Sashe 79
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da mahaifiyarsa ta hadasu bata ta'ba jin komai akansa ba sai dai tana danne komai saboda mahaifiyarta da mahaifiyarsa . yana ganin girman mahaifiyarta sosai yana kula dasu sosai tun kafin a had asu aure "kinyi shiru kina kallona kice wani abu mana ?shiru ne dai Ya sake biyosa baya har sanda wayarsa ta dauki qara sauti Ya dauki wayarsa dake ajiye a gefensa ya duba sunan nadia ya gani yana yawo a screen din wayar cike da firgic ya dubi inda maryama take sannan ya sake maida idanunshi akan wayar da kyar ya sauke naunayen ajiyar zuciya yayi disconnecting din kiran ya cigaba da magana " a she dai ni ne wanda zanyi wuf da wannna kyakkyawar yarinyar magana yake amman zuciyar maryama ta kasa samun natsuwar allah sarki yusif ashe Ke din ba rabonsa bace ?naunayen ajiyar zuciya ta sauke kina da kyau sosai na godewa ummah datayi tunanin hadani dake na gaji da ganinmu haka ina son na killaceki a gidana "kana son ka killaceni agidan cike da rashin yanci ba ?tayi masa tmbyr a zuciyarta . maganar da nake miki yanzu haka komai da zan saka agidanmu ya kammala zamu yi rayuwa mai dadi ko kina son na ajiyeki a wajen umma ne saboda yanayin aikina. ? yana gama fadar haka Ya mike sakamakon wayarsa data sake daukar qara "excuse me! ya kamata ace kana duba yanayina yaya sadam har yanzu ban ji amincewarka akan aikina ba zaka yarda na cigaba da yiwa kafanunka zane ko kuwa ?. bana son sai bayan munyi aure kace bakasan da zance ba wannan aikin rayuwata ce kuma ina son ya kai ni matakin da ya zarta yadda nake a yanzu babban burina bai wuce na samu aiki kafanin AGC ba .ta shiru tana jiran taji mai zai ce amman yayi mata shiru saboda raayinsa amman dole yanzu kam ya amince dan yasan idan yaki amincewa zai ta ba zuciyar ummansa ya tsura mata ido yana nazarinta a yanayinta zata iya komai akan aikinta ." ta mike a natse tana dubansa "kayi shiru yaya sadam kace wani abu mu kawo qarshen maganarmu banason muyi aure daga baya muzo muna samun matsala akan aikina "ka amince zaka aureni da aikina sannan zaka min hanya naga mai kafanin AGC ? ta fad a hk sbd tasan su yusif nada hanya da karfin iko shiru yayi yaki cewa komai yana sauke numfashi da kyar, domin kuwa abu biyu n suka hade masa guri daya ga tambayar maryama ga kiran da nadia ta damesa dashi wanda baya jin zai iya duka abu biyu din ." Ina duba yanayi na zaman takewar aurene yaya sadam domin kuwa kai kana cikin mutanen da suka san koni wacce irin rayuwar gidanmu mahaifiyata da mahaifina ta mgnr tmkr zatai zubar da hawaye dan gbdy idanunta har sun canza kala daga fari zuwa yellow "ya kamata mu tsara komai yaya sadam domin kuwa banason damuwa arayuwar aurena ta qarasa mgnr tare da kai yatsun hannunta biyu ta dauke hawayen dake kokarin saukowa kuncinta ". numfashi ya sauke da karfi sannan yace "shikenan zakiyi aikinki bari naje ana nema zamuyi waya ya fada yana kokarin barinta tsaye tare da manna waya a kunnensa ya nufi kofar fita ta shiru tsaye tana duban bayansa "yanzu irin wannan mijin zata aura tai rayuwar aure dashi ?anya kuwa idan ta auresa zata ji dadin rayuwar aure kuwa