← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 105

Sashe 20

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 7 Ahankali motocinsa suka fice daga cikin abdullahi estate ,mr ATA zaune a bayan mota yayi shiru yana sake tariyo tautaunawarsu da ammar shi dai baya jin zai auri mai kamanceceniya da harafin sunan maryam ma bare mai sunanta, sai kace babu mata a duniya masu sunan arziki sai nata , tabbas shi yasan dan dole ya qara aure kuma acikin tsakankanin wannan lolacin amman kuma ba mai irin sunan yarinyar ba . wani dogon tsaki yaja sanda ya tuna dole zai koma ya kwana gida d aya da yarinyar da yafi tsana . Qarfe goma daidai suka qaraso bakin get din gidansa wanda sai alokacin ya tuna daya sallami masu tsaron get din gidan, hakan yasa ya lalubo wayarsa ya kirasu su dawo bakin aiki kuma alokacin wanda zuwa wannan lokacin motocinsa sun kutsa zuwa cikin haraban gidan kai tsaye parking space suka nufa . sukai parking suka firfito da sauri ata na qoqarin bud e murfin kofar motar mutun d aya acikinsu ya bud e masa cike da girmamawa . cike da natsuwa ya fito daga cikin motar ya tsaya yana magana can kasan makoshi gobe da wuri zan bar gida ya fad a atakaice okay sir duk suka had a baki gurin fad ar haka, daga haka bai sake cewa komai ba ya soma takawa . maryam dake zaune tana cin abinci tana kallon series na turanci my husband my destiny ,title din series din ne ya d auki hankalinta har ma yasa ta cigaba da kallo, ahankali taji ana qoqarin bud e kofar parlour n,zumbur ta mike tsaye tabar cin abinci da kallon da take sbd jin motsin shigowarsa . tsumammun idanunshi ya zuba mata masu matukar firgitarwa cikin salo na harara , gabad aya maryam ta gigice da sauri ta d auki remut din tv ta rage volume ,shi kuwa wani kallon tsana ya cigaba da binta dashi tun daga sama har kasa tabbas zaton shi ya tabba manu direban mami ita zai kawowa abinci . yadda yake kallonta yayi mugun d aga mata hankali dan bata san abinda zai biyo baya ba , jikinta ya saki sosai yayinda qirjinta ke wani irin bugawa da karfin gaske a sanda ya qara taku biyu ya qaraso tsakiyar parlour n ya tsaya still kwayar idanunshi yana yawo ajikinta . tsoro da matsanancin firgici ne duka suka kamata alokaci d aya zuciyarta ta cigaba da bugawa da karfin gaske,yayinda gefe gudu kuma sanyayyen kamshin turarensa ke neman buwayar hancinta ,nan da nan hankalinta ya sake tashi jikinta ya kama rawa rawa wayyo allah nah me yasa na zauna a parlour n ban koma d akina naci abinci ba gashi zan jawa kaina maseefa da tashin hankali? ta fad a tana dungurin kanta . da kyar ta sanyawa jikinta jarumta tace san ..sannu da zuwa .ya jita sarai amman yayi tamkar bai ji ba . a kallon da yake mata yana iya ganin yadda qirjinta ke bugawa da sauri wanda hakan ke tabbatar masa da tsananin tsoronsa da take ji ne ,wannan ne kawai abinda yake d an so daga gareta bayan shi babu komai ,ta koina bai ga ta yadda zai sota ba bare har suyi rayuwar aure daita . tsaki yaja tare da d auke kanshi yana cewa minti d aya!minti d aya kawai na baki ki tattara ki bar nan kuma daga yau karki sake na shigo parlour n nan na d aura kwayar idanuna akanki dan bana son ganinki me nace ?ya tmbyeta yana watsa mata harara kar na sake ka shigo parlour n nan ka d aura kwayar idanunka akaina dan baka son ganina ta fad a idanunta na cikowa da ruwa hawayen tausayin kanta good idan kuma kin isa ki fad a ki janyo wa kanki massefa dan wallahi matsawar sweetheart ta sake zuwa gidan nan da wata matsala na rantse da girman allah sai na kawo karshen auren nan bayan na gana miki azaba mai rad .ya fad a cikin zafin rai. bazan .. ! shut up nonsense girl kawai bar nan yanzu kafin na sauya miki kamani guntuwa kawai mara fasali ina magana kina magana sa anki ne ?. da sauri ta d auki basket din da babbar kula da qarami yake ciki ta nufi hanyar kitchen ,ajiyar zuciya ta sauke bayan ta shiga kitchen din tasa hannu ta share hawayenta wani irin mutun n shi da bai da imani haka ? sam sam zuciyarsa bata gajiya da fad ar bakaken maganganu , gabad aya ko cikaken minti biyar bai yi da shigowa gidan ba har ya hargitsa mata lissafi . Oh ni maryam ta yaya zan iya shawo Kan mutumin nan bare na samu kulawar sa ?ya Allah kasan yadda ka jarabeni da soyayyarsa ya allah shima ka jarabesa da soyayyata ko dan yaji yadda nake ji akanshi ta fad a a fili tana neman inda zata juye abinci zaman