Sashe 58
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da waya tana chart a group dinsu na matan so ya shigo ko kallon inda take zaune bai yi ba ya nufi hanyar sama yana furzar da hucin iska daga bakinsa da sauri ta d ago daga abinda take tabi bayansa da kallo tana tuno gamuwarta dashi tana sake jin wani sonshi na shigarta amman shi ko kad an bata hango sausauci daga garesa ba har yanzu yana Kan nashi kudirin na rashin sonta kuma ta tabbatarwa kanta da wahala ya sota din dan bata hangowa kanta dalili ko abinda zai sanya shi nemanta ba koda zasu shekara dubu a haka ne , ita yanzu kanta take tausayawa dan duk ranar daya fahimci ya kusancenta wanda itace silar faruwar haka ta kade . Mikewa tayi da sauri tun kafin ya kai ga hawa sama ta sha gabansa tana masa sannu da zuwa tare da qoqarin amsar jakar hannunsa ,wani kallo ya d auketa dashi tun daga sama har qasa sannan yaja tsaki meye haka ?ya fad a a tsawace sannu da zuwa nayi maka sannan ka kawo jakar na kai maka d aki wani tsaki yaja kina da matsala wallahi wai sau nawa zan nuna miki bana son duk wani abinda zai had a ni dake ?sau babu adadi ta bashi amsa da haka tana kallon cikin idanunshi okay tsayawa matsayinki ne bazakiyi ba kome ?Ko d aya wannan hakin daya rataya a wuyana ne kaga dole na sauke kallonta yayi kawai sannan ya cigaba da magana an nan kayan na jikinki da wanda kika saka last week kar na qara ganin kin sashi acikin gidan idan ba haka zaki had u da damuwa yanzu ma kije ki ciresu bana son ganinsu idan ma kina sakasu dani ne kinyi aikin banza dan wallahil azim bazaki dauki hankalina ba saboda bana ganinki a matsayin mace yana gama fad ar haka yabi gefenta ya hau sama. ta biyasa ta shiga d akinsa alokacin yana tsaye a bakin gado ya soma cire kayan jikinsa ta cikin madubi ya hangota tsaye still da kayan da yace ta cire tsaki yaja yayi cilli da kayan daya cire ya shige bathroom fitsari yayi ya fito ya kwanta flat akan katifa yana sauke numfashi tare da runtse idanunshi dan wani irin ciwo kanshi Ke masa wanda ya rasa dalili tun last week yake fama dashi ahankali bacci ya fara fixgarsa , cikin sand a ta shige bayin ta had a masa ruwan wanka ta fito domin had a masa coffe dinsa na gado baccin minti goma yayi ya mike ya fad a bayi yana shirin hada ruwan wanka tsayawa yayi cike da tunani bai yi mamaki ba dan yasan aikinta ne ,haka take masa a duk sanda ta samu damar shigowa d akinsa . ya sanya hannunsa cikin ruwan babu shiri ya shiga dan ruwan yayi masa yadda yake so dan har wani qamshi yake bai bata lokaci ba ya shige bathtube ya kwanta luf aciki kamar wani qaramin yaro dumin ruwan na ratsashi ahankali gajiyar jikinsa ke warwarewa yayinda acan bedrom dinsa maryam tuni ta hau tattara kayan daya cire ta kai inda yake ajiyewa ta sake gyara masa dakin ta feshe da air freshener . Shiru yayi kwance acikin ruwan yana tunanin irin qoqarinta garesa duk duniya a yanzu bayan sweetheart dinsa tafi kowa sanin abinda yake so sannan tana iyakar qoqarinta akanshi sai dai bai san dalilin da har yanzu zuciyarsa ta qasa amincewa daita ba ,zuciyarsa tashiga wasi wasi anya bazai hakura da mafarkinsa ya rungume qaddararsa ba tunda ya rasa mafarkinsa ?hisham ya hakura ya rungume qaddararsa suna zaune lafiya ,daidai gwargwado yarinyar tana binsa tana masa biyayya tana jin tsoronsa wanda abinda yafi buqata kenan ga matar aurensa. idanunshi ya daga ya kalli saman bayin karka kuskura ka karbi wannan yarinyar yanzu ta yaya zata nuna irin wannan matar a idon duniya matsayin matarka ?mace sam babu tsari mace kamar ba halitta mutane ba wannan yarinyar kad an ya rage bata zamo wada ba .tunani ya dinga yi ya dauki wannan ya duba ya ajiye akanta a qarshe yace no way Adam you can do that sam sam bata cancata ba kwata kwata ma bawan nan tunani ya kamata ka tsayi ba kai da kake da tafiya agabanka a gobe gara ma ka tafi ko zuciyarka zata samu natsuwa dan yawon ganin ayyukan alkhairinta gareka zai iya sauko da zuciyarka kuma abinda bazaka so faruwarsa ba kenan wannan tunanin yasa shi mikewa daga cikin bathtube ba dan ya gama awanni daya saba yi ciki ba ya saba sabulu ya qarasa wanke jikisa ya daura towel ya fito . Abakin madubi ya tsaya da niyyar shafa mai yaji ta shigo ta matso kusa dashi zata kai hannunta jikinsa yayi saurin matsawa yana mata wani irin kallo yana mai jin zafi da haushin shishigi irinta bata damu da irin kallon tsanar da yake mata ba ta sake matsoshi wani mugun tsaki yaja yana sake matsawa tare da jin zafi, zuciyarsa na sake tsanarta ya qarasa gefen gadonsa wani abu ya danna a gefen gadon