← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 105

Sashe 88

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sha allahu bazan rasaku ba sadam da maryama ina maku fatan alkhairi a duk inda kuke Allah ya dawo mun daku cikin koshin lafiya ." suna nan zaune cikin tsananin jimami da tashin hankali har yamma sai ga habib da abokinsa ajigace suka karaso gida sakamakon yanayin damuwar da suke ciki cikin tashin hankali aka kira baba gali da sauran yan'uwan dangin mahaifinsu cikin kankani lokacin suka hallara dan daman suna bangaren aunty hassana .bayan sun gama jin komai suka fara zuba ruwan maseefa hajiya fatima tace "ai duk abinda ya faru laifin umman sadam ne dan itace ta basu gudunmuwa tafiya , inda take shiga batan take fita ba nan da nan sauran yan'uwa suka kama ita dai ummah shiru tayi kawai tana karanto duk adduar datazo bakinta ita yanzu batasu take ba yadda ya'yanta zasu dawo gareta take ."yadda suka wuni jiya cikin tashin hankali haka suka wuni yau din ma dan har karfe 12:00 na dare ba labarinsu ummah tace kowa yaje ya kwanta aga zuwa gobe ."washgari baba gali da habib da sauran yanuwa maza suka bazama nemansu har ogun state din aka sake komawa sai dai babu wani labari duk hankulansu a tashe yake aunty kuka kawai take ummah kam tayi dauriya habib ma kuka yake yana kiran sunan maryama da yaya sadam abun gwanin ban tausayi ." bangaren aunty salma kam abun yayi mata dadi fiyye da tunanin mai karatu ,dan adduar mutuwa ma ta dinga masu ,allah yasa mummunar hatsari suka samu a hanya "burinta daman maryama ta bar duniya ko kuma tayi rayuwar kaskanci ko zama babu aure. sai gashi burinta ya cika batare da ta 'bata kudinta ba ,tana zaune baba gali ya shigo ya tsaya akanta "salma ina fatan dai babu hannunki cikin rasa sadam da maryama ?wani irin kallo ta watsa masa "idan da hannuna me zai faru ?Aa to gsky ni dai babu ruwana kuma muddin da hannunki Kiyi maza kisa a dawo dasu "gsky a wasu lokutan sai naga kamar kana bin bayana amman kuma wani lokacin sai naga kana nuna min wariyar launi ,kai yanzu meye damuwarka dan an nemesu an rasa kai daya kamata kaji dadi kayi farinciki an nemesu an rasa maryama bazata yi rayuwar jin dadi a gidan ba zata bar ya'yanmu suyi rayuwarsu cikin jin dadi ko da yake shi kanshi yusif din yanzu mun rasa gane kanshi ko shekaranjiya da suka zo daurin aure da abbansa bai leko inda muke ba da alamun aikin daakayi masa ya fara barin jikinsa sai an sabanta wani sabo "ni yanzu ba wannan bane damuwata ki fad'a min gsky da hannunki a rashin dawowar su gida ko babu hannunki ciki ?"ta sosa idanunta da hannunwanta duka tace "babu hanuna !"to amman ai shekarajiya naji kina waya da malaminki kina cewa ayi duk yadda zaayi a salwantar da .."kaga dakata daka ji ina magana cewa nayi a salwantar dasu duka ko maryama ?to ai ni ko maryama ma bana son ta rasa rayuwarta bare kuma sadam "tsaki taja tana turo masa baki "ai daidai ne ma idan sadam ya mutu idan bakasani ba bari na fahimtar da kai, idan sadam ya mutu kai ne zakaji dadin rayuwarka dan duk wani abu daya mallaka zai zama naka halak malak kai da sauran yanuwanka hassalima naka ne zai fi na kowa yawa tunda bashi da magaji ,mahaifiyarsa ce kawai ita kadai ranta kuma bazata gajesa ba "kinji zaki sake lalata komai ni dai bana son ran kowa ya salwanta a hannuna ".yana gama fad'ar hk ya fice tabi shi da kallon kaskanci tana ta'be baki "ina ganin shima wannan sokon sai nasa an gama min dashi gabad'aya na huta tai murmushi "wallahi ina farinciki da rashin dawowarsu allah yasa ko gawar su kar agani ." Maryama kam cikin wani jahili gida su jojo suka nufa daita a sume can wajen gari a tsakanin lagos to ile ife , gida ne na sirri wanda ba kowa yasan dashi ba gida ne da mai gidan ya gidana domin taronsa na sirri ko kuma duk sanda zai holewarsa ko kuma wani meeting sannan yana ajiye mahimman abubuwansa agidan ,gida ne mai hawa daya kuma agyare yake babu abinda babu acikinsa najin dadin rayuwa gida ne wanda babu wanda zai san an shigar da mutun sai su da kansu idan sunyi raayin asani ." a babban parlour'n sukai masauki tare da wanda ya basu aiki shima kuma ba gidansa bane gidan abokinsa ne ya amshi key a hannunsa kai tsaye ya nufi bedroom suka biyosa da maryama kan wani makeken bed din dake dakin ya nuna masu suka shimfideta "aikin ku yayi kyau sosai fa .gabad'aya suka kwashe da dariya shikenan an kashe boss kowa ya huta sosai kuwa suka amsa masa atare tsaye yayi yana kallonta yana sauke numfashi yana lashe lip's dinsa "kusan wani abu ?gabadaya suka girgiza masa kai "da alamun yarinyar nan ta shiga comer?nima abinda na fahimta kenan "idan dare yayi ku dawo ku dauketa ku bar nan daita domin bata da wani sauran amfani agareni , ku dauketa ku kaita duk hospital din da kuka ci karo dashi amatsayinku na