Sashe 83
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
masa mgn idan ya amince sai kuje tare . Bayan kwanaki uku Tsaye yaya sadam yake a d akinsa muryarsa can qasa qasa yana waya da nadiya haba nadiya nasani nasan ban miki adalci ba amman kema Kinsan yadda nake mutuwar sonki ,soyayyar shekaru biyar fa ni kad ai nasan me nake ji ajikina tabbas nasan laifina ne da ban shigo da maganarki da wuri ba har aka zartar da wannan hukunci ,No bazan iya cewa mahaifiyata haka ba . zan dai san abun yi ki kwantar min da hankalinki ki saurareni at anytime .a natse ya fito cikin jallabiya ruwan qasa kawai yaga maryama zaune ita kad ai a falon . sai daya zauna sannan suka kalli juna shi da maryam gano yanayin maryama kamar tana cikin damuwa ya matsota sosai har suna iya shakar numfashi juna dan a tunaninsa ko taji wayarsa ne ahankali ya kamo yatsun hannunta wanda yasa taji wani irin zirrr a sansar jikinta nan da nan tayi qoqarin zare hannunta bai damu ba yace lafiya na ganki haka ?daman magana nake son muyi ina jikin me zaki fad a min ? amm amm daman akan wani aiki ne daaka kirani nace na fad a maka nan dai tayi masa bayanin komai ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta kinji abinda naji kuwa ?wani irin aiki ne har ogun state kuma a ranar daurin aurenmu ?nan da nan jikin maryama ya kama rawa kayi hakuri bansan mgr zata bata maka rai ba na hak ura ba sai naje ba na cigaba da aikina anan daman ba wai zasu d auke bane aiki ne na lokaci zuwa lokaci kuma ba aikin kwana bane amman kayi hakuri karkayi fushi dani ta qarasa mgnr muryarta cike da rauni . ya kalleta cike da tausayinta sakamakon yadda take magana cikin sanyin murya da tsoro ,ita kanta a yadda take maganar tana jin babu dadi har cikin ranta shikenan ki kwantar da hankalinki yanzu me kike ganin zamuyi ? ya tambayeta cikin sanyin rai wai idan ka amince sai muje tare da kai ,idan kuma baka amince ba wallahi babu komai na hakura allah ya zaba min abinda yafi zama alkhairi murmushi ya sakar mata yace shikenan karki damu amaryata zamuje tare ai ni yanzu duk abinda kike so ina so ko bangon duniya kika ce zamuje tare allah ya nuna mana ranar nan da nan murmushi ya bayyana a fuskarta amman naji dadin amincewarka wallahi baka ta ba sakani farinciki irin na yau ba na gode sosai allah ya jikan iyayenmu Allah yasa suna aljanna Allah ya saka maka da alkhairi Allah yaja da kwanan ummah ,Allah ya bamu zaman lafiya a arayuwar aurenmu Ameen Ameen ya Allah Allah ya nuna min kin haifa min yara masu yawa tasa hannu tana rufe fuskarta nan suka cigaba hirarsu. Ranar lahadi 14 ga watan October shekara ta dubu biyu da bakwai aka daura auren maryama da yayanta sadam .ana gama daurin aure suka fara shirin tafiya ogun state wanda kusan yaya sadam ne yayita matsa mata ta d auko kayan aikinta tare suka shiga wajen ummah lokacin tana tare da yan uwanta dana mijinta tayi masu fatan alkhairi fuskarta dauke da farinciki maryama ta zama mallakinta gabdaya lokacin da zasu wuce aunty hassna tace yanzu dan lalacewa aunty har da murna kike tun baaje koina ba an mallake miki d cak maryama ta tsaya cike da sanyin jiki me zanyi hassana matarsa ce kuma ya amince tunda ya amince meye nawa aciki ?kunga kuyi maza ku kama hanya Allah ya tsare min ku suka sa kai zasu fice har sun kai bakin kofa umma tace sadam ya juyo daga inda yake ka kular min da maryama da kyau ,Allah ya tsare hanya to ni ummah bazakice ta kular miki dani ba ?tayi murmushi shikenan maryama ki kular min dashi Allah yayi maku albarka suka ce ameen suka fito suka shiga mota suka d auki hanyar ogun . Cikin sauri sauri ATA ya fito daga dayan bedroom dinsa cikin wasu had den kanana kaya bakake ajikinsa ,ya shiga dayan dakinsa wanda kusan abubuwansa masu mahimanci anan suke, yadda jikinsa ke fitar da kashin turarensa reed akoda yaushe haka dakin Ke dauke da kamshin turensa, cikin sauri ya dauki farin glass dinsa ya manna a kwayar idanunshi sannan ya qaraso ya dauki agogo baki ya daura a tsintsiyar hannunsa ya bude bedside ya dauki wallet dinsa ya tura cikin ajihunsa ya daura facing cup yayi mugun kyua ya fito sanyayyen kamshin turarensa na binsa cikin sauri yake taka step cikin . a zaune ya iske mami tana waya ya d an tsaya yana kallonta dan ga dukkanin alamun da wannan yarinyar take waya gyaran murya yayi yana sham kamshi ta waigo tana dubansa ina zuwa kuma ? wani aiki !ya bata amsa atakaice yana had e gira sama data kasa dan kar ma tayi masa mgnr mrym naga yau weekend ce ?eh ogun state zani zan