Sashe 2
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tashi matuka ,wai shi sai ya kai ni wajen mai gidansa wallahi aunty yau Allah ne kawai ya taimakeni da sai dai wata bani ba ,wama ya sani ko masu satar mutane ko masu shan jini haka kawai yaje ya saceni su zuke min jini ." ."aunty tayi murmushi tace "masu satar mutane da shan jini ne zaa basu office acikin babbar maikata haka? wata killa dai maigidansa mai kama dake yake mafarki kawai shine kuka yi aran gama dashi Ke kuma kika tsorata" maryama tayi murmushi wallahi nayi matukar tsorata dan bazan qara zuwa aiki wannan maakatan ba "baki da zabi princess dole idan an sake buqatarki kije ke dai kawai ki dinga addua kafin ki bar gidan nan "wallahi aunty ina yi ban ta'ba barin gidan nan batare da nayi addua ba ." "To shikenan Allah ya qara tsarewa yanzu dai karki saka damuwar wannan abun a ranki har kizo ki rame dan yanzu ma duk kin canza kin rame ba kamar kwanakin baya ba dama ya lafiyar kura" murmushi maryama tayi" allah aunty ba wani rama da nayi ina after dad ? na fita da safe bangansa ba gashi na dawo ma banji motsinsa ba da alamun ya baya gida ?"bai jima da fita ba "bana son ina gida baya nan duk sai gidan yayi min wani iri gida ya dawo kamar gidan mutuwa"ni kuma nafi son shi haka bakina ya huta kwakwaluwata ta huta dan duk abinda akayi akan idonsa bai masa ba sai ya tanka shiyasa idan ya fita sai naji kwanciyar hankali haka sukai ta hira har Maryama ta wastsake daga damuwar da take ciki ." Shi kuwa bangaren m.malik cikin dauki ya shiga neman layin mai gidansa, daman abinda yasa tun farko bai nemesa ba so yayi yayi masa suprice sai dai kawai ya gansa daita ,duk da ya rasata yau amman sai da yayi dariyar farinciki , lallai mai gidansa dan bawa ne shi da mahaukaci ma ya daukeshi a she dai mafarkinsa zai zama gaskiya ko babu komai a yanzu sun tabbatar ita din gsky ce kuma dole su basu nemanta "ahankali ya zauna akan daya daga cikin kujerun office din hankalinsa yaji ya dan fara tashi sakamakon abinda computer sadawar ke fad'a masa number a kashe take ." cigaba yayi da kiran numbobinsa sai dai amsa daya ake bashi wayar is switch off "oh my goodness wai me yasa ya kashe wayoyinsa?wani yaronsa ya kira ya budesa yana fitowa direbansa ya taso cike da girmamawa yana qoqarin ya bude masa mazauninsa ya mika masa hannu alamun ya bashi keyn motarsa "yalla'bai ka bari na kai mana "ya fadi haka ne saboda ganin yanayin da yake ciki kai kawai ya gyada masa ya shiga gidan baya direba yaja suka wuce "ina muka nufa yalla'bai?" "Babana esatate zaka kai ni direba ya d'auki hanya, duk bayn second sai ya kira layin a kashe a karshe dai ya yanke shawarar turawa ATA sako kamar haka "Slm sir Please call me sir I have gist for you." tafiya kadan sukayi suka kawo bakin tafkeken get din gidansa ,sai dai kash basu samesa ba dan tun daga bakin get aka sheida masu baya nan "shiru yayi yana tunanin jiya ne fa aka d'aura masa aure kuma ya kamata ace ya tare da amaryarsa "kenan baa nan ya tare da matarsa ba ?yayi wa kanshi tmbyr ." Ko da yake mutun mai tarin arziki haka ai yana da gida bilaadadin duk kusan yasan rabin gidajensa sai dai bai san wanda zai nufa ba ahalin yanzu dole yana bukatar yayi waya dashi kafin ya nufi kowanne daga ciki ,cike da tashin hankali ya bawa direbansa umarnin su wuce zuwa apapa gra yasan dai dole mahaifiyarsa ko cikin yan'uwansa zasu san inda yake tafiya kad'an sukayi suka hadu da wani matsiyacin go slow tsaki m.malik yaja yana dafe kanshi." Bangaren ata kuwa yana can kwance shame shame ya sha whiskey Kmr yadda ya saba yayi mankas yana ta sharar bacci a kasan d'akinsa wannan dalilin n yasa m malik yaji gabadaya wayoyinsa akashe dan sai daya kashe wayoyinsa sannan yayi mankas,hakan bai sa m malik ya hakura ba duk wucewar mintuna sai ya kiran layin mai gidansa amsar daya ake bashi ,ganin har zuwa wannan lokacin bai samesa ba yasa yayi qoqarin kira salim ko suna tare dashi shi kuma kiran na shiga baya dauka haka zalika number hisham ." Wanda a wannan lokacin m.b ,salim ,yaya Ibrahim amar kai har ma da hisham suna tsaye akan ATA cikin tsananin damuwa ,hisham ya fito da wayarsa ya duba number m. malik ya gani bai dauka ba dan nan take ya fahimci magana yake son yi da ATA ya sake kallonsa yadda ATA din Ke kwance wani iri tamkar mara rai ya maida wayarsa cikin aljihu gabdayansu zukatansu cike yake da tashin hankali halin da yake ciki tunanin kawai hisham yake me zai faru idan mami tasan halin da yake ciki dan shi bai san iya kwanakin daya dauka yana shan giya ba sai yau da mb ya kira salim suna tare