← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 105

Sashe 24

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 8 A matukar razane maryam take kallonsa jikinta na wani irin rawa idanunta suka canza kala sakamakon hawayen data soma d'an taruwa acikin kwayar idanunta cikin tsananin fad'uwar gaba maryam tace "ga ..gashi can akan table sai dai ba'a samo exactly irin ..."sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa maganarta dan tasan me karshen maganar tata zata janyo mata, ta tsura masa ido kawai tana cigaba da kallonsa hawaye na gangaro mata akan kuncinta ." "exactly irin me ye ba'a samu ba ? yayi maganar a tsawace yana sake had'e fuska "ta runtse idanunta gam hawaye masu zafi suka biyo kuncinta "irin wanda kake sha n ba'a samo ba "me yasa ba'a samu irinsa ba ?"ya tambayeta yana tsareta da tsuma mmun idanunshi masu matukar firgitarwa "tayi shiru tana kallonsa hawaye na faman turereniyar zubo mata "nima ban....ban sani ba ?"ta fad'a a muryarta na rawa tana share hawayenta da hannunta d'aya tare da kai tafin hannunta daidai saitin zuciyarta dake beating very fast ." Tsumammun idanunshi ya ware sosai akanta yaga yadda ta qara shiga tashin hankali wanda hakan Ke masa dadi, a duk lokacin daya ganta cikin damuwa yana jin sukuni aransa, wani abu ya had'iye mai d'aci a makoshinsa kafin ahankali ya motsa lip's dinsa da kyar "babu ruwana ki nemo min exactly irin sigarina shi nake bukata kuma a yau dan kinsan halina sai dai ki bawa wani labari ,ban ta'ba d'agawa kowa kafa ba kuma bazan fara akanki ba yana gama fad'ar haka ya juya a zafafe ya soma d'aga kafafunsa zai haye sama ." jiki a sanyaye ta qara taku biyu tana wasa da yatsun hannunta tace "wallahi yaya Adam ban san yadda zanyi a samo maka irinsa ba sai dai kayi hakuri ka aika wanda ya saba zuwa inda yake siyo maka ko kuma kayi amfani da sauran na jiya ."wanda kika zubar a shara kike nufi ?ya juyo a fusace tare da fad'ar haka, taja baya da sauri tana gyad'a masa kai gabanta na dukan uku uku "you are very stupid ,ki nemo min ko kuma inci ubanki acikin gidan nan yau ." "Ubana kuma !?"yes of course ubanki ko zaki rama ne da kika tsaya kina tambayata ?ta sauke numfashi tana girgiza masa kai "okay ki nemi min abata kuma irin wanda kika wulakanta min cikin kasa da murya tace "ni dai gsky ban san yadda zanyi ba kai dadin me ma kake ji a shan sigari abinda zai cutar da kai ? ni zaki fad'awa haka ? kanta ta gyad'a masa alamun Eh !to ai gsky ne me zakayi da wani sigari abinda yake saurin kashe mutun "are you out of your sense ?." "ni kike fad'awa haka "? shiru tayi tana tunani amsar da zata bashi wanda kafin nan idanunta sun sake kawo hawaye tace "yanzu meye illar maganata bayan gsky na fad'a maka "?"Are you mad ?"da sauri ta girgiza masa kai alamun a'a "okay iskanci ne kenan yasa ina magana kina magana ?"ta sake girgiza masa kai idanunta na kawo ruwan hawaye domin dai gbdy a tsorace take dashi ,maganar ma allah ya sani dauriya ne kawai take yi da kuma son rage tsoronsa dake kunshe a zuciyarta ". cikin rawar murya tace "am sorry"!da sauri yace "sorry for your self "amman dai kuma kasan shan sigari yana da matuqar illa sosai arayuwar d'an adam "so what? ina ruwanki da rayuwata ?gabanta taji yayi mummunar fad'uwa ta shiga girgiza masa kai hawaye na sake fita daga idanunta ."ahankali taga ya soma takowa zuwa inda take tsaye yana mata wani mugun kallo ."nan da nan jikinta ya fara rawa ganin idan ta tsaya kanta zata cuta yasa ta juya da sauri ta fad'a d'akin dake manne da parlour'n ta murd'a key ."ta jingina bayanta da kofar ta tsaya tana sauke numfashi. A zafafe ya qaraso jikin kofar ya tsaya tare da runtse idanushi kafin ya dunkule hannunsa ya kai wa kofar naushi yace "me yasa kika gudu baki tsaya ba kiga yadda zanyi dake shasha duwaf din banza kawai ? wallahi wallahi da kin tsaya da sai na karya miki kafa sai dai uwarki ta haifi wata mai kama dake nonsense "muryarta a sanyaye tace "kayi hakuri dan allah bazan sake ba ."yana jin yadda take kuka take bashi hakuri tana tsaye kusan minti biyar dafe da saitin zuciyarta dake bugawa da sauri sauri , taji alamun tafiyarsa amman ta kasa fitowa har sai da minti biyar ta wuce bata sake jin motsinsa ba hakan ya tabbatar mata ya bar gurin . ta bud'e kofar ahankali ta fito tana maida numfashi tare da goge hawayenta ta hau sama, ahankali ta sanya kai cikin d'akinsa ta leka tsaye ta samesa ya bawa kofar baya hannuwansa hard'e a saman faffad'an qirjinsa sai huci yake fesarwa tmkr zakin daya nemi