Sashe 15
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da dadi ,ka duba kaga yadda ya bari aka wuce da maryam ita kadai babu wata kulawarsa sannan kaji irin maganar daya fad'a maka sam sam maganarsa babu da'a acikinta, baya respting din mace , ka sani na sani kowa hakuri yake da abinda yazo hannunsa ,shi mai yasa bazai yi hakuri ba ? bana son nana hauwa'u nuzlah nake so amman hk na hakura daita nuzla dake sauronsa ta sauke numfashi aranta tace "sai ma ka rabu daita yadda danuwanta ya nuna rashin qauna gareni itama sai na bari ta d ani qiyayya mai zafi daga gareka dan babu abinda zai hanani shiga gidan "kaga mu bar maganar mayi daga baya ."inji cewar salim. Direbansa cike da girmamawa ya tambayesa inda suka nufa "muryarsa can kasan makoshi yace "mb ! dan haka kira motar da zata fara yin gaba yayi ya sheidawa direban sannan suka sa kai motoci biyu ne a gabansu sannan motar da ata yake ciki sai mota biyu abayansu,cikin kankanin lokaci suka qaraso kan titin oduduwa road inda anan gidan mb yake ." bayan motocinsa sun shigo cikin haraban gidan sukai parking ,sai dai shiru ata ya cigaba da zama yaki fitowa sai daya d auki mintuna shabiyar sannan ya fito a natse yana shan kamshi. Mb na zaune yana kallon tashar labarai yaji sautin muryar ata yana sallama aciki ,fuskar mb cike da farinciki ya mike tsaye daga zaune da yake ya tarosa ya rungumesa ajikinsa yana cewa "kai mutumina daga ina haka ?sai daya sauke numfashi sannan yace "daga gida ! ya bashi amsa atakaice sannan ya samu waje ya zauna yana fesar da numfashi tare da runtse idanunshi ,amira dake kitchen ta fito hannunta rike da tray ta gaishesa fuskarta a sake "ango kasha kamshi ina yini ? " ta fada idanuta na kan tray din dake hannunta tana zuba hadin salad. fuakarsa a hade tmkr wanda aka fadawa sakon mutuwa ya amsa "lafiya lau madam ya gida da yaran ?"lafiya lau muke tace masa atakaice dan ta qagu ta kammala abinda take ta bar gun taje ta shirya kanta ."tana sauka daga stares din dining area din mijinta ya cigaba tambayarsa amaryarsa ." "Manta da wata amarya na dai baro su aunty sun wuce daita amman zan basu mamaki "kamar ya zaka basu mamaki ?. "bazan ta ba kwana a gidan ba, aure ne nayi ,tariya ce na basu damar sukaita ,rayuwa daita kuma bai zame min dole ba haka zata qare rayuwarta batare dani ba " haba abokina karka yi haka mana ka tausayawa yarinyar nan mana , kaga ni ba abinda ya kawoni kenan ba mb ya gyara zamansa yana dubansa a tsanake tare da cewa me ya kawoka? nazo ne akan hisham ". hisham kuma ?mai faru dashi ?yayi masa tambayar a jere cikin tsananin tashin hankali ya sauke numfashi kana ya motsa lips dinsa kadan "hisham yana son mu samu matsala dashi a natse ya cigaba da magana ya zayyano masa komai mb ya numfasa kana yace "gsky bai kyauta ba zan masa magana amman kai kuma ai bai kamata kaji ciwon abinda yayi ba tunda kaima halinka ne koma nace a wajenka ya koya,kaga yanzu lokaci yayi da zaka canza ata ya d an d ago kanshi ya tsura masa tsumammun idanunshi wallahi ka canza halinka kaga yadda yaruwarka baza taji dadin aure a gidanta ba kana cin zarafin ya yan wasu da kanen wasu amman kai baka son ayiwa naka ai kai ma kasan hakan ba abu ne mai sauki ba ,kasani duk abinda kayi sai anyi maka wannan ba gasky bane yayi maganar yana lasar lip s dinsa duk dai abinda mutun yayi akanshi zai qare ba akan wani ba mb ya bud e baki zai sake magana ata yayi saurin dakatar dashi ta hanyar cewa dan allah na gama da wannan maganar shi kuma hisham ka nemeshi kaja masa kunne, kuma zan kira auta matukar tana facing din matsala a gidansa sai kunji tsoron abinda zai biyo baya dan wallahi sai na kashe auren gabad aya. idan kuma tana son mijinta fa ? shiru ata yayi batare da ya ce komai ba yana nazarin maganar mb ka tsaya ka natsu kayi tunani mai kyau domin kashe auren ba shine mafuta ba , ka barta tayi zaman aurenta lafiya , babu ruwanka da matsalar gidanta idan da wata matsala nayi imani nana hauwa u zata kawo karshensa ,ina baka shawara ka cire hannunka karka zo kayi abinda zaa zo ana kuka da kai shiru ata yayi ya kasa cewa komai yana nazarin maganarsa har sanda amira ta sake fitowa ta cika masu table din gabansu da kayan abinci iri iri ta juya zuwa d akinta ." "Abokina ..!"rin wannan liyafa haka,gsky ina da rabo acikin abincin gidanka yau shyasa haushina ya kawo ni gidanka kasan bayan mun shigo haraban gidan nan naji kamar bazan shigo ba"yanzu dai kanka ake ji sarkin kwad'ayi,ga abinci nan kayi sarving din kanka ata yace " no bari amira ta fito "ta fito tai maka me ? yayi masa