← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 105

Sashe 10

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

babu abinda take wasu siraren hawaye suka gangaro mata ta fara sheshekan kuka tana jin motsin fitowarsa tayi saurin danne kukanta tana share hawayenta ." Numfashi ta dinga saukewa sama sama ya dawo gabanta ya tsaya daga shi sai 3 qauter dake jikinsa duk wani zati dake jikinsa mai daukar hankali ajikinsa ya bayyana wani tsoro ne qarara ya bayyana akan fuskarta dama zuciyarta gbdy wanda yasata saurin runtse idanunta gam ji tayi ya kwanta jikinta har tana jin saukar numfashinsa ya kai hannuwansa ya d'an matsar daita "ki koma wajen baccinki sannan kukan me Kike yi wa mutane ?" "Ba kuka nake yi ba " ta fad'a muryarta na rawa "uhm shi wannna kuma ya sunansa?ya fad'a yana kwanciya "qoqari tayita ta danne kuka ya fuskanceta sosai "alokacin da numfashinta Ke sama da kasa ya kai hannu daidai qirjinta inda ya suka sauka akan dukiyar fulaninta wani abu yaji alokaci daya yadda numfashinta Ke sauka da kuma tsarga wa wani abu da yaji mai kama da shoucking " "Kina jina zuciyarki tayi nauyi sosai da alamun akwai abinda Ke damunta "ta lumshe idanunta tana sauke numfashi kuma har lokacin bai dauke hannusa ba "na rashin son hisham ne ?ta girgiza masa kai alamun a'a "to na meye to?bana komai bane "okay yanzu ki bude baki kiyi kuka mai sauti domin ki rage nauyin da zuciyarki tayi aiko kamar jira take ta bude zatayi kuka dan har sautin muryarta ya soma fitowa taga ya zaro ido tare da bude bakinsa ba zato ba tsanani yaji saukar laulausan lip's dinta akan na nashi .." "Tsura mata ido yayi batare daya sake cewa komai ba illa kwayar idanunshi daya zuba mata yana jin wani irin sauyi ajikinsa tmkr wanda ake jona masa wutar lantarki cikin lokaci kankani komai ya birkice masa bai san yadda akayi ba ya had'eta da jikinsa still bakinsu na manne cikin juna , sai fidda numfashi nana hauwa'u take cikin jin wata irin kunya sam bada wata manufa tayi hakan ba gudun abinda zai fad'a ne dan yanayin yadda ya zaro ido babu sauki zai iya yin komai ." Da ba dan period din da nana hauwa'u take ba da babu abinda zai hana hisham saninta ya mace a daidai wannan lokacin wannan shine abinda ya hana komai faruwa amman murza kam ta sha gbdy ya manta wata kiyayya jin dadinsa kawai yake da jikinta ita kuwa babu abinda Ke fitowa daga cikin kwayar idanunta sai ruwan hawaye tare da mugun tsoronsa tana son hanashi abinda yake tare da sheida masa bafa ita bace zabinsa amman tsoronsa ya hanata ." "Yau ne kawai shima nice na jawo ta fadawa zuciyarta hakan, in sha allahu hakan bazai sake kasancewa ba ,ita dai bata jin wanzuwar tsanarsa ko kiyayyarsa acikin zuciyarta idan ya shirya yin rayuwar aure daita zata bashi dukkanin farinciki idan kuma zai cigaba da nuna tsanarta ne zata janye jikinta sosai hisham yazo hannu gashi babu damar aiwatar da komai lumshe idanunshi yayi tare da komawa gefe ya kwanta yana mayar da numfashi bai san meke damunsa adaidai lokacin ba domin kuwa idan yace yasani yayi karya ." Bayan ta juya masa tana rufe rabin jikinta ya dan waiga ya kalli bayanta wanda hakan yasa shi jin wani irin ajikinsa gabansa ya dinga tashi tsurawa bayanta ido yayi shape dinta mai matukar kyau da d'aukar hankali,duk da yasan jikinsa na da taushi amman sai yaji nata kamar yafi nashi soft kai everything ko dan bambamci halitta ne jikin ,nuzla ya tuno wanda yasa tunaninsa ya koma kanta itama fa masha allah tana da sura mai kyau da taushi uwa uba kuruciya dan nana hauwa ta girmeta da kusan shekaru hudu zuwa biyar ya dauki kusan mintuna talatin a haka bai motsa daga inda yake ba yana kuma jiyo saukar numfashinta ,numfashi ya sauke ya canza hasken d'akin zuwa mara nauyi sannan ya zame ya kwanta ya d'an janyo gefen bargon data rufa dashi ya rufe jikinsa ." Washegari hisham ya bude ido bai ga nana hauwa'u ba ya kunna wutan dakin tare da kai idanunshi ya sauke akan agogon dake ajiye akan table it was 9:44tsaki yaja tsaki sannan ya mike ya shiga bathroom ,bathtube ya shiga yayi wanka ya fito black boxcer da black singlet ya saka sannan ya daura kaya akai ya fito fuskarsa a hade ya gaishe da abbansa dake zaune rike da jarida sannan ya shiga dakin mumy domin ya gaisheta ko kallonsa batayi ba bare ta amsa sallamarsa, ahankali ya qaraso har inda take zaune juyar da kanta gefe tayi alamun bata son ganinsa "momy Kiyi hakuri nana hauwa'u ma da kike fushi akanta bata damu ba ." maganarsa ta sake bata haushi "mumy ina magana "a shake ta juyo ta kalleshi "maganarka bata da wani amfani agareni fitar min a daki kar na qara ganin ka shigo min daki sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba korosa tayi daga dakinta ." ya fito sami abban yana