Sashe 86
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
maku ba ,su waye ku ?meye hadina daku ?laifin me nayi maku ?ya jera masu tambayoyin yana sake riko maryama jikinsa "kai karka nemi ka rainawa kanka hankali dan ubanka kayi tunani laifin daka aikata acikin satin nan wanda kai kanka kasan dole zaa iya bibiyarka?". yaya sadam yayi shiru yana nazarin maganr shi dai asaninsa bai aikatawa kowa laifin komai ba baya ga auren maryama da yayi "har kusan minti biyar yaya sadam bai ce uffan ba yasa suka cigaba da magana "me taurin kan tsiya kawai amman tunda baka tuna ba idan kaje lahira zaa maka bayani dalla dalla akan taurin kan da kayi ,kai jojo ku daukosa mu aikasa lahira yadda yayi taurin kai dan son more duniya bazai zauna a duniyar ba "nan da nan suka rufe masa ido da bak'in kyalle ,suka d'aure masa hannayensa duka abayansa kafafunsa ma a d'aure ,suka rufe masa baki suka ciccibosa suka watsa shi acikin mota "itama yarinyar kuyi mata kamar yadda kuka masa ku sata acikin mota ku had'a daita batare da 'bata lokaci ba aka rufe fuskarta aka tasa keyarta cikin mota tunda tashiga motar take rutsa kuka mai ta'ba zuciya tare da kiran sunan Allah yayinda yaya sadam yasa hannuwansa duka ya dafe goshinsa yana zurfafa tunaninsa alokacin da motocin suka karya kwana cikin wani kungurmin daji mai cike da duhu da ban tsoro suna sharara gudu." tunanin duniya yaya sadam yayi amamn iya tunaninsa bai ga wanda zai iya masa haka ba idan safiya ce yasan baa akansa zata huce ba sai dai akan maryama tunda tasha fad'a masa muddin taganta sai ta aikata lahira ."nadiya kuwa yasan kwata kwata bazata masa haka ba shi kuwa wa yayiwa laifi ?"idan ma laifi ne to sai dai akan auren maryama da yayi ne to waye wanda zai masa hk ?bai samu amsar tambayarsa ba yaji motocin sun ja wani irin burki sun tsaya a daidai karshen dajin tare da bubbud'e kofofin motocinsu a zuciye, na karshen ne ya fito rike da kwalar rigar yaya sadam wanda babu halin yin kwakwaran motsi ballantana yasamu damar yin ihun ceton ransa da'ake barazanar raba shi dashi, ahankali suka shiga jansa a k'asa suna tafiya dashi cike da tsansar rashin imani , wanda kallo daya zaka masa kasan a rikice yake d'aya daga cikinsu ya rike hannun maryama ." Basu tsaya akoina ba sai a bakin wani katon rami suna huci "ku binnesa da ransa jin haka yasa maryama ta rikice ta gigice tashiga wage wage tana kiran sunan yaya sadam "dan girman allah karku kashesa karku binnesa da ransa gara ku kasheni wallahi banason na rasashi yana da matukar mahimanci arayuwata na bada rayuwata fansa, gara ku dauki raina ku barshi dan Allah karku kashesa duk wani abu da zaku masa kuyi min ni daman nafi bukatar mutuwa da rayuwata dan bana jin dadin rayuwar nan na rasa komai karku bari na rasa mijina tausayinta ya kamasu "d'aya daga cikinsu ya jawosu gefe yace "me kuka ga zaa yi ?"ya tambayesu "kar mu batawa kanmu lokaci wajen tausayi mu cika aikin daaka ba mu "shikenan a wuce gurin . aiko suka dauki yaya sadam suka jefa cikin rami suna shirin jefa maryama mutun daya acikinsu wanda shine yafi jin tausayin maryama yace mu barta tunda daman shi kadai aka bamu aiki "okay! suka amsa. a matukar gigice take batasan ya akayi ba ta zare kyalen da suka rufe mata ido dashi tana gama bude idanunta yaya sadam dinta ta gani acikin rami suna zuba masa kasa zuciyarta ce ta tsaya cak ta daina aiki a lokaci har suka rufesa da ransa ." Bayan sun gama suka hau jijigata a gigice ta dawo haiyacinta idanunta na zubar da hawaye wani razananniyar qara ta saki da karfi tana kiran "ina mijina yake ?idan har kun kashesa ku had'a dani ku kashe dan allah karku barni a raye dan bazan iya rayuwa babu shi ba haka ma mahaifiyarsa ." numfashi suka sauke atare "aikin gama ya gama yarinya tuni mijinki mai taurin kai yana cikin nan suka nuna mata inda suka binnesa, an gama da labarinsa sai dai uwarsa ta haifi wani idan an sake haifosa a duniya bazai sake kinjin magana ba "ai tana gama jin maganarsu numfashinta ya soma barazanar d aukewa "me yasa ?me yasa zaku masa irin wannan hukuncin inna lillahi wa inna ilaihi rajiun me yasa zaku kashesa tayi taku biyu zata isa inda suka binne mata miji kafafuwanta suka gagara daukarta ga wani irin nauyi da kanta yayi idanunta suka fara rufewa jiri take gani nan take ta zube kasa sumammiya ." Mmn Sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 26 Ran ATA a matukar 'bace yake zaune acikin jirginsa yana tunanin maryama ,wani irin ciwo yake ji a zuciyarsa dan bazai iya misalta yanayin bugun zuciyarsa ba ,ga wani sara da kanshi ke masa har baya iya bud'e idanunshi sosai yayinda kowani second 'bacin ransa na sake nunkuwa wanda baya raba d'ayan biyu damuwar