take duk wasu kayan shafe shafensa suka bayyana ya soma dauka daya bayan daya yana amfani dashi tayi taku uku ta tsaya abayansa har yana jin saukar hucin numfashinta ya juyo a fusace tayi saurin ja baya hanyar fita ya nuna mata da yatsan hannunsa yana cewa wai me yasa baki da zuciya ne ?dole ne ?! nace dole?!! nace banayi banason ganinki a inda nake ki kama kanki mana ko dole sai mun hada inuwa daya dake ?nasani ba dole bane amman ni ina qoqarin sauke hakinka dake wuya ne nace bana so ,In your life don t you ever enter this room again idan ba haka ba duk abinda nayi miki kice kika jawowa kanki leave ya sake nuna mata hanyar fita . Shikenan zan fita amman ga flaks din coffe can na kawo maka nasan zaka buqata oh my goodness god ya furta yana dafe goshinsa murmushi tayi sannan ta fita tana leka fuskar shi bayan ta fita yaja tsaki sannan ya cigaba da abinda yake byn ya kammala ya fitar da qananun kaya ya saka sanann ya sanya takalmi silifas wanda ya dace da kayan jikinsa a nutse yake saukowa qasa, har yanzu parlour n shiru yake bata ma cikinsa bai damu ba sai ma dadi yaji da bai tarar daita ,tunanin abinda zai sakawa cikinsa yake dan tun safe zuwa yanzu bai ci komai ba hankali ya samu waje ya zauan yana kiran daya daga cikin masu tsaronsa byn ya dauka yace a turo masa musa domin samo masa abinda zai ci . cikin kankanin loaci musa yayi knocking ya bashi izinin ya shigo ya fad a masa abinda yake so ya ciro wallet dinsa, fararen sababbin yan dubu dubu guda goma shabiyar ya mika masa ya juya ya fita da sauri shi kuma ya mike akan kujera ya kwanta ya daura hannunsa daya akan cikinsa yana shafa lafaffen cikinsa . Bai Jima da kwanciya ba musa ya dawo yayi knocking kofar parlour n yana daga kwance ya bashi izinin shigowa ya shigo cikin parlour n hannunsa da fararen ledodi cike da girmamawa ya sake gaishesa aciki ya amsa tare da mikewa zaune ya amsa ledodi ya ajiye a saman table din gabansa wallet dinsa ya sake ciro ya ciro kudi ya mika masa musa yayi Godiya ya fice daga parlour ahankali ya bude ledodin ya baje akan table din gabansa ya fara ci sai daya ci ya koshi sannna ya mike ya ya bar sauran ya haye sama alokacin an fara kiran sallar magrib bayi ya shiga yayi alwala ya fito ya fita zuwa massalacin dake manne da gidansa bai dawo gidan ba sai wajen qarfe goma yana shiga d akinsa system dinsa ya kunna ya zauan akan kujera. kusan karfe daya na dare ya kai yana faman aiki akan system wanda maryam duk tana hankalce dashi dan itama sai zariya take daga d akinta zuwa parlour n qasa cikin wasu hadaddun kayan bacci sosai ATA ya gaji kuma alokacin babu abinda yake bukata kamar coffe dole tasa ya janyo flaks din da maryam ta ajiye masa da cup ya tsiyaya ya fara sha yana cigaba da aikinsa kafin ahankali bacci ya fara fixgarsa ya tattara komai ya ajiye ya kwanta nan da nan wani bacci mai nauyi ya daukesa .ahankali maryam ta shigo dakin , ta tsaya akansa tana qare masa kallo tsab ina ma zaka iya bani dama dana bayyana maka irin yadda nake ji akanka azahiri bani da muni da kake tsanata akanshi ,duk wani abu da mece take dashi na daukar hankali ina da shi yaya Adam, abu daya ne kawai bani dashi shine tsawo kuma nima bani nayi kaina haka ba ,haka allah yake son ganina . Tana tsaye shiru tana kallon tana zance zuci daya daga cikin wayoyinsa ta dauki qara da sauri ta durkusa kasa ta kamkame jikinta wuri daya tana rawa jiki, ya lulobo wayar ya daga da kyar batare daya bude idanunshi ba sakamakon nauyin da sukai hello !!! yaji shiru dan haka ya mayar ya ajiye wayar ya koma ya kwanta da hannu hagu . ta sauke naunayen ajiyar zuciya ta mike a hankali tana lika fuskarsa bacci ya koma dan hk ta soma kokarin dawo gabansa ta zuba masa idanunta tana jin kamar ta had iyesa tsabar son da take masa shine farin Cikinta wallahi da zaa tambayeta dashi da kanta wa tafi so tabbas shi zata za ba akan kanta wani kiran ya sake shigowa da wani irin mugun sauri ta hantsila byn kujerar sofa tana rawar jiki .okay zuwa gobe kenan eh kazo mu wuce ta nan iya abinda taji ya fad a kenan ya kashe wayoyinsa gbdy ya koma ya kwanta yana sauke ajiyar zuciya wani bacci mai nauyi ya daukesa cikin sand a ta fito daga bayan kujera ta tsya akansa kusan mintuna talatin tana kallonsa kafin ahankali ta kai hannuta fuskarsa taji gabad aya yanayin saukar numfashinsa ya canza tayi taku biyu ta haye gadon ta kwanta abayansa rungumesa tayi tsam ajikinta tare da zagayo da hannuwanta Kan qirjinsa tana shafa Kan nipples dinsa da hannuwanta duka wani wahalallen numfashi ya sauke . Ahankali ta dinga murza