yadda yake da rashin nuna caring ? yanzu a halin da take ciki kowa Ya ganta yasan tana cikin damuwa dan gbdy komai nata Ya canza amman kalli yadda ya bar gabanta batare da Ya tsaya ya fahimci matsalarta ba bare ya kawo mata mafuta oh allah karkasa nayi Kuskuren aure irin wanda Mahaifiyata tayi ya allah ka taimakeni kasa ya canza duk da banason shi saboda rashin caring dinsa dan kusan matan duniya shine matsalarsu a gidajen mazajensu a yanzu, cike da sanyin jiki har ya bacewa ganinta tana tsaye a wurin rungume da hannunwanta a kirji jiki a sanyaye ta nufi kofar part dinsu ." ******* motarsa na shigowa haraban ma'aikatan yaji gabansa yayi wani mummunar faduwa da karfin gaske shiru yaki fitowa daga cikin motar yana tunanin abinda yasa yaji hk byn tun a gida bai tsinci kansa cikin wannan yanayi ba sai daya shigo ma'aikatan iskar ya furzar ya daga kafadunsa alamun babu komai a hankali ya zuro kafafunsa dan tuni an bude masa kofar mota ya fito yana gyara zaman suit din jikinsa sannan ya soma taku a hankali qirjinsa na cigaba da luguden bugu yayi qoqarin kawar da yanayin da gangar jikinsa ya shiga ta hanyar tura hannusa daya cikin aljihun wondonsa." duk inda ya wulga maaikata ne Ke kokarin kawo gaisuwa sai dai kai kawai yake gyada wasu ,wasu kuma yayi masu banza har ya hau lift da zai kaisa sama na uku inda anan office dinsa yake yana sauka yaji wani sabon faduwar gaba wanda ya rasa dalili nan ya dan rage tafiyar da yake ya dawo yana daga kafafunsa da kyar saboda sanyin daya ziyarcesu alokacin daya tun daga nesa ya hango bayan wata yarinya suna magana da wasu daga cikin maaikata kamar ya tsaya sai kuma ya karya kwanan da zata kaisa office dinsa cak yaja ya tsaya sakamakon jiyo sautin muryar yarinyar shiru yayi yana cigaba da saurara maganarta tamkar dai mafarkin da daya saba yi anya kuwa muryar tace ko dai mafarkin daya saba yi daita ne suna hira ?. hannunsa ya kai yana shafa daidai satin zuciyarsa dake bugawa tmkr zata fasa qirjinsa tayo waje ya dinga jin tamkar yayi reves ya dawo ya shiga inda yake jiyo murayarta ya tabbatar ita din ce ko kuwa muryar ce kawai tazo daya amman sai zuciyarsa ta kwabesa wankakkiyar zuciyarsa ta sake yin magana dashi kaje ka duba ko itace wata zuciyar tace kai ba itace ba ,ba yarinyar mafarkinka bace, dan haka a natse ya daga kafarsa daya bai kai ga ajiyewa ba ya sake jiyo sautin muryarta"."ku ne fa kuka bukaci kwararrun masu irin aikinmu yau tsawon wata guda kenan ina zariya a ma'aikatan ban samu nasarar ma hawowa saman ba sai yau ,yau din tun karfe bakwai na safe nake cikin compaing dinku kafin ma ku yarda na hawo saman nan sai da kuka bata min lokaci na samu da kyar na hawo yanzu kuma kuna kawo min qabli da baadi kunsa irin wahalar dana sha kafin na kammala aikin nan kuwa ?"kunsa lokacin da yake daukar mutun kafin mutun ya kammala ,shikenan shikenan!! tunda bakwa bukata ku bari na wuce na kama gabana daman an fada min wahalar banza kawai zanyi byn hka bakwa girmama masu tallata kasuwancinsu tana gama fadar hk ta juya haka zalika fuskarta a rufe take "no madam bamuce bama bukata ba mutane dayawa sun kawo nasu zanen maganar da nake