← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 105

Sashe 69

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

."shadaya da rabi daidai ata ya sauko ya fita daga gidan kuma alokacin maryam ta gama komai har da miya suna tsaye suna hira da nana hauwa u inda nana hauwa u take fad a mata ciki gareta wani ihu mrym tayi ta rungumeta gsky sister am very happy for you Allah ya hada miki komai da komai kema sister kiyi ahankali fa dan baki sani ba ko ciki gareki mrym ta zaro ido waje sister ina jin tsoron abinda zai biyo baya ina nufin an samu a daren jiya allah yasa ai da ni kad ai nasan irin farinciki da zanyi dan ko baya so zan rike abina bare ma da gudu zai kwace suka dariya basu gama rufe bakinsu ba kawai suka jiyo sautin muryar ATA cikin hargagi da tashin hankali . "ku yanzu daku zaa had'a baki ayi min haka "? a she yadda nake qaunarku ku ba haka kuke qaunata ba ?"daman na dade dasanin haka ,na gode allah ya saka da alkhairi ku tashi ku bar min gidana gabandayanku bana son ganin fuskokinku ya qarasa maganar adaidai lokacin da su maryam suka fito rike da hannun juna a bakin kitchen suka ja suka tsaya jikin maryam banda rawa babu abinda yake ".dan kwata kwata bata son ganinsa cikin tashin hankali Ya kalli inda maryam suke tsaye ya nunata da yatsan hannunsa kema bazan qara zama dake ba ki tattara duk abinda kikasan naki ne acikin gidan nan ki bar min gidana na sake ki saki u cike da tashin hankali aunty shahida tayi wani Irin qarasowa inda yake ta rufe masa baki tana girgiza masa kai tare da nuna masa yatsanta d aya alamun d aya zai furta maryam kuwa tun kafin ta gama ji ta d aura hannuwanta duka bisa kanta tare da shiga wani sabon tashi hankali"wani laifi suka masa haka ?ta jefawa wankakkiyar kwakwaluwarta tambayar ." inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda nana hauwa'u ta shiga furtawa tana maimatawa wanda yasa maryam ta kama tana yi bakinta na rawa wannan wace irin maseefa ce inji cewar aunty khadija dan gabadayansu babu wanda jikinsa bai d auki rawa ba maryam kuwa tashin hankalin da take ciki ya hanata kwakwaran motsi a inda take tsaye magana take son yi koda kalmar hakuri ce garesa amman ta qasa furta komai numfashi kawai take ja ta bakinta tana fitarwa dashi da kyar . alamarin ATA ya girmi tunanin yan'uwansa suna kallonsa ya buga ma aunty shahida razananniyar tsawa bayan ya cire hannunta cikin tsananin tashin hankali da fad uwar gaba take rokonsa "Adam ba a saki cikin fushi idan kuma ya zama dole sai kayi kayi d aya wani mugun kallo yayi mata yana mai janye jikinsa daga nata ya sake maida kallonsa ga maryam tsayuwar me kike yiwa mutane maza ki fara qoqarin bar min gidana ,kuma haka banason ganin kowacce acikinku wallahi na tsaneku sannan na cire kaina acikinku aunty khadija ma tayi karfin halin qarasowa inda yake yayi saurin ja baya "bana son jin komai kawai kuje tunda kunfi son farincikin yarinyar nan akaina shekara nawa ina fama da zazzafar qaddara amman acikinku ko sau d'aya babu wacce ta zaunar dani ta fahimceni amman dan rashin Imani irin naku daku aka had'a baki na kusanci wannan guntuwar yarinyar wallahi kun cuceni . ai tun daga zuwa d auko shahida ya kamata ace na fahimci akwai wani abu a qasa amman babu komai kuje na gode . mamaki da matsanancin tsoro suka kama maryam daman akan ya kusanceta ne ya zartar da wannan hukuncin akanta? ganin maryam bata da niyyar bar masa gidansa ya qarasa inda take ya kamo hannunta yana ja bata iya ce masa komai ba sai ma binsa da take har ya kai bakin kofa ya bud'e tare da hanka d ata waje ya maida kofar ya rufe da karfi wasu hawaye masu zafi da ciwo suka zubo mata tasa bayan hannunta tana gogewa wasu na sake biyowa kuncinta ