← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 105

Sashe 87

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

d'aga kafafunsa zuwa Kan gado ya fad'a ya kwanta flat ransa duk babu dadi yayinda idanunshi na kallon saman d'akin babu abinda yake gani sai kwayar idanun maryama da yatsun hannun ta da sautin zazzakar muryarta mami tazo ta zauna kusa dashi tana daura hannunta saman kansa tana masa sannu "bayan mintuna shabiyar sai ga doctor ya shigo tare da sallama tashi yayi ya zauna ya jingina bayansa da abun gado yana sauke numfashi da kyar tare da yiwa doctor bayanin yadda yake ji batare da 'bata lokaci ba doctor ya fara masa gwaje gwaje bayan doctor ya gama yayi masa allura sannan yace "ranka ya dade jininka ne ya hau kad'an yana da kyau ka dinga saukakawa kanka wasu abubuwa dan zuciyarka na bukatar hud'u yanzu dai nayi maka allurar bacci in sha allahu kana tashi zakaji daidai Allah ya baka lafiya ya ajiye masa magunguna yace zai wuce ."mami tayi masa godiya adaidai lokacin da doctor ke had'a kayansa yayi mata sallama ya wuce ." "Ka tashi kayi sallah magriba kafin bacci ya d'aukeka sannan me za'a kawo maka coffe ko tea "any one sweetheart." ya furta tare da mikewa da kyar ya shiga bathroom ita kuma mami ta fita kawo masa coffe dan tasan shi yafi bukata wanka ya fara sannan yayi alwala ya fito ya cire kayan jikinsa ya canza zuwa jallabiya brown colour mai ratsin baki ya isa inda abun sallarsa yake ya gabatar da sallah bayan ya idar ya koma Kan gado ya kwanta lamo tare da janyo bargo ya rufe jikinsa koda mami ta dawo d'akin ATA na bacci ta zauna gefensa tare da zuba masa idanunta tana jin wani irin qaunar d'anta na ratsata bata iya dogon fushi dashi hakazalika bata son ta rasa shi. hawaye ne ya fara bin kuncinta ji take a duniya data rasashi gara ta rasa komai dan idan ta rasashi ta ina zata cigaba da rayuwa?" ina bazata iya ba bazata iya jurar rasashi ba gara ita ta bar duniyar tun kafin taga mutuwarsa ahankali ta mike tana goge hawayen idanunta ta qarasa ta rage masa karfin ac sannan ta canza masa wutar d'akin zuwa mara haske ta duka daidai fuskarsa tayi masa addua sannan ta fita daga d'akin ." Washgari tun da yayi sallah ya koma bacci har karfe goma bai tashi ba yana kwnace yana sharar bacci shigowar mami yafi sau uku dubashi yana bacci sai dai ta kalli fuskarsa ta fita sai wajen shadaya da wasu mintuna ya tashi hanyar bathroom ya nufa ya fad'a yayi wanka ya fito yana goge sansar jikinsa ya sanya kananan kaya masu matukar kyau he look very attractive kullum ka kallesa qara kyau yake ya d'auki kwalbar turare yana feshe jikinsa yana fesa turare kwakwaluwarsa na tunanin maryama da sauri ya ajiye kwalban turaren hannunsa ya qarasa inda ya ajiye kayansa na jiya daya cire ya dauki dogon wondonsa ya shiga laluba wondon cikin kankanin lokaci ya ciro agogon sarkarta .yayi shiru yana kallon agogon yana ganin tsinysiyar hannunta aciki "mai yasa zuciyata ta damu akanki ? zuciyarsa tace "kasani ko ubangiji ne ya turo maka ita cikin rayuwarka da wata manufa a boye kayi duk yadda zakayi tayi aiki akarkashinka sosai ya dinga jin damuwa akan abinda yayi mata abu ne da bai tabayi ba .wai ya kai hanunsa jikin wata mace da sunan ta burgeshi ya dauki kusan mintuna goma yana kallon agogon tsarkar sannan ya bud'e durowarsa ya jefa ciki ya fito yana taku . " cike da isa yake taka step, tun daga kan step yake jiyo sautin muryar baba qarami yana tafiya da kyar har ya sauko kasa ya tarar da mami zaune a inda ta saba zaman a parlour'n gabanta kuma baba qarami ne zaune yana magana cikin tsananin fushi tunda yayi masa kallo d'aya ya dauke kanshi bai sake kallon inda suke ba ya wuce dining ya dibi abinci da kanshi ya a zauna akan kujerar dake kallon step bayansa kawai zasu iya hangowa haka zalika duk abinda suke fad'a yana jinsu bayan ya gama cin abinci ya d'aga kanshi yana kallon agogon dake manne a parlour'n dake walwalin haske karfe 12:00 na safe ne yanzu mikewa yayi ya qarasa gurin mami yace "sweetheart ni zan fita mami tace "kai da baka da lafiya ina kuma zaka ka dinga hutawa dan Allah ?" numfashi kawai ya sauke batare da yace komai ba "ka zauna akwai maganar da babanka yazo dashi shiru yayi yaki zama "banason musu kayi abinda nace "a natse ya samu waje ta zauna still bai kalli inda baba qarami yake ba bare ya gaishesa "magana ce yazo daita akan hindu me kasani akai ?zuciyar ata a dake ya fad'a mata komai game da abinda ta aikata ." baba qarami ya kalli ata yana jin haushi irin haushin da mutun zai iya kashe mutun "na dauka ko wani ka ga yayiwa hindu haka sai inda karfinka ya qare kuma zaka taimaki rayuwarta amman wulakanci ka bar min 'ya a tsare har tsawon watani sannan aka wuce daita gidan yari bancin