salim din ne ma ya takura masa yazo ." wayarsa ta sake ringin ya fito dashi ya duba still m malik ne dan haka ya sakata a silet ya sake maidata aljihunsa "ku kama min shi mu daurashi akan bed inji cewar mb daya kai hannunsa jikinsa yana zubar da hawaye "he don't want to loose him at all ,shi bai san ma soayyar mafarkinsa ya kai haka ba wallahi duk tunaninsa da zarar an daura aurensa shikenan komai ya zama tarihi agaresa a she komai zai yi worst ne atare dashi wani irin tausayin abokinsa ne ya lullesa ". "Me Ke damun tunanin adam ne ?he's so much in love with his dream ,what will happen idan bai sameta ba? "zan iya mutuwa for real." salim yaji sautin muryarsa cikin maye yana bashi amsa da haka "farincikina na ganta I just love her with all my heart "gbdy suka suke numfashi suka daurashi akan katifa ya kwanta sharaf yana sauke wani wahallalen numfashi "yanzu me zamuyi mu raba rayuwarsa da wannan damuwar ?" yaya Ibrahim ya fad'a "yana dubansu." Amar ya numfasa yace "ni dai idan son samu ne a rabashi da auren nan na maryam yaji da matsala daya "idan kuma ita yarinyar mafarkinsa ba gsky bace fa ?inji cewar hisham, kawai mu tayashi da addua, yanzu bari mu sheidawa mami halin da'ake ciki saboda idan ya farka karta bari wani ya shigo inda yake ko shi ya fita zuwa koina a tsareshi zuwa na wani lokaci adai samu wanda zai zauan tare dashi da zai dinga kula dashi kamar zai fi "mb ya fad'a yana dauke hawayensa ni bansan wake zuwa siyo masa giya ba dan dai da kanshi bazai iya zuwa ba wallahi muddin naga mai siyo masa giya sai naci uban kowa waye ya qarasa mgnr yana naushin iska ." "kun fa san halinsa, kunsan halin taurin kanshi babu wanda zai hanashi abinda ya ga dama inji cewar hisham "duk da haka dai a samu mutun biyu zuwa uku su tsaya tare dashi wannna karon bai isa ba matsawar bazai daina shan giya ba ya zama dole mu dauki mataki akanshi haba nifa na fara tunanin aljana ce yarinyar mafarkinsa duk suka zuba masa ido " to idan ba haka ba kamar adam me zai tsaya batawa kanshi lokaci akan wani mafarki diya ko ta uban waye ai zai samu, kawai aljanna da yake gani nata salon kenan ,amamn da yarda allah qarshenta yazo sai muyi 'bata 'bata daita da ayoyin Allah yanzu dai bari na kira mami "inji cewar yaya Ibrahim ." Mami kam dake cikin mutanen da suka zo mata biki suna ta'ba hira acikin damuwa take dan duk wanda ya kalleta yaga yadda take abubuwanta yasan tana cikin damuwa mai tsanani sam sam ma babu kuzari ajikinta kawai she's thinking of abubuwa daywa abu biyu yafi damunta rayuwar adamcy bata san yadda zatayi dashi ba, ga kuma ta uwar maryam da kawayenta suna buqatar amarya ta tare a gidanta kafin su wuce ga ango baya cikin natsuwar da zasu tare,yanzun ma da take zaune addua take allah ya saukowa danta tilo da kwanciyar hanakali da natsuwar zuciya." tana cikin wannan halin wayarta ya fara ringim ta dauka ta duba "sunan yaya Ibrahim ta gani yana yawo akan screen din wayarta da sauri ta dauka cikin tsananin damuwa tace "Ibrahim yaakayi .? "mami adam ne yake cikin wani .."bai kai ga karasawa ba ta katse masa hanzari ta hanyar mikeww tsaye ta nufi kofar fitowa daga dakin dan ba wayr da zata iya amsawa bane a wajen da take ta koma d'akinta tun da taji ya ambaci sunan adam ta fara karanto duk wata addua data iya a can bangarensu kuwa wayar yaya Ibrahim tana loudspeaker har sanda mami tace "yauwa Ibrahim ina jinka yanzu me ya faru da adam din ."? "Mami da akwai matsala "mb ne yazo ya iske shi cikin wani yanani adam yana son kashe kanshi saboda wani banzar mafarkinsa I think ya kamata mu dauki mataki akan wannna matsalar nifa nama fi tunanin mafarkinsa jinu ne ya dace mu sa ayi masa rukiya ya fad'a mata, tashin hankali mami ya qaru ." Muryarta na rawa ta soma furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ."kardai giya ya sake sha ?numfashi ya sauke kana yace "eh mami daman kinsan ya fara sha ne ." Kuka ta fashe dashi tana cewa "shekaranjiya nan ya fara sha ban san me adamcy yake son maida kanshi ba ace mutun bazaiyi tawakali da hukuncin allah ba"mami ki kwantar da hankali in sha allahu komai yazo karshe da ikon allah zamu yaki koma menene da karfin addau ,nifa bansan abun nasa ya kai haka ba sai yau din nan "ya kai Ibrahim na shiga uku ni zulai wani irin jarabawa ne wannan ?"ta fad'a tana sake fashewa da kuka saboda tashin hankali." " yanzu dai mun d'auke shi daga inda yake kwance a kasa mun maidashi kan bed kizo muna son mu wuce muje muyi sallah amaman bama son abarshi shi kadai zamu barshi da salim da amar sai ke idan ya tashi ya ganki a kusa dashi ya fad'a