Sashe 70
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aga mata hankali ya zame hannunsa ya mike ya qarasa qarahen dakin ya tsaya rike da kugunsa yana jin zafi da ciwon abinda mahaifiyarsa da yan'uwansa suka masa "."Adamcy na !ta sake kiran sunansa a karo na biyu yana jinta yaki juyawa mami ta cigaba da magana "ka sake min wani alfarma a karo na biyu adamcy . ya d an juyo a natse ya kalleta "kayi hakuri ka janye sakin da kawa maryam ka maidashi d aya sannan ka maida maryam d akinta saboda allah da girman mahaifinka da darajan haihuwarka da nayi "ya bud'e baki yi zai magana "karka ce aa adamcy ta katse shi ta hanyar fad ar haka kayi dan allah da mahaifinka da kuma ni da nayi silar zuwanka duniya domin muddin ka rabu da maryam zata shiga damuwa mai tattare da tashin hankali idan ta kasance cikin damuwa nima zan shiga domin nice silar komai . ya juyo sosai ya fuskanci mami "abu na farko tana rayuwarta batare da kai ba na shigo daita cikin rayuwarka, abu na biyu yanzu kun zama abu daya wayasani ma ko rabo ya shiga tsakaninku "gaksy ni sweetheart bana son abinda kike min akan yarinyar nan ban gama fita cikin matsala ba zaki sake shigo min da wata damuwa "ba zancen shigo da damuwa bane adamcy naji hakan ajikina akwai rabo a tsakaninka da maryam . yayi shiru kawai yana mamakinta a ransa yace ai kuwa badani ba dan bazan sake gigin kusantarta ba kuma ni bana jin haka ajikina domin spam din daya fitar ba d a bane dan duk spam din da zai zama d a fitarsa nada matuqar wahala daga jikin d an adam mami ta d'an yi gyaran murya "ni mahaifiyarka ce zan iya sakaka kayi min abu dole koda kuwa ranka bai so amman a wannan karon banason na maka dole alfarma nake sake neman da baka hakuri saboda dalilai masu yawa dan allah ka janye ka kuma maida maryam iska ya fesar mai zafi daga bakinsa sannan yace "shikenan naji na janye na maida ita ."iyakar abinda ya fad'a kenan ya fice daga dakin domin idan ya cigaba da tsayuwa zata nemawar yanuwnasa afuwa abinda bazai so ba kenan shi dasu har abada . Alhamdulillah! mami ta dinga furtawa tana nemammansa afuwa da sauki a wajen Allah suna zaune jugun jugun ya sauko ya nufi kofa "zabiba ta zabura ta mike zata bishi aunty shahida ta dakatar daita tana cewa "da alamun kin fara manta waye adam arayuwarki wallahi zamanki matar aure da ya ya bazai hanashi yi miki mugun bugu ba mu barshi har ya sauko da kanshi "ni dai zan wuce gida dan bazan bari wannan fuskar ta sake shigowa muyi ido hudu ba inji aunty khadija gabdaya suka kwashe da dariya ban da maryam wacce idanunta sukayi jajur tsabar kuka nima tashi zanyi na wuce nasan mami zata shawo kansa suna shirin mikewa mami ta sauko "mami ni zan wuce gida inji cewar aunty khadija itama zabiba ta gyara zaman mayafinta nima zan gudu dan yau sai wani ikon allah ,allah yasa dai ya sauko "kun gama hadasa mana tashin hankali shine zaku gudu daya bayan daya ?"dan allah mami Kiyi hakuri bamu san zai dawo ba tunainmu fitarsa yayi nisa "ai shikenan tunda ya janye sakin ."" Wani irin ihu nana hauwa ta saka tare da zuwa inda maryam take ta rungumeta "sister yaya ya maidake ai na fad'a miki yanzu kin zama wani bangare na rayuwarsa "kunga kuzo ku wuce sai qarshen wata kenan "in sha allahu mami suka hada baki gabdayansu sukai mata sallama gidan ya saura daga mami sai maryam nasiha da kwnatar da hankali mami tayi tawa maryam muryata a dashe tace mami na gode har karfe goma suna zaune a parlour'n sallah ne kawai Ke tashinsu amman babu ATA babu alamunsa har shabiyu ta buga suka rufe kofar parlour'n batare da sun murd a key ba koda zai shigo suka hau sama daga maryam har mami babu wanda ya runtsa sai faman juyi suke bayan sunyi sallar asuba ne suka kwanta inda wani naunayen bacci ya d aukesu sai karfe shadaya suka tashi da sanyi jiki maryam ta sauko domin samawar mami abinda zata ci kawai ta gansa kwance akan kujera ya daura tafin hannunsa d aya a daidai mararsa yayinda d ayan hannunsa ke saman goshinsa idonsa biyu sai dai tunaninsa yayi nisa domin likitansa bai dade da wucewa ba abinda sakamakonsa ya nuna ne yake yawo acikin brain dinsa wai anyi masa amafani da wasu kwayoyin jima i ne wanda shine ya haddasa masa azababben ciwon kai da bai jin magani how come ?ya tambayi kanshi Idanunta na kanshi ta shige kitchen ta fara aikinta . Kwana bakwai kenan da ATA ya maida maryam sai dai bbu wani saukin al'amura dan babu abinda ya canja daga yanayin zamansu duk da mami dake tsakaninsu dan bai kallon duk inda mrym take idan yana gida hatta mami baya wani hira daita harkar gabansa kawai yake .addu'a dai mami take qara yi kan Allah ya canza masa rayuwa ya kuma daidaita