uban me kike yi aciki ? ammmm uhmm gani nan fitowa ,ta samu wani kwanon silver ta juye abincin haka ma stew din ta bud e fridge ta saka bata tsaya wanke kulalin ba ta fito da sauri ta d auki plet din abinci data fara ci tayi d akinta tana sauke numfashi . a natse ya haura sama ya shiga d akinshi bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwa ya jima ruwa na sauka akanshi sannan ya fito yazo ya sauya kaya marasa nauyi ya dawo parlour n kasa ya zauna tare da d aukar remut ya canza channel zuwa na labarai yana cewa useless girl kawai babu abinda tasani sani sai kallon abinda bazata samu ba . bayan kamar minti goma yaji cikinsa ya fara masa zafi alamun yana bukatar ya saka masa wani abu . Wayarsa ya d auka ya kira d aya daga cikin masu tsaronsa a gaugauce sale adamu ya qaraso bakin kofar shigowa ya tsaya yana neman izini shigowa may i coming sir coming! ya fad a batare da ya kalli kofar ba sale adamu ya shigo bakinsa d auke da sallama kasancewarsa muslim ne ina bukatar abinci da sigari okay sir ya fad a masa inda yake bukatar yayi masa order din abinci sannan ya mike ya sake komawa d akinsa bai jima ba ya sauko ya zauna ya mika masa kudi yana fad a masa irin abinci da yake bukata cike da girmamawa sale adamu ya amsa ya juya ya fice daga parlour Tsakanin gidan da wajen siyar da abinci babu wani nisa shiyasa bai wani jima ba ya dawo a natse ya turo kofar ya shigo dan yasan halin mai gidansa baya son yawon kwaramniyya ,ahankali ya maida kofar ya rufe , wanda tuni shi ata idanunshi a runtse suke yana tunanin mami yana sake jin aransa kamar bai kyauta mata ba ,ko zata iya runtsawa yau ?shi kanshi idan ya tuna furucinsa gareta yana jin fad uwar gaba mai tsanani , yana jin ciwo sosai aransa, idan d an daya haifa ne yayi masa abinda yayiwa mahaifiyarsa yau ya zai ji ?ya tmbyi kanshi . Cike da girmamawa sale adamu ya ajiye ledodin daya shigo dashi akan dogon kujerar din dake gabansa yana cewa sir gashi na siyo duk abinda ka bukata kanshi kawai ya iya gyada masa ,sale adamu ya juya ya fice ATA ya sauke idanushi akan ledodi kafin ahankali ya janyo ya fara bud ewa yaushe rabonsa yaci abinci daga waje ? matsawar yana qasar abincin mahaifiyarsa yake ci amman gashi yau sanadiyyar auren maryam zai koma cin abinci daga waje. tsaki ya ja sannan ya bud e robar abinci inda idanunshi ya soma cin karo da shimkafa yar waje da gasashiyar kaza ya fito da robar fresh milk dana ruwan tataccen inibi . a natse ya soma ci yana korawa da ruwan inibi kusan kazar kawai ya iya ci da ruwan ininbi da fresh milk bayan ya gama ya kunna sigari ya sha iya shansa ya mike ya rufe koina ya haye sama . yana shiga d akin ya cire kayan jikinsa ya saura daga shi sai qaramin plan pant ya kwanta flat akan katifa yana kallon saman d akin yana shafa kwantaccen gargasar gashin qirjinsa dake kwance luf luf ,lokacin da zuciyarsa take son hasko masa fuskar mafarkinsa yayi saurin kawar da hakan ya sako tunanin mahaifiyarsa ,cikin haka wayarsa ta soma ringing bai mike ba har sai data katse aka sake kira sannan ya yunkura ya tashi ya d auka yana duba screen din wayar sunan mb ya gani yana yawo ya d auka ya koma ya kwanta . Acikin wayarsu da mb ne yake koro masa yadda sukai da mami shima dai fad a yayi masa sosai tare da nuna masa mahimmancinta arayuwarsa, yayi qoqarin tun abun bai yi tsawo ba yaje ya bata hakuri ya nemi yafiyata, ya jima yana waya dashi saka makon baccin daya soma ji ne yayi masa sallama ya sake mike wa ya kashe wutar d akin ya bar na bacci guda biyu ya koma ya kwanta ya lullube rabin jikinsa ya runtse idanunshi yana aiyana gobe daga office direct gidan mami za shi ya bata hakuri ko zai samu natsuwar zuciya da kwanciyar hankali . Lullube jikinsa Ke da wuya bacci ya d auke masa cak tamkar wutar nepa sakamakon hoton mafarkinsa bud e idanushi yayi sosai yana sauke numfashi tare da amboton sunan allah wani iri juyi yayi ya canza yanayin kwanciyarsa sai dai yasan tunda ya fara da tunanin acikin irin wannan yanayin ba lalle bane bacci ya d auke shi sai yayi da gaske. yayi juyi yafi sau d ari nan da nan ya soma jin haushin kansa ya kamata ya cireta gbdy arayuwarsa ya samu yayi rayuwa kamar kowani mutun ko kuma ka maye gurbinta da wannan yarinyar ba wannan tunanin ya fad o masa arai abinda bai ta ba ji cikin ranshi ba Kenan sai a yanzu . dogon tsaki yaja yana furta
Chapter 20 · 0% Book details