iya dawowa a yau watakilla kuma sai gobe dan aikin nada matukar mahimanci . yana gama fad ar haka ya nufi kofar fita . To adamcy mami fatan nasara Mmn sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 25 Tafiyar awanni hud'u ta kawosu maryama ma'aikatan ATA dake jahar ogun state yaya sadam yayi parking din motarsa acikin haraban ma'aikatan sannan suka fito atare yana gyara zaman farar shaddar jikinsa yayinda maryama ke qoqarin neman layin mr segun kira d'aya mr segun ya d'aga sukai magana na second biyu sannan ta fuskanci yaya sadam fuskarta kwance da annurin farinciki mara iyaka tace "kad'an yi hakuri yanzu za'a yi mana iso zuwa ciki " yaya sadam ya gyad'a mata kai kawai alamun babu komai yana sakar mata tsadaddaden murmushinsa ,suka tsaya suna magana kasa kasa kafin ayi masu iso .wani matashin saurayi ne ya sauko sanye da bakaken kaya ya shigar dasu ciki . a wani dogo office aka shigar dasu wanda gabad'aya nsa glass ne dan ana iya hango duk wanda yake ciki ,basu d'auki cikakken mintuna goma ba mr segun ya shigo yana tmbyr saurayin daya shigo da su maryama "niyi ina bakuwar daka shigo daita ? "sir itace a gabanka zaune mr segun ya d'an ware idanunshi akan maryama dake zaune yana mata barka da zuwa yana mai sake masu iso zuwa wani office din dabam wanda daga shi sai wanda ATA yake cikin zaune zaman jiran qarasowarta "kusa da maryama yaya sadam ya samu waje ya zauna kamar zai mata numfashi "madam ya hanya ?" mr segun ya tambayeta cike da kulawa yana kallonta "alhamd sir tunda gamu mun samu mun qaraso lfy amman fa da kyar dan hanyar nan taku bata da kyau tafiyar da ya kamata ace one to two hour's ne ya kawomu shine ya d'aukemu har four hours amman alhamdulillah "wannan gsky ne mutane na yawon complain akan hanyar nan tamu amman dai alhamd tunda kun qaraso lafiya tun mai gida bai gaji da zaman jiranki ba dan awaninsa biyu da qarasowa bari nasa akawo maku abun sha, idan kin gama wancan office din dake kallonki zaki shiga kafin nan ma zaki same aciki "yana gama fad'ar haka ya fita da d'an sauri ya barsu zaune maryama ta zuba ma yaya sadam ido har sanda aka kawo masu abun sha ta d'auka ta tsiyaya masa a glass cup ta mika masa ." ahankali yasa hannu ya amsa cup din hannunta ya kur'bi kad'an yana mai lumshe idanunshi sannan ya ajiye cup din hannunsa yana dubanta a tsanake "ya naga duk kinyi wani iri ?"naji yace idan na gama na shiga ni kuma nafi son mu shiga tare da kai banason na barka kai kad'ai zaman jirana " Gajiyayyun idanunshi ya ware sosai akanta kafin ahankali ya hadiye wani abu daya tsaya masa a makoshi sannan yace "karki manta aikinki kika zo ,kuma kema Kinsan ke kad'ai zasu bukaci gani banda ni ?" duk da haka idan a son raina ne mu shiga tare "ta fad'a tana mai tsareshi da narkakkun idanunta ." suna zaune wnn saurayin da yayi masu iso shigo yana cewa "madam ki shiga ke kad'ai mai gida yake jira "ok but dan allah ko zamu iya shiga mu biyu ?cike da jin haushin maganarta yace "tare zakuyi aikin ne ?no ni kad'ai ce !to ke kad'ai ake buqatar gani aciki dan mai gida baya son hayaniya "ya qarasa maganar tare da ta'be baki sannan ya fice ya shige wani office ." hankalin maryama ya tashi matuka dan har ga allah haka nan taji bata son shiga ita kad'ai qarara damuw ta bayyana acikin kwayar idanunta da shi kad'ai yaya sadam yake iya gani har ya fahimci halin da take ciki ,ahankali yaya sadam ya tsiyaya mata drik ya miko mata ta girgiza masa kai alamun bazata sha ba ,"why ?! ya tmbyeta yana sake tsareta da idanunshi dafe goshinta tayi tana cewa "bana jin shan komai a yanzu ,tun daya ga haka yasan ko me zai yi 'bata lokacinsa kawai zai yi dan bazata kar'ba ba, dan haka ya mike tsaye suka fito tare tana gabansa yana take mata baya har suka fito dogon hanyar da zata kai su office din ATA wanda alokacin yana tsaye acikin tangamemen office dinsa ya hard'e hannuwansa duka a faffad'an qirjinsa idanunsa kyam akan maryama da yaya sadam ta cikin glass door ,har ta fara taku domin qarasowa zuwa inda office dinsa yake yaga ta tsaya ta koma baya kad'an tana magana da wani da bai san ko waye ba ,sai dai idanuwanta yana kansa ,kwakwa luwarta na hasko mata fuskarsa daga nesa kamar tasan fuskar yayinda shi din ma kallonta yake cikin shigarta ta mutunci kamar ranar farko daya fara d'aura kwayar idanunshi akanta ."doguwar riga ce sanye ajikinta har qasa mai dogon hannu da qaramin hijab dinta mai zip a gaba,sai nikaf kalar hijab din da take sanye dashi wanda iya kwayar idanunta kad'ai ake iya gani