← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 105

Sashe 62

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yayi albarka . yana zaune a falo yana kallon labarai suka fito tare da maryam suka hau sama har kusan karfe shadaya saura suna hira . cikin wani irin yanayi ATA ya shigo d'akin maryam wanda ranar ne karo na biyu daya shiga dakin ya tsaya yana kallon mami wacce fuskata ke kwance da annurin farinciki tamkar mai koyan magana ya bude bakinsa yana wa mami sallama "Sweetheart ni zan shiga na kwanta sai da safe ya soma taku cikin isa da kasaita don barin dakin, cikin sanyi murya mami ta kira sunanshi adamcy !d'an tsayawa yayi tare da juyowa suna fuskarta juna da mami idanunta ta xuba mishi kawai Tana kallonsa tare nazarinsa ganin yadda gabadaya yanayinsa ya sake sauyawa cikin dan kankanin lokaci meke damunka naga yanayinka haka ?"babu komai sweetheart "hakika mami tafi kowa sanin koshi waye ta fannin halayyarsa da abinda ke tattare dashi bata rai mami tayi tare da ajiye wayar hannunta "meke damunka ?dan qaramin tsaki yaja "kaina Ke dan min ciwo shiyasa nake son na kwanta da wuri tunda taji haka bata sake cewa komai ba dai ina da sabo ta rigada tasa ba da rashin son hayaniyarsa daman shi mutun ne ba mai san hayaniya ba ballanantana gashi yau tasashi magana "allah ya tashemu lafiya ta fad'a adaidai lokacin daya kusan fita daga dakin "kai tsaye bedroom dinsa ya wuce ,yasoma cire kayan jikinsa yaja towel ya daura Tare da shigewa bathroom ya sakarwa jikinsa shower byn ya gama wanka ya dauro alwala yana fitowa bai wani tsaya shafa mai ba ya bude wordrob dinsa sai kamshi turaren ne ke tashi a gurin , ahankali yasa hannu ya zaro jallabiya milk colour ya zira a jikinsa ba qaramin kyau ta maisa ba ya qarasa inda daddumar salla take ya dauka ya shimfida shafi I da wutiri ya gabatar sannan yayi addua ya mike batare daya nade daddumar ba ya zare Jallabiyar jikinsa yayi fillinging daita ya sanya vest da boxcer ya canza wutar dakin zuwa mara haske ya d auki remut ya qara karfin ac sannan ya fad'a Kan bed dinsa ya lullube jikinsa da bargo mai taushi ." Bangaren mami kuwa har karfe shabiyu ta buga suna tare da maryam wacce bacci ya soma daukarta kasa kasa ta soma kiran sunanta "maryam ki tashi kije dakin mijinki mana kema fa na fahimci baki kulawa dashi kamar yadda nake zato maryam ta mike ta zauna tana duban mami da fuskarta da d an mamaki ,sosai mami ta shiga mata fada tare da bata shawarar hanyoyin da zatabi gurin shawo kan mijinta cikin sauki , sosai jikin maryam yayi sanyi likis ita kanta tasan" inda mami bata kasance yar,uwa,ce ga mahaifinta ba ,hakika bazata dinga damuwa akan damuwarta ba kullum burinta ta gansu suna zaman lafiya tare da nusar daita yadda zata sake mallakarsa a tafin hannuta cikin ruwan sanyi batare da biye biye ko wani abu ba, hakika mami dabance acikin mutane km zuciyarta may kyau ce ba kmr irin ta mahaifiyarta ba km gashi Allah yayi ta may tsananin zumunci ce mami takarasa zanceta " da maza tashi ki sake shirya kanki kije ki kula da mijinki "km cire wannan tsoron nasa da nake hangowa acikin kwayar idanuki da kyar maryam ta samu ta mike tana may dagawa Mami kai alamun taji Gaban mirrow dinta ta qarasa ta feshe ilahirin jikinta da turaruka masu sanyi kamshi sanna ta dauki hijab ta daura a saman rigar baccin dake jikinta ta fito zuwa dakinsa sai datayi addua sannna ta tura kofar dakin ta shiga ."acikin hasken da bai gama haskaka dakin ba ta hangosa kwance cikin bargo ahankali ta dinga daga kafafunta dan kar mostinta ya tayar dashi ta dan tsaya gabansa tana kallon kyakkwar fuskarsa ahankali yake sauke numfashi inda tasan mami zata bukaci tazo dakinsa data zuba masa magani acikin coffe ya sha ta samu natsuwar kwana tare dashi cikin salama ta zare hijab dinta ta ajiye bayansa ta zagayo ta hau saman gadon ta dan yaye bangon dake lullube dashi ta kwanta bayan ta cire hijab din jikinta bai motsa ba hakan yasa tayi tunanin baccinsa yayi nisa ta sake matsosa tana shakar kamshi jikinsa da kamshin turarensa. jikinta daya hadu danashi yaji kamar an ta ba shi da wuta yayinda ita kuma sauyin yanayi taji a ilahirin jikinta kusan awa daya da wani abu suna kwance haka yadda bata runtsa ba haka shima bai runtsa ba . Zuciyarta ce ta bata kwarin gwiwar kai hannunta jikinsa ta soma shafasa tana aika masa wasanni stil bai motsa ba kuma bai ji komai ba sai tarin bakinciki mamaki da karfin halinta ya kamata shi Kmr ya tashi ya rufeta da duka amman ya kyaleta saboda darajan sweetheart dake gidan ganin bai motsa ba yasa maryam tayo kasa da hannunta daidai kasan marasa nan ne fa yaji bazai iya barin ta cigaba da iskancinta data tsiro dashi ba a yau ,zaraf ya damke