miki har yanzu mai gida bai duba ba bare ya tantance bazamu iya cewa komai ba a yanzu dole sai an agwadawa boss ". Ta juyo ta fuskacensu sosai. har zuwa wani lokaci kenan zaa gwada masa sannan zuwa yaushe zanji feed back ?zai iya daukar wata uku zuwa ..tsaki taja ta sake juyawa tana tafiya tana cewa "gashi nan na bar maku bana da bukata domin ko na koma dashi gida babu amfani da zai min ."snyayen Kamshin turarenta ya bugi hancinsa yayi saurin lumshe idanushi zuciyarsa na cigaba da mugun bugawa ta kusa dashi tazo ta wuce har tayi taku uku ta fahimci ba ta nan hayar fita take ba dan haka ta sake juyo wa ta nufi kofar da lift yake ahankali Ya juyo yabi bayanta da kallo yana kallon every step of her doguwa ce sosai kuma bakar mace ce yayinda tsayinta ya fito da ainin shape dinta na cocacola iya haka kawai ya iya fahimta domin hannunta da kafafunta abayyane suke haka hijab din dake sanye ajikinta qaramin ne hkn ne ya bashi damar dan fahimtar wani abu a tattare daita " ATA yana tsaye tamkar gunki yana kallon tafiyar yarinyar da bai san ko wacece ba amman jin sautin muryarta da yanayin tafiyarta yasaka zuciyarsa jin wani irin tsoro mai tsanani da shiga tashin hankali shi gani yake ma babu tantama itace ba anya kuwa ba gizo tayi masa ba kamar yadda yake ganinta a mafarkinsa har yanzu kwayar idanunshi yana Kan hanyar databi ya kasa kwakwaran motsi wani irin ajiyar zuciya ya sauke tamkar ya dakatar daita ya daga black nikaf din dake manne da idanunta yaga fuskarta amman gangar jikinsa da komai nasa yayi rauni zuciyarsa kuwa sai bugawa take babu Kaukautawa ba shiri ya dafe daidai saitin zuciyarsa ya a manne jikinsa da bangon wurin dan yanayin da yaji akanta ya wuce misali hakan yasa kafafunsa suka kasa dauakarsa ."ya sake kurawa hanyar data bi ido har lokacin tafiya take mai hade da rasauya tamkar fure hankalinta kwance take taka kasa tana gyara zaman qaramin hijab dinta wanda akewa lakabi da haif sunnah, gyara tsayuwarsa yayi sosai tare da zura hannunwansa duka cikin aljihun wondonsa zuciyarsa na cigaba da bugawa da sauri sauri yayinda gabadaya ma'aikatan dake aiki a office din da maryama ta shiga suka fito domin binta da makeken hotonsa wanda ta zana ." turus sukai gabadaya suna kallonsa kowannensu ya gyara tsayuwarsa yana kare masa kallon abinda basu ta'ba ganin ya faru ba, basu ta'ba ganin abinda ya dauki hankalin mai gidan nasu ba sai yau ya kusan miniti goma yana tsaye yana fama da zuciyarsa dake karkarwa" Wayyo allah ina ma zai iya da yasa an dakatar daita ko sau daya yaga fuskar ko mafarkinsa ce har ta shige lift bai motsa ba ,sautin gaisuwarsu ce ta dawo dashi hankalinsa a natse .kallo daya yayi masu ya juya batare daya amsa ba yana tafiya yana sauke numfashi a natse ya dinga daga kafafunsa tamkar mara laka a jiki jikinsa baqaramin sanyi yayi ba har ya shiga office dinsa ya wuce sectary dinsa zaune tana ganinsa ta mike da sauri cike da girmamawa ta biyosa office dinsa har sai data ga ya samu wuri ya zauna "good morning sir cewar sectary ya gyada mata kai ta wuce domin komawa bakin aikinta , a can waje kuwa tabe baki ma'aikatan sukai sannan suka koma office