masa complain shima da farko abban bude masa wuta yayi amman ganin yana bashi hak'uri da janyo masa ayoyi akan masu hakuri da yafiya ya hakura shima ya daura da yi masa nasihohi yana janyo masa ayoyi da hadisai akan irin tanadin da Allah yayiwa masu hakuri da biyayya ga iyaye ." bayan ya gama ya riko hannunsa zuwa dakin da mumy take ya mata nasiha sosai akan hakuri da yaya nan mumy tace "naji na hakura amman ka fad'a masa kar na sake ji ko ganin yaje wajen nuzla idan ba haka ba zaka sha mamakina zaka haddasa gabar da baa san ranar qaresa ba akan nana hauwa'u kuwa zan iya tsine maka "hisham ya dan saci kallon mahaifiyarsa Kmr zai mata kuka "wai momy me yasa yanzu kike yin haka ne ?."abinda bakya yi da "yanzu ka canza shiyasa nima na canza idan ka s abinda nike son zaka cigaba da ganina a yadda kasani sabanin haka kuwa matsaloli zamuyita samu da kai sha sha mara hankali "Ke dai kiyi hakuri ki bar mgnrsa da nuzla raayinsa ne idan yana sonta ya qara daita tunda allah ya halasta masa ajiye mata sama da daya "a ina ?ba dai wannan yarinyar ba sai dai wata dabam kai watan ma ba dai ina raye ba mu iyayensa mu ishesa misali tunda muka haifesa ya taso mu biyu kawai ya gani ya koyi example daga garemu ". Abba yayi murmushi yana cewa "wannan raayinmu ne ta yuwu shi kuma bashi da wannan raayin "mumy zatayi mgn abba yayi saurin dakatar daita ta hanyar cewa "abar maganar haka yanzu dai ki sanya masa albarka tare da kyakkywar addu'a da kuma fatan alkhairi acikin rayuwarsa " mumy ta numfasa kana tayi Kmr yadda abba ya umarceta ,hisham sam bai ji dadin kalaman mumy ba ya tashi ya fito ransa a bace ya shiga d'akin baccinsa ." Nana hauwa'u na gyaran daki taji an shigo ta dan juyo ahankali domin ganin wanda ya shigo , yaya hisham ta gani a tsaye fuskarsa babu alamun fara'a ya sha kunu tamkar bai tab'a dariya ba,tana kallonsa ya qarasa inda durowar mirrow yake yana dube dube ta bar abinda take ta qaraso ina yake ta tsaya gabanta na wani irin bugawa da karfin gaske "me kake nema ?shiru yayi har sai data sake maimaitawa, fuskasa a hade yace "ai Kinsan abinda nake nema ki dauko ki bani "babu musu ta nufi inda ta ajiye wayoyinsa guda biyu da wallet dinsa daman da zata goge saman durowar ne ta canza masu wajen ajiya ta dawo ta mika masa tana cewa "fatan ka tashi lfy?bai amsa ba ya fice daga cikin dakin yana jan tsaki tabi bayansa da kallo ." lumshe idanunta tayi tana jin damuwa cike da sanyin jiki ta gama abinda take ta fito yana zaune a falo ."Kusa dashi taje ta zauna tana wasa da yatsun hannunta "abinci fa yayi ready ? a qalla ya kusa minti goma sannna yace "bana da raayin ci "tayi shiru ta rasa me zata sake cewa" oh allah ban ta'ba tunanin zan yi irin wannan rayuwar ba ,sai yanzu take ganin gskyr maryam akan yayanta aure ba abu ne da zaka iya sadaukar da rayuwarka akanshi ba domin abune da mutuwa ce kawai take rabawa tashi yayi ya nufi wata kujerar yana dane dane a wayarsa ." daren ranar da kuma wunin safiyar data waye duk a cikin k'unci nana hauwa'u tayisa har izuwa yanzu cin abinci kawai ke fito da'ita shima bisa takurawar mumy ce ."dan kar mumy tazo ta tarar daita a d'aki tana kuka bayi take shiga taci kuka har ta godewa ubangiji, idanuwanta sunyi jajir kamar barkono, da dare ma da mumy tazo zata d'auketa domin kaita gidanta sai da mumy tayita rarrashinta dan ji take gara ta cigaba da zama dasu akan zamanta da yaya hisham mumy ta fito tana bata kwarin gwiwa sai da abba ya sake masu wasu nasihohi masu ratsa zuciya da kuma gangar jiki sannan yaya hisham ya d'aukesu suka wuce direban mumy na biye dasu abaya domin shi zai dawo daita ." Har suka isa gidan nasiha mumy take masu shi dai yaya hishsm bashi da wani kuzari saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa amsarta dan bai jin zai iya mata irin son da yake wa nuzla yayinda nana hauwa'u itama jin momy kawai take amman har a zuciyarta tasan yaya hisham bazai bari su zauna lafiya ba sai 9 na dare sannan direba ya dawo da momy ta barosu su kad'ai acikin makeken gidansu. d'akin take kallo a tsanake komai yayi mata kyau most especially parlour'n wanda aka qawata shi da kayan zamani masu kyau". Karfe tara da minti shabiyar daidai wayarsa ta soma ringing ya d'auka ya duba, ita kuwa tunda wayar ta fara ringing ta tattara gabad'aya hankalinta kacokan akanshi , bata san dalili ba taji wata irin muguwar faduwar gaba ,ta dan saci kallon inda yake a zaune a tun sanda suka shigo ,bata dauke kwayar idanunta akanshi ba har sanda ya dauka yana cewa "wallahi nuzla rigimarki tayi yawa dare fa yayi okay shikenan ganin nan zuwa yana gama wayar ya fice batare da yace mata komai ba ." wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sauke tana dafe
Chapter 10 · 0% Book details