tsintsiyar hannunta tare da jijiyo ya zabura ya mike zaune tamkar wani zaki mikewa tayi zaune Kmr yadda yake ,kallon da yake mata yasa qirjinta dokawa da sauri sauri saboda kallon ne mai tattare da tsana da gargadi ."a matuqar tsawace yace "uban wa yace ki shi go min daki ?kinga nayi kama da wanda zaki ta'ba? Ko jikina saanki ne ?yayi mata tmbyr ajere nan da nan yasa maryam ta gigice "tmbyarki naki "tayi shiru wallahi komai zaki min bazan ta'ba jin komai ba saboda bana kallonki amatsayin mace kmar yadda nasha fad a miki idan kika sake gangancin kai hannunki jikina wallahi sai cakawa zuciyarki wuka . kallonsa tayi da bayananen tsoro wannan ya zama karo na qarshe da zaki shigo min daki domin har abada bazaki zamo abokiyar rayuwata ba jikina ma bazaki samu ba bare zuciyata fuskarsa babu annuri ya nuna mata kofar fita oya get out from this room kafin na miki mugun bugu cike da sanyi jiki ta rarumo hijab dinta ta soma qoqarin jirawa ajikinta sai dai ta kasa fita daga dakin tana tunanin me zata koma tacewa mami ganin taki fita ya sauko ya kamo hanuta bai tsaya wata wata ba ya soma janta ya bud'e kofar tare da hankadata waje da sauri ta tokare hannunta da bango batayi mamaki ba dan tasan zai iya aikata fiyye da haka ." Makalewa tayi a bangon koridor hawaye masu dumi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta ta goge shi kuwa rufo kofarsa yayi ya murda key a galabaice ya fad'a bed dinsa ya runtse idanushi ya sake jan laulausar bargo ya lullube jikinsa maryam kuwa natsuwarta take qoqarin daidaitawa amman ta kasa dan hawayenta ya gagara tsayawa bata koma dakinta ba sai wajen karfe daya wanda a tunaninta zuwa wannna lokacin mami tayi bacci sannan ta nufi dakinta tana danne sheshekar kukanta Koda tashiga dakin mami na kwance , maryam ta haye saman gado ta kwanta lamo abayan mami tare da kamkame jikinta wani irin kewa da son mijinta ce ke damunta amman shi babu halittar daya tsana kamarta , kuka take son yi dan rage damuwarta amman bbu dama domin damuwarta zata iya haifawar da mami damuwa , a dalilinta mami zata iya muzgunawa yaya Adam , ita km abinda bazata so ba kenan, batason abinda zai sake hassalashi akanta ta kai hannunta ta dafe daidai satin zuciyarta dake mata ciwo bayan Kmr minti goma mami ta tashi zaune ta dubeta tana mata kallon tsab batare da tayi magana ba sannna ta sauko ta shiga bayi ta dauro alwala ta fara gabatar da nafilflii . " juyi tayi tare da sake kamkame jikinta yanzu ita yaya zatayi da rayuwarta ? mayye zatayi ? ga soyayyarsa ga tsananin sha,awarsa duk sun taru sun hade mata ,take zuciyarta ta bata amsa da kima kama kanki da rashin hakurinki dan muddin kikayi kuskure sake zuwa inda yake zai iya kasheki tunda har ya rantse ya allah ka taimakeni kasa na samu ciki a karon mu na biyu dashi yanzu ta shiryawa kowani rigima zaiyi idan ciki ya bayyana ajikinta a boye take goge hawayen dake bin kuncinta ,har mami tagama tayi laziminta da sauran addu'o,inta .bacci bai yi nasarar daukar maryam ba kuka take qasa qasa . Tana jin motsin mikewar mami ta shanye kukanta Tare da goge hawayen idanunta amman hakan bai hana mami gane wani abu ba ,daidai inda fuskarta take tazo ta zauna tare da kamo hannuta ,"me kike tunanin maryam ko kuma nace me ya dawo dake dakin nan har ya hanaki bacci ? Kafin maryam tace wani abu mami ta km jiho mata wata tmbyr sai ma naga kmr kuka kika yi ko? Maryam ta Mike zaune suna fuskartan juna da mami ,yayinda hawayen dake makale a idanunta suka yi nasarar zubowa...."mayye km abin kuka tmbyrki kawai nayi fa? sai km ki kama min kuka. wani abu adamcy yayi miki ?ahankali ta girgirwa mami kanta ki fad a min idan wani abu yayi miki da kyar maryam ta iya bude bakinta ..." ammi me yasa yaya Adam ya tsaneni haka ?kullum so nake naga na rayu dashi har qarshen rayuwa amman shi kullum burinsa ya ruguza rayuwar gidan aurenmu da ni kaina bansan yadda zanyi abubuwa su dawo min daidai tamkar kowasu maurata ". basan abinda na aikata masa ba da kullum yake son ganina cikin qaqa na kanyi .Ida abubuwa da yake min suka cigaba da faruwa bana tunanin zuciyar dake kirjina zata cigaba da bugawa , mami tambayar min shi laifin me nayi masa ? wallahi ni ina qaunar zama dashi muddin raina . mami ta rungumeta ajikinta tana mai tausaya mata "kukan ya isa haka babu abinda kika masa halinsa ne haka halin bakar zuciya irin tasa yana damuna ni kaina na gaji da halinsa ,amman matsawar Ina raye ba zaki taba kasancewa cikin bakinciki ba , bugu da qari har yanzu kina da sauran damar rabuwa dashi dan bazan cigaba da baki hakuri ki cigaba da zama dashi ba dan duk wani abinda zaa masa anyi masa idan dai ba rayuwarmu yake nema ba . Mmn sudais MAR'ADAMS
Chapter 62 · 0% Book details