sojoji bazaayi wani bincike akanku ba, kuce kun tsinceta ne a hanya cikin wannan yanayin ."an gama!" zuwa gobe zakuji alert dina "okay babu matsala ." Da misalin karfe goma ba daren ranar mutun biyu acikinsu suka fitar da maryama wacce bata san halin da'ake ciki ba suka nufi wani hospital daita yadda akace suyi haka sukai suka ajiyeta da wayarta da jakarta suka qara haba taimakon gaugauwa aka fara bata sai dai har zuwa washegari bata farfado ba har sanda aka kira number number wayarta suka dauka tare da sheidawa wanda ya kira halin da'ake ciki ." Kallo daya zaka yiwa su ummah ka tabbatar da cewa baa cikin nutsuwa walwala da kwanciyar hankali suke ba, tunda suka duro hospital bayan wayar sukai da ma'aikatan hospital din ,daman kuma tun ranar farko da tafiyarsu sadam din basu sake samun isashen bacci da nutsuwa ba har sai da suka daura kwayar idanunsu akan maryama "me ya sameta haka da har ta fice hayyacinta bata gane kowa?,me ya kawota asibiti "ina sadam da suka ganta ita kadai kwance rai hannun allah? kamar kar su zo ta fara sambatu tana kuka tana kiran sunan yaya sadam tana fad'ar irin abinda akayi masa aunty Kuka ta fashe dashi cikin tsananin tashin hankali tana bubbu qasa tana fad'in "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "dan allah karku kashesa dan Allah ku fito min dashi daga cikin rami ,su waye suka sakaku wannan aikin ku fad'amin wanda ya sakaku zan mika masu rayuwata dan bana son na rasa yaya sadam .wannan mummunar kissar dani yafi dacewa bada bawan Allah kamar shi ba dan Allah ku fito min dashi "tana ihun fad'ar haka sai taji anfasa wani razanannen kuka akanta mai kukan tana fad'ar "lahaula wala kuwwata " me ya samu sadam shikenan kin kaishi an kashe mana shi"inji cewar aunty hassana ummah kam kalmar innalillahi wanna ilaihi raji'un kawai take furtawa "wannan yarinya me yayi miki da zaki sakamasa da wanna muguwar sakayya."? farkawa maryama tayi ta ganta akan gadon hospital cikin yan'uwanta dana ummah ,ummah ta riko hannunta cikin nata tana mata sannu aunty kam kuka kawai take tana furta adduaoi, cikin haka doctor ya shigo ya sallamesu gabdaya domin duba jikin maryama sai bayan daya fita suka dawo dakin suka cigaba da zage zage har sai da ummah ta dinga taka masu burki , duk wanda zai yi magana sai ummah ta hana tare da cewa yaje waje maryama na bukatar hutu a qarshe dai daya bayan daya suka fice sai daga baya suka dawo har dare babu wanda ya sake cewa komai sai da irin kallon da suke binta dashi babu sausauci ."maryama dake kwance cikin tsananin tashin hankali ta zuba ma ummah dake zaune a gefenta ido tana dubanta ,itama umma ita din take kallo duk ta fita haiyacinta yadda idanunta suka kunbura sukai wani irin girma sun bata tsoro matuka yayinda gabad'aya fuskarta tayi jajur saboda kuka ahankali ummah ke mata nasiha tana tofa mata addua wani irin yanayi maryama ta shiga alokacin da idanunta da kwakwaluwarta suke sake hasko mata komai daya faru ." a natse ta dinga bin kowa dake gurin da ido sai dai taga wani irin mugun kallo suke mata zuwa can taji aunty hasana na cewa "ji yadda take bin mutane da kallo wannan yarinyar fa muguwar munafuka ce dan allah tashi ki fad'awa mutane inda kika kai mana d'anmu daga rakiya ai wallahi baki isa ba sai kin fito mana dashi dan shi kadai muke kallo a matsayin mahaifinsa ."mikewa maryama tayi jikinta a sanyaye har ga allah tafisu bukatar yaya sadam arayuwarta sannan yadda suke nuna mata baya mata dadi duk da tasan basa qaunarta amman batayi tunanin zasu zargeta ba kanta ta daura akan cinyar ummah tasa kuka tare da jin wani kullin abu ya tsaya mata yaki gaba yaki baya "ummah ce ta dinga rarrashinta tana yiwa aunty Hasana fad'a "wallahi ummah bansan mutane nan ba bazan iya cutar da mijina kuma danuwana ba wallahi ina son yaya sadam ." "nasani maryama bazaki ta'ba iya aikata hk ba cikin jin dadin kalaman ummah maryama tasa kuka tana cewa "ku taimakeni ku nemo min yaya sadam domin ban san inda zan saka rayuwata ba tana kuka ummah na share mata hawaye duk da itama hawayen take sosai hankalin mutane ya tashi kowa kuka yake a wajen ". "ummah Kiyi hakuri ki yafe min nayi nadamar fita wannan aiki ban san me ya jani na aikata haka ba kuma wallahi na daina farinciki da iya wannan aiki da nayi arayuwata ummah kuzo muje inda aka binne yaya sadam da ransa zaa iya samunsa a raye ina ji ajikina bai mutu ba hawaye umma ta share amman maryama kwanaki biyar kenan da faruwar wannan alamarin kina ganin zai rayu "?numfashi ta furza mai zafi "ummah !"sai kuma tayi shiru tana wani irin kuka tana tuna kalamansa na qarshe gareta "abinda nake so dake maryama ki natsu sosai kiyi abinda ya kawoki ina sonki ina kuma alfahari dake na kuma yarda dake a duk inda zaki kasance nasan zaki kame min
Chapter 88 · 0% Book details