← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 105

Sashe 76

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 22 Kwanaki hamsin kenan da ATA yasa anemo masa kwararrun masu zane wanda yayi daidai da sauran sati uku daurin auren maryama da yaya sadam acikin lokacin nan babu abinda maryama take sai zariyar zuwa AGC domin gabatar da zanenta, haka zalika ta saki jikinta sosai da yaya sadam domin ta fara cire rashin son da bata masa tana ta qoqarin dasa soyayyarsa mai karfi acikin zuciyarta ,shima kuma bangarensa yana qoqarin kyautata mata shiyasa a yanzu damuwarta ad auketa aiki akar ka shin AGC ne . idan kaga maryama da yaya sadam a yanzu zaka d auka tun asali masoya ne wadan da suka d auki tsawon lokaci suna son juna, abu d aya ne kawai dai har yanzu yake damun zuciyar maryama shine yawon shiru da shiga tunani mai zurfi da yaya sadam din yake ko suna tare ko yana shi kad ai ko ayita kiransa a waya baya d auka agabanta wanda ita hakan na damunta, kuma haka nan take ji ajikinta kamar akwai wani abu dake damunsa wanda yake boye mata , tayi iyakar qoqarinta tasan meye damuwarsa amman abun ya cutura domin dai abu d aya ne kullum yake fad a mata babu komai al amuran aiki ne . mami na zaune a had den parlour nta na farko idanunta na kallon tv yayinda hannunta Ke rike da casbaha tana ja ahankali kira ya shigo wayarta, tasa hannu ta d auki wayarta tana dubawa sunan d anuwanta data gani yana yawo a screen din wayar ne yasa tayi saurin kara wayar a kunneta bakinta d auke da sallama wani irin mikewa mami tayi jikinta na rawa tare da furta kalma inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ,ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagisu aslili shaani kulluhu wala takilni ila nafsin d urfata kace yau kwana biyu kenan da faruwar sakin ?ta tambayesa cikin tsananin damuwa da shiga tashin hankali yayinda cikin tsananin fushi d an uwanta ya cigaba da sheida mata abinda ya faru . wallahi Abdul ban san komai akan sakin nan ba ta fad a jikinta na wani irin bari haka ma zuciyarta bayan ya katse kiran kuka mami tasa tare da jin wani kullin bakinciki ya tsaya mata a qirji yaki gaba yaki baya wayarta ta lalubo ta soma neman layukansa amman shiru bata shiga dan haka ta kira Amar nan ta samu labarin tafiya yayi zuwa hollond abun yayi mata ciwo fiyye da tunanin mai karatu ammar din ma yana tambayarta ko tana son wani abu amman tuni ta katse kiran . batayi sanya a gwiwa ba ta kira ya yanta a waya ai kuwa washegari gabdayansu suka hallara a gidan cikin tsananin tashin hankali aiko mami tasa masu kuka tana kiran adamcy zai kasheni shikenan ya zama sila shiga tsakanina da d anuwana muna zamanmu gwanin sha awa, kana ganinmu kasan akwai shakuwa da soyayya a tskaninmu, muna ta qoqarin had a kanmu dana ahlimu, mun rungume juna babu kyarma muna tsananin son juna amman yau sanadiyar adamcy ran d anuwana ya sosu yayi min abinda bai ta ba min ba .Abdul ra uf bai ta ba min magana cikin fushi ko bacin rai ba sai a jiya ni zulai na shiga uku nah me yasa na had a auren nan ? wallahi dana san abinda zai biyo baya kenan da ban had a ba dana bar adamcy ya cigaba da rayuwarsa haka babu aure dan duk abinda zai lalata zumuncina da yan uwana bana qaunarsa kiyi hakuri mami ki daina kuka haka Allah ya qaddara kowani bawa da kalar qaddararsa wannna rabon dake tsakaninsu fa idan baa yi auren ba ta ina zaa samu ?inji cewar aunty shahida , kuka fa ya zamammin dole abdul rauf na min biyayya duk abinda nace shi yake yi bai ta ba sa bawa umarnina ba "wai mami zaginki yayi ne ko me ?zabiba ta tambayeta ko d aya zabiba abdul bazai ta ba zagina ba amman yayi min magana cikin fushi abinda bai ta ba min ba sai jiya nifa na kasa gane abubuwan nan na yaya adam mutun kamar babu tausayi a cikin zuciyarsa gsky mami yakamata ki san yadda za'ayi da yaya ga ciki ga saki dame sister zataji wallahi ni tausayi take ba ya dawo daita kawai . nana hauwa u ta qarasa mgnr tana sheshekan kuka aunty shahida ta numfasa kana tace karki d aga hankalinki auta kinga kema bake kad ai bace za'a haukatar dashi bari ya dawo daga hollond lafiya amman dan dolensa ya maidaita ta haihu a gidansa idan ba haka ba wallahi wannan karon zai had u da tashin hankali da bai ta ba gani ba ku dai bi komai a hankali domin dai acikinku babu wanda bai san waye yaya adam ba kusan yafi buqatar rarrashi da lalama muddin da tashin hankali zakuje masa wallahi bazai maku abinda