abincinsa ya rasa ,gefe guda kuma duk ilahirin gashin dake kwance a jikinsa sun mike tsabar bala'i ji tayi kamar taje ta rungume shi ta baya ta sake bashi hakuri ya sauko dan bata son ganin yana fushi most especially daita ." Wani dogon tsaki yaja yana sauke hannuwansa ya rike kugunsa da hannu d'aya acikin ransa yace "wannan wace irin jaraba ce ?yarinya kamar mayya duk abinda zai mata bata damuwa ko ya zagi uwarta ya zagi ubanta duk a banza baya mata ciwo sai dai tayita bashi hakuri "ya fahimci mugun hakuri ne daita ,kuma shine dalilin da yasa mahaifiyarsa tayi masa sha'awar aurenta" tsaki yaja ya soma cire kayan jikinsa ya fad'a bathroom ya sakarwa kanshi ruwa ya fito ." Bai sauya wasu kaya ba vest da boxcer kawai ya saka ya kwashi wayoyinsa guda biyu ya sauko zuwa parlour'n kasa ya zauna ,ya d'auki remut ya canza channel sannan ya d'auki wayarsa ya soma danne danne yana duba sakwani mutane ringing din waya ne ya karad'e parlour'n ya bar abinda yake yana yatsina fuska alamun qarar na damunsa ko ba a fad'a masa ba yasan qarar wayarta ne ,can gefen kujera ya hango wayar yashe tsaki yaja , ya d'auke kanshi ya cigaba da abinda yake yayinda aka cigaba da kiran wayar ,qatar wayar ta dameshi sosai gashi kuma shi bazai ta'ba iya bud'e bakinsa ya kirata ba ." cikin haka ta sauko ta shiga kitchen ta soma fito da abubuwan da zatayi amfani dashi na girki wayarta ce ta sake d'aukar qarar sauti ,ya tsaya cak ya bar abinda yake ransa na qara 'baci ,da d'an saurinta ta fito tana goge hannunta da towel ta soma duba inda wayar take ta d'auka taga sunan mahaifiyarta ce ke yawo a screen din wayar tayi shiru ta kasa d'auka a gabansa ,ta d'an d'ago ta kallesa taga ita yake kallo ta qasan idanunshi "nan take gabanta ya shiga fad'uwa "mummy ce "ta fad'a muryarta na rawa." " yasan zaa rina dan zata fad'a masa ko wacece ta kira ,tsaki yaja "na tambayeki ne ?ya fad'a yana sake jan wani tsaki "naga kana kallona ne shiyasa nayi tunanin ko kana neman qarin bayani ne "akan me kenan zan bukata ?duk ma wanda zai kiraki ya kiraki mana menene matsalata da hakan ?kai kuwa kake da matsala dani tunda zamanka nake "ta fada tana tsura masa ido taji abinda zai sake fad a ."bai sake cewa uffan ba yayi tmkr bai ji abinda tace ba ta juya ta koma kitchen ta kira layin mahaifiyarta tana aiki suna waya daita wanda duk hirar akan zaman aurenta ne ." ****** Da misalin karfe shida daidai hisham ya shigo gidan a gajiye a parlour'n gidansa ya zauna yana sauke numfashi nana hauwa'u dake zaune cikin tsananin tashin hankalin abinda zai faru tsakanin maryam da yayanta tai masa sannu da zuwa babu yabo babu fallasa ya amsa yana furta "wash allah ! sannu ka gaji ko ?girarsa ya dage mata alamun eh ! ko cikakken minti biyu bai yi da zama ba nana hauwa'u ta mike tsaye tana cewa bari naje na kawo maka ruwa mai sanyi kasha ya juya "tafiyarta yabi da kallo ,yadda take jujjuya jikinta yana ta basa. Daman kuma ba tun wannna lokacin ba yasan tana da kyawun jiki sosai fiyye da maryam dan tana da tsawo sosai , gyara zamansa yayi ya cigaba da kallo every step of her , . ya runtse idanunshi sannu ga ruwa kasha da alamun ka gaji dayawa yau "ta fad'a tana miko masa cup ahankali ya bud e idanunshi yana kallonta sannan ya karbi cup din hannunta alokacin da wayarsa ta fara ringing ,ya ajiye cup din ruwan akan table din gabansa ya ciro wayarsa a gaban aljihun rigarsa yana duba screen din wayar ." ganin mai kiransa ya d'auka da sauri yana cewa "hello my dear " Wani irin bugu qirjin nana hauwa u yayi da karfi ko baa fad a mata ba tasan ko wacece ta kirasa ta samu waje kusa dashi ta zauna tare da janyo kafafunsa ta d aura akan cinyarta ta soma mammatsa masa no no!! your time is my time my time is your time am always with you,kowani lokaci naki ne karki damu am always with you my dear ai tunda nace miki zanzo zanzo ne bari na dan watsawa jikina ruwa ,ko banzo yanzu ba zan shigo da daddare "tunda ya cigaba da wayar ta kasa cigaba da massaging din da takewa lafafunsa ta janyo wayarta tana neman layin maryam taji yadda suka qare da yayanta . Kira kusan biyar tayi mata bata d aga ba yayinda hisham ya cigaba da wayarsa da nuzlah yana fad a mata kalamai masu sanyi da sanya natsuwa wanda hakan yasa nana hauwa u ta soma jin wani iri aranta zuciyarta ta dinga tafasa tana mata zafi da ciwo ,nan da nan yanayinta ya sauya haka ma kwayar idanunta ta cika da ruwan hawaye sai dai duk yadda taso ta danne amman sai da sheshekar kukanta ya bayyana "ta fara
Chapter 24 · 0% Book details