tmbyr yana hararasa hankali kwance ata yace ta zuba min mana ai kuwa baka isa ba sai dai idan bazaka ci ba ,amman matata ni kad'ai zata sarving ,idan kuma lallai ka matsu da cin abinci kaje ga matarka . "uhm !ata ya furta daga kasan makoshinsa sannan yace "banson iskanci fa mb matarka ko matarmu ? mb yayi murmushi yana dubansa adaidai lokacin da amira ta sake fitowa yace "darling zubawa wannan gogaggen dan iskan abinci yaci ba dan halinsa ba murmushi tayi ta zuba masu tare ."sai da ya gama shan qamshinsa kafin ya soma cin abinci."mb ya gyara zama yace gsky abokina karka cuci kanka wallahi kaje wajen matarka ko babu komai ai ka rage mara ata najinsa amman yayi masa banza yayi tmkr ba dashi yake mgn ba ya cigaba da kai abinci bakinsa . mb ya ajiye spoon din hanunsa ya zuba masa ido yana kallonsa wallahi ata ka canza rayuwa me ya faru da rayuwata da zan canza ?abubuwa daya kuwa sun faru da rayuwarka taya da ranka da lafiyarka ga lafiyayyar mata allah ya baka amman ka tsaya cutar kanka . kowa da yadda yake rayuwarsa ni yadda nake rayuwata empty yayi min . ata ya fad a batare daya jallesa ba shiru mb yayi yana cigaba da kallonsa kafin daga bisani yace kai ko baka da lafiya ne? ata ya d ago a natse yana dubansa mgnrsa ta bashi dariya sai dai yaki yi dan ba aladarsa bace yin dariya . Ka tsareni da ido ko kuma maganar mami ce ta tabbata yarinyar mafarkinka aljana ce ? uhm mb kenan babu wani mb kenan ka fito ka fad a min gsky gabanka na tashi ko kuwa zero ne kai ?ata ya dauke kanshi yana cewa babban tashi ma kuwa dan a halin da nake ciki sannan na samu irin kalar yarinyar da nake so to wallahi sai ahankali dan zataji jiki mb ya kwashe da wata dariya yana buga hannunwansa kasan wani abu abokina ?ata ya kai abinci bakinsa yana dan kallonsa alamun yana jinsa "daman irin ku ne idan suka shiga hannun mace sai allah ,sai yadda akayi daku ba soyayya ba hatta gaban mace sai ku lashe baku sani ba abincin bakinsa ya tofar da sauri bayan ya dalla masa katuwar harara kamar zai cinye shi ". allah ya isa tsakaninmu da kai mb wannan ai cin fuska ne,ko zan so mace sai na kama wani lashe gabanta gabanta fa? ni adamcy ,i think ka fara hauka ,kai allah ma ya isa tsakanina da kai ya sake maimaitawa yana ajiye spoon din hannunsa tare da ture plet din abinci , alokacin da sugura ta fito da mugun gudu daga d akinsu mansor na biye daita tana ganin ata ta nufo wajensa ta fad'a jikinsa tana kiran "uncle !"kaga yaya mansor ko ." Ya rungume tsam ajikinsa yana kallon mansor dake haki " haba yaya mansor mai baby nah ta maka ?textbook din assignment dina ta yaga ya fad a Kmr zai yi kuka ata ya kalleta "baby da gaske kin aikata haka ?tayi shiru tana sake lafewa ajikinsa "ai tunda kaji tayi shiru ta aikata ne dan barna a cikin yarinyar nan baa magana babu abinda zata gani bata 'bata ba inji cewar mb tare da kai hannu zai zuba mata rankwashi aka ata ya tare hannunsa "yana cewa haba meye haka kuma ?wannnan hannun naka koni ka zubawa shi ai sai na tashi aiki bare ita ,mb yayi murmushi kawai ata ya kalli mansoor yace kayi hakuri je ka dauko textbook din na gani ya juya da sauri ya shiga daki ." ATA ya cigaba da shafa bayan sugura "a duk lokacin dana kalli baby sugura sai naga kamar princess dina tana yarinya "ko itace? Mb ya fad'a yana murmushi ata ya had'e rai sannan yace" banason iskanci yau fa naga wasu abubuwa kake min "babu wasu abubuwa idan itace shikenan sai ka cigaba da jira zan baka aurenta ."ATA bai qara cewa komai ba ya cigaba da shafa bayanta dan ya fahimci yau iskanci abokinsa yake ji ." Bangaren maryam kuwa tana can zaune cikin tsananin tashin hankali gefe guda kuma jifa jifa tana duba agogo awani suka dinga zuwa suna wucewa ahankali ta mike ta shiga bathroom din dake manne acikin dakin tayi alwala ta fito tayi sallah magrib ,haka da ishai tayi ta sake mikewa tayi sallah duk abinda take gabanta banda faduwa babu abinda yake . "nan da wasu 'yan shekaru zamu fara ajiye surukai ,ya dai kamata kasan ciwon kanka Ata ka rungume aurenka , ko bazaka yi dan kowa ba kayi dan kanka dan rayuwar nan babu tabbas " karka mutu baka ajiye kowa ba muryarsa a matukar sanyaye ya motsa labbansa wallahi ina matukar son haihuwa amman bada wannan yaron ba ,bana sonta mb kayi hakuri ata ka daina fad ar haka dan Allah kayi addua kawai shikenan zan fad'awa sweetheart tayi min addu tunda addaur iyaye babu shamaki idan alkhairi ce arayuwarta allah yasa min sonta ko kad'an ne a zuciyata amman wallahi mb I don't know why ban ta'ba jin son yarinyar nan ba , kullum na ganta kamar na kasheta