na tashi tsaye da haka rayuwarta zata qare . tsakanina da kai adamu allah Ya isa ban yafe maka ba duniya da lahira "kayi hakuri baba qarami duk abun bai kai haka ba zai sa a sakota in sha allahu "wani irin kallo ata yayiwa mami ta juyo ta kallesa a tsanake tace "me yasa kayi haka adamcy ?dokarki nabi kikace a dauki mataki akan duk wanda yayi yunkurin kashe miki maryam ko ba haka ba ?mami tayi shiru tana dubansa sam bashi da tsoro akan komai "naji amman kasa a sakota bana jin ma itace zata aikata haka "kiyi hakuri sweetheart babu ta yadda zaayi na saka baki saboda abinda ta aikata mummunar laifi ne kuma ta amsa da bakinta ta aikata "a gidan ubanka ta amsa haka ?" "mugun kawai mai mugun hali ni nasan hindu bazata aikata hakan ba sai dai idan azabtar daita akayi yasa ta amsa laifin da ba nata ba gefen bakinsa ya ciza da karfi "nifa duk abinda zaa fad'a akaina ba damuwata bace idan kuna da hujjar da zata wanke kanta tayi ,ku kuma ku sake shigar da qara kotu amman ni Adam bazan saka baki a fito da tantiriya yar tasha irinta ba." tayi laifi kuma ta amsa laifinta dole hukuma ta hukuntata ni na gama magana sweetheart ko zan iya tashi ?"daga baba qarami har mami suka zuba masa ido suna kallonsa ranshi fess ya mike yayiwa mami sallama ya wuce yana fita ya iske masu tsaronsa a inda suka saba tsayawa suna ganinsa suka qaraso da sauri cike da girmamawa suna gaishesa atakaice ya dinga amsa masu batare da bata lokaci ba aka bude masa bayan mota ya shiga suka bar gidan a can parlour'n mami kuwa hakuri kawai take bawa baba qarami tana tabbatar masa lallai hindu zata fito ya bar komai a hannunta da kyar ta samu ya wuce sai dai kallo daya zaka masa kasan ransa a bace yake kuma zai iya aikata komai akan adam ." ***** Bangaren maryama kuwa har karfe goma na dare babu su babu labarinsu, aunty da umma da habib da sauran yanuwan ummah wadan da suka zo biki da dangin mahaifinsu da basu wuce gida ba duk suka damu sukai ta neman layinsu amman shiru ga dai wayoyinsu yana ringin amman ba d'agawa nan fa hankalinsu ya tashi matuka zuciyarsu ta far tsinkewa gabad'aya suka taru acikin parlour'n umma cikin jimami da tashin hankali ."Allah sarki umma duk yadda take jin mummunar faduwar gaba da tsinkewar zuciya amman sai ta dake ta kasa nunawa kowa damuwarta da yanayin da take ji sai ma ta dinga kwantar masu da hankali tana cewa "babu komai wata killa yanayin aikin ne ko kuma ababen hawa n sukai yawa a hanya "haka suka kwana zaune cikin tashin hankali da zullumi ." washegari kuwa tun da asuba fari habib da a bokinsa faisal suka d'auki hanyar ogun state kasamcewar duk inda maryama zata aiki tana tura masa address gabad'aya habib baya cikin natsuwarsa ji yake kamar zuciyarsa zata buga hakan ne ma yasa sam baya ganin gudun da motar tasu take akan titi har ma yaji kamar su fita su canza wata motar kamar bazasu kai ba sai gashi sun karaso jikinsa na tsuma kamar wanda ake zubawa ruwan zafi suka dauki hanyar ma'aikatan isarsu ke da wuya aka sheida masu sunzo amamn tun a yammacin jiya suka wuce cikin tsananin tashin hankali habib ya shiga kiran number aunty kira d'aya ta dauka tana kiran sunansa nan dai habib ya sheida mata komai tunda aunty ta kira sunan habib idanun ummah ke kanta tana jiran ta gama wayar taji mai zata fad'a ganin yadda ta fashe da kuka tana salati yasa ummah ta dawo kusa daita jikinta na wani irin rawa "balkisu meke faruwa mutuwa sukai ko me ? "Cikin muryar kuka aunty tace "ummah wai tun da yammacin jiya suka baro kamfanin salati ta saka tana addua tare da karfafa zuciyarta data aunty "karki damu balkisu babu abinda zai samesu koma menene in sha allahu Allah zai kawo masu mafuta ta fad'a tana share hawaye "gsky ummah ina ji ajikina akwai wani abu dake faruwa dasu." numfashi ummah ta sauke cikin karfafa ma aunty zuciya "haba bilkisu ki daina wannan tunani kisa aranki babu abinda zai samesu "Allah yasa amman tun jiya da yammaci suka baro kamfani amman har zuwa wannan lokacin babu su babu alamunsu "ke dai kiyi masu addua kawai ta fad'a cike da tausayawa kanta dan ita kanta tana ji ajikinta akwai wani abu dake faruwa dasu sai dai tana fatan ya zama alkhairi arayuwarsu gabad'aya."ta mike ta shiga dakinta ta zauna cikin tsananin tashin hankali hawaye ne ya dinga zuba daga idanunta ahankali idanunta ya sauka akan frem din hoton sadam dake ajiye akan qaramar durowarta yana sanye da kananan kaya ya daura rigar sanyi akan kayan idanunshi manne da bakin glass ,tayi shiru kawai tana kallonsa kallonsa take saboda shi kadai ne ya rage mata a duniya bata da uwa bata da uba bata da miji yanzu idan wani abu ya samesa dole zata shiga damuwa ta qarasa zancen zuci tana fashewa da kuka mai ban tausayi "in
Chapter 87 · 0% Book details