tsakaninsu yasa zaman lfy ya shigo cikin rayuwar aurensu .yau tunda safe maryam ta tashi da aikace aikace gyaran cikin gidan, aiki kawai take kmr wacce tasha kwaya domin koina yayi kura dan ta kwana biyu bata kakkabe gidan ba tun kafin zuwan mami duk mami na zaune tana kallonta shirun da mami tayi ne yasata kallon inda mami take mami tace anya kuwa mrym bazaa kawo miki masu aiki ba dan naga aiki yayi miki yawa kuma ko babu komai zasu dinga d auke miki kewa idan na wuce .?tayi murmushi kawai batare da tace komai ba ki bar aikin nan haka mrym ki huta gobe zansa a kawo miki masu aiki sai suyi ,yanzu zanyiwa cristi magana tasa akawo mutun biyu nasan sun isheki ? Maryam ta girgiza kai alamun a ! mami karki wani damu da masu aiki dan ni bana ra ayi masu aikin. bbu abinda na fi tsana a rayuwata sama dasu dan wallahi wasu masu aikin ba aiki yake kawo su ba , mami tayi murmushi dan ko bata fad a mata ba ta fahimceta to ai shikennan Allah ya bada sa'a Amman dai yanzu ki bari ki dan hutu haka. naga ko karyawa bakiyi ba ,ai yanzu nan zankarasa nama kusan gamawa.mamaki ya cika zuciyar mami ganin irin aikin da take wanda bata yinsa a lokacin da take gidanta komai masu aiki suke yi mami ta gyara zamanta tare da kunna TV tana kallo daga nan inda take zaune suke hira da mrym din ,kafin wani lokaci mrym ta gama komai har abinci . koda yamma tayi ma zagaye mami tayi ta shiga kitchen ta shirya masu lafiyayen abinci , farar shikafa ce da miyar pepesoup din kayan ciki ,sannan da miyar pepesoup din freshe fish dataji kayan hadi da ganye ugu aciki sai kamshin ke tashi . sannan taje ta shirya komai tsaf tsaf a dinning ta bude kulolin abinci ta dinga d aukar girkin hotuna da vedio byn ta gama ta rufe komai taje ta sheka wanka ta hade cikin daguwar rigar atamfa wacce ta sha stone work sai kalli take zubawa ga wani kamshi na musamman dake tashi ajikinta. karku manta mrym akwai son kwalliya da posting a social media tana gama kwaliyar ta fara zubawa kanta hotuna kala dabam dabam kamar yadda ta yiwa girkin sai datayi posting sannan ta soma qoqarin fitowa ahankali take saukowa zuwa parlour kasa tayi maseefar kyau sai kyali take abu ga farar mace kusa da mami ta samu guri ta zauna sai dai idanunta na kallon tsaitin kofar shigowa mami ta kalleta tana murmushi tace kai Kai maryam kinyi kyau ,yau adamcy bazai ganeki ba mrym ta saki wani murmushin jin dadi tana cewa kai mami har wani kyau nayi . ? wallahi kinyi kyau sosai kuma naji dadin ganin wannan kwaliyar daman inata son nayi miki magana akan kin rage kwalliya ba kamr sanda kike gida ba, marym ta sake yin murmushi gsky kinyi fine sosai allah yasa adamcy yaga kyan kwaliyar nan Ameen ta amsa a cikin ranta . bayan kamar mintuna goma suka jiyo sallamarshi a ciki suka amsa alokacin da yake taku cikin parlour, kunnenshi makale da waya yana magana da saurinta ta mike ta tarbeshi zata karba briefcase din hannunsa ya hanata batare da ya kalleta ba ya nufi hanyar sama yana jan tsaki dan baqaramin jin haushin nacinta yake ba jiki a sanyaye maryam ta shige kitchen ta zauna tana runtse idanunta yayinda zuciyarta ke mata wani irin zugi mami sarai ta fahimci damuwace tasa yin haka nan da nan itama taji damuwa zuciyarta ta sosu ta mike ta shiga kitchen din ta iske mrym zaune har lokacin idanunta a runtse suke ta kai hannunta ta riko hannunta ba tace daita komai ba suka fito kai tsaye dining area suka nufa ta zaunar daita itama ta zauna tana ta ba qirjinta alamun ta kwantar da hankalinta . byn kmr minti talatin ATA ya sauko jikinsa sanye da riga white t shirt da wando jeans three quater sai kamshin turarensa Red ne yake tashi ajikinsa , kai tsaye dinning area ya nufa inda ya hangi su mami zaune da alamun zaman jiran fitowarsa suke .'ahankali ya karaso gurin tare da samu guri ya zauna kusa da mami yana gaisheta ai na d auka bazaka gaisheni bane ?dan ka wani shigo ko kallon inda mutane suke bakayi ba ta fad a cikin rashin sakin fuskar numfashi ya sauke yace barka da dare sweetheart ?barka ya aikin ?alhamdulilllahi ya fad a atakaice sannan ya ciro wayarsa yana operating . ahankali mami tayi wa mrym alamar ta koma kusa dashi ta tashi ta koma kusa dashi ji yayi kamar ya tashi ya canza guri amman ya share ya cigaba da dandana wayarsa maryam bismillah kiyi serving dinmu wani irin mikewa tayi wanda yasa gabadaya santsar jikinta girgiza most especial qirjinta d agowa yayi da niyar sauke mata ruwan bala'i idanunshi yaci karo da girjinta kallo daya yayiwa Rabin nonuwanta ta saman rigarta ya d auke idanunshi amman duk da haka say da yanayinsa ya d an canza nan da nan kwalkwaluwarsa ta shiga circulating