kuke so ba . da mamaki aunty khadija ta kalleta abinda muke so kuma ke banda ke ? gsky banda ni abinda kuke so am sorry to say dani yanzu bazan sake goyawa zaman aurensu baya ba ,ya kamata zuwa yanzu abarsu haka kada a takura masa ku kyalesa ya huta idan yayi ra ayin maidaita da kanshi zai yi idan kuma iyakar zamansu kenan Allah yasa ya zama alkhairi ,sun d auki lokaci suna tautaunawa a tsakaninsu sai dai zabiba ta tsaya akan raayinta wanda bai yi masu ba har mami . Bayan kwana uku ahankali oga ATA yake saukowa daga cikin jirki tare da yaransa mutu biyu kai tsaye in da driver da masu tsaronsa ke jiranshi suka nufa, ya qara kyau aciki kwanaki uku kacal farinsa ya sake fitowa ga cigaba da ya samu da nasarori akan business ,yana sanye da royal blue three piece suit daya daga cikin yarasa na sak'ale da bak'ar jakarsa daka ganshi kaga wayayye wanda yasan duniya ko nace duniya ke damawa dashi, yayinda idan ka kalleshi zaka d'auka d'an shekara talatin da biyar ne amma gaskiyar lamari shekararsa arba'in da wani abu yake, da sauri aka bude masa gidan baya ya shiga ya kame yana shan kamshi daya daga cikin wayoyin ne ta soma ringin ya dauka ya soma magana a natse yana ciccin magani har suka qaraso unguwarsu waya yake bai ji komai ajikinsa ba sai da suka shiga cikin haraban estate dinsu yaji gabanshi ya fad'i sakamakon bai san abinda zai tarar ba amman a kudurtawa ransa komai zai faru sai dai ya faru amman har abada bazai qara zama da mrym ba". ahankali ya fito daga cikin motar ya nufi babban falon cikin isa da iza ga kamshin daddan turarensa Reed na tashi ,yasa hannu ya tura kofar glass din parlour n ya shiga ya iske mami zaune kamar koda yaushe yayi sallama aciki fuskarsa a had e tamkar zaki , itama aciki ta amsa masa ya ta be baki yadda ta amsa masa yaso ya bashi dry amman sai ya maze ya d age girarsa duka tare da dakewa ya gaisheta sweetheart barka da rana wannan karon kam shiru tayi bata masa ba bai qara cewa komai ba kai tsaye samansa ya nufa mami ta karkace tabi bayansa da kallo yana taku d ay d ay batare da wata damuwa ko tashin hankali ba sai ma wani kyau da kwanciyar hankali daya samu matsuguni ajikinsa su kuma ya bar zuciyarsu da tashin hankali.duk wani tarba da rawar jiki da mami take akanshi idan ta gansa yau kam babu dan kana kallon fuskarta zaka fahimci akwai damuwa . yadda mami bata masa maganar wata maryam ba shima bai yi mata maganar ba abun ma yayi masa dadi ya cigaba da tsabgogin gabansa da mulkinsa daya saba dan babu abinda ya canja har kawo yanzu dan ji yayi kamar an raba zuciyarsa da matsala ne dan da kullum zuciyarsa cikin tuttukin bakinciki da kunci take idan ya tuna zai koma gida ya ga fuskarta kuma amatsayin matarsa . mami dai bata gaji ba ta sake tara ya yanta har yanzu shiru adamcy bai ce min komai ba ga mrym da ciki har wata uku akace dame zataji saboda Allah ga ciki ga kuma gurb'ata mata raywua da yayi, gashi ya dawo yayi wa mutane shiru kamar bashi yayi sakin ba , ni na gaji wallahi nayi waya daita mrym din ta fad a min abinda ya faru akayi sakin taki sai kuka take min ,shi kuma ya dawo ya min dif wallahi na kasa komai gashi bana son lokaci ya tafi batare data koma dakinta ba dan da zarar mrym ta haihu a gidansu shikenan abu ya sake dawowa baya bazai ta ba maidaita ba mami ta fad'a tana kallon ya yanta d aya byn d aya da suke zaune.aunty khadija tace "kwantar da hankalin ki mami zamu san abun yi bubuwa daya ne kawai ya tabbata a aurensu samun cikin mrym in sha allahu sauran ma zasu tabbata ne"Yaushe? Kusan shekaru ana abu d'aya ace har yanzu an kasa cimma komai babu wanda adam yake shaka daga mami har mu na gaba dashi kowa shakkarsa yake gsky zuwa yanzu dai ya kamata mu tashi tsaye . inji cewar aunty shahida . kallonsu kawai mami take zuciyar na karye wa zaku cimma daman amman dole sai kunyi hak'uri sannan ku bisa ahankali dan karku dinga mgn kuna manta waye shi b'angaren zafin kai da zuciya dole sai kun sha wahala kafin ku samu ku ya sauko ya saurareku ni wallahi dan tani da an bar kome nan kowa ya huta wai meye haka zabiba? sai ki dimga magana kina cire kanki acikinmu idan Kinsan bazaki goya wa mami baya ba me yasa kika zo ?Inji cewar aunty Khadijat to yanzu me nayi kuma ?ai bazan ki zuwan kiran mahaifiyata ba haka zalika bazan goyi da bayan a sake tursasa wa yaya ba haba Auty zabiba ya kike magana kamar babu tausayi a zuciyarki ?karki manta
Chapter 76 · 0% Book details