maryama ce bai san dalilinsa na kai hannunsa jikinta ba ."mai yasa yaji sauyi ajikinsa adalilin sake d'aura kwayar idanunshi akanta ?"mai yasa yaji yana buqatar ganin fuskarta a zahiri ? yana jin wani irin sauyi akanta lallai yana buqatar ganin halittarta a zahiri zuciyarsa ta amsa masa kuwan haka ." da wannan tunanin ya isa gida alokacin da magariba ta kawo kai .jirginsa mai saukar ungulu na gama tsayawa a haraban gidansu rai a 'bace yake tattaka matattakala yana qoqarin saukowa , kai tsaye ya shiga bangaren mami sosai yake jin damuwa acikin zuciyarsa qoqarin danne damuwarsa yayi dan kar hankalin mami ya tashi sai dai kallo d'aya tayi masa ta fahimci akwai damuwa atattare dashi ." "muryarsa a kasalance ya gaishe da mami ."kamar ko yaushe ta amsa masa tana mai tsura masa kwayar idanunta kamar wacce taga wani sabon halitta ,cike da kulawa tace "sannu da zuwa adamcy ya hanya ka dawo lafiya ?da sauri ya amsa mata da "lafiya !"yana qoqarin hayewa samansa hannunsa d'aya soke acikin aljihun wandonsa .bayansa tabi da kallo "shigowarsa cikin wannan yanayin yasa duk mami ta d'an rikice kasa samun kwanciyar hankali tayi ,cike da tashin hankali ta mike tsaye tabi bayansa . ahankali ta tura kofar parlour'nsa ta shiga duhu falon dan haka ta kunna wuta nan da nan haske ya haskaka koina a parlour'n sai dai bata gansa ba dan haka ta nufi hanyar bedroom dinsa ta shiga nan ta iskeshi tsaye ya jingina jikinsa da bango d'akin yayi sama da kanshi hawaye ne kwance acikin idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasa ya rasa meke masa dadi arayuwarsa bai san ta ina zai fara ba ,komai ya rigada ya tsaya masa gabad'aya baya jin dadin rayuwarsa ,ya kasa fahimtar kansa ko kuma yace yau tazo masa da abubuwa da yawa wanda duk tarin damuwa ne akan wanda yake ciki ya dinga jin kamar ya kashe kansa ya huta da rayuwar da yake ." lumshe tsumammun idanunshi yayi sai ga hawaye sharrr na bin kuncinsa "adamcy nah ! ".mami ta kira sunansa cikin tsananin tashin hankali har jikinta na rawa . amatukar firgice ya tsaida kwayar idanunshi dake cike da ruwan hawaye akanta qirjinsa na wani irin dokawa da sauri dan bai ji motsin shigowarta ba sai sautin muryarta wani irin zazzafan numfashi ya sauke yana sake maida kanshi sama tare da ciro hanky ya shiga d'auke hawayensa"lafiyarka kake zubar da hawaye adamcy ?ta tambayesa cikin tsananin tashin hankali dan duk abinda zai sashi zubar da hawaye baqaramin abu bane da muninsa ya wuce misali. shiru yayi ya kasa magana dan bai san me zai fad'a mata ba "kayi min magana mana adamcy dan kasa har zuciyata ta fara tsinkewa." da yatsan hannunsa ya nuna mata daidai saitin zuciyarsa dake bugawa fiyye da kaida ."sake matsoshi tayi sosai tana cewa "meke damunka "?"zuciyata sweet.." yana kai wa nan yayi shiru ya kasa cigaba da maganar idanunshi na sake cikowa da ruwan hawaye"me ya samu zuciyarka ?" ta sake tambayarsa hankalinta na qara tashi "I don't know what's wrong with me sweetheart amman dai nasan zuciyata kullum ciwo take min"."inna lillahi wa inna ilaihi rajiun " allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta "abinda mami ta shiga furtawa kenan tana sake maimaitawa " i know something is wrong with my heart wallahi sweetheart akwai ciwo mai zafi acikin zuciyata wanda zai iya kasheni nan kusa .." nan da nan fuskar mami ta qara sauyawa hankalinta a matukar tashe tace "ka dinga sausautawa kanka adamcy da yawon tunani ,ka dinga addua akan duk abinda ya dameka addua tana canzawa bawa qaddararsa kuma tana saka natsuwa acikin zuciyar bawa "numfashi ya sauke da karfi yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ,magana yake son yi amman zafin da zuciyarsa keyi ya hana shi cewa uffan "kasamu natsuwa adamcy ka dinga furta wannan adduar zaka samu natsuwa da sausauci a wajen Allah zai yaye maka dukkanin damuwarka "allahumma rahmataka arjun fala takilni ila nafsiy d'arfata'ai wa aslihli shahni kullahu la ila a illa anta ahankali ya sauke idanuwanshi ya tsura ma mami kawai yana kallonta cikin yanayi na tsanani damuwa "ka sani idan wani abu ya sameka nice farkon wacce zata fara shiga damuwa ga kuma d'an cikin jikin maryam wanda bamu san abinda zata haifa ba karka bari muyi maraicinka. adamcy kasan yadda nake sonka idan na rasaka zan shiga damuwa a kullum adduata na mutu na barka a duniya ba ka mutu ka barni ba tunda ta fara magana bai ce mata uffan ba sai ma ciro wayarsa da yayi ya soma neman layin likitansa muryarsa ce ta katse mami daga maganar da take masa ahankali yake magana tamkar mara lafiya "doctor kazo ka dubani please ".daga haka bai sake cewa komai ba ya katse kiran d'akin yayi tsit tamkar babu mutane acikinsa ." Ahankali ya soma