyarsa na sake ratsata baza ta'ba kuskuren rabuwa da yaya Adam tayiwa kanta wanan alqawarin suna tare mutuwa ce kawai zata rabusu ,koma yayi qoqarin rabuwa daita baza barshi ba tagumi ta zuba cikin zullumi da rashin sanin madafa dan bazata iya aikata abinda mami take buqata ba ,duk magiyar da mami take mata amman maryam taki bud'e baki tace zata rabu da ATA." sosai mami ta fahimci soyayyar ada mcy din ce mai tsanani ta hana maryam bin umarninta jikin maryam a matuqar sanyaye ta mike batare data kalli fuskar mami ba tace "mami dan allah ki bar maganar rabuwar nan haka ,ni abinda nafi buqata daga gareki shine addua ko kad'an yaya Adam ya soni acikin zuciyarsa tana gama fad'ar tace "bari naje na kawo miki abun sha har tayi taku biyu ta taya "dan allah mami karki masa magana akaina tana gama fad'ar haka ta cigaba da d'aga qafafuwanta ." Mami tabi bayanta da kallo duk ta zube ,duwawukan nan nata duk sun kusan qarewa, ramar da tayi tasa ta qara kankacewa ,ta fito daga kitchen rike da cup da jug ,kawai taga mutun tsaye kikam tamkar wani jami'in tsaro cikin wani had'ad'den suit ash colour haka ma takalman dake sanye a qafafuwansa ash ne sai sheki suke ,tsintsiyar hannunsa makale da agogon rolex ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa ga sihirtaccen kamshin turarensa mai tsananin kamshi ,nan da nan kamshi parlour'n ya canza zuwa na kamshinsa ."suka tsurawa juna ido shi yana kallonta cike da tsantsar tsana yayinda ita Ke kallonsa cike da tsantsar qauna satinta uku kenan bata sanya shi acikin kwayar idanunta ba bata san tayi kewar ganin kyakkyawar fuskarsa ba sai a yanzu da take kallonsa tsaye agabanta ,kullum kamar qara masa kyau ake sam bazaka ce 40 garesa ba ,ga kamshin daddan turarensa duk inda ya shiga sai anji wannan mayataccen kamshin nashi mai tsayawa arai da dagula lissafi,taji kamar tayi wulli da cup din hannunta taje ta rungume shi ajikinta taji d'umin jikinsa ." Qaramin tsaki yaja ganin yadda take kallonsa kamar bata ta ba ganinsa ba arayuwarsa baya son yawon kallo ya d'auke kwayar idanunshi ya qarasa shigowa sosai ya zauna kusa da mami ya baje akan kujera yana furta "wash allah nah na gaji yayinda maryam ta qaraso tayi masa sannu da zuwa aciki ya amsa mata shima ganin mami zaune ne ,a natse maryam fara hidima da mami "sweetheart a she dana biya ta gida bazan sameki ba ?"tace uhm bazaka sameni ba amman nasan ko kwanaki nawa kayi zaka zo ka sameni zaman jiranka kallonta kawai yayi ya d'an ciza lip's dinsa yana d'aure fuskasa dan ya fahimci kamar akwai wata a qasa . mami ta kalli maryam dake zaune kusa daita taga ta girgiza mata kai alamun karta masa maganarta take ta fahimci abinda take nufi numfashi ta sauke inda ATA ya fara jan mami da hira maryam ta tashi ta dawo gabansa ta tsugunna yayi saurin janye qafafuwansa tmkr yaga mugun abu numfashi ta sauke ta sake matsowa ta kai hannuwanta ta janyo qafafunsa saurin runtse idanu yayi yana jin kamar da wuta ta ta ba shi . Ahankali yaji ta soma kwance igiyan takalminsa d aya kamar ya zare qafarsa ya buga mata takalmin a fuska amman ya share sakamakon darajan mami dake gurin ,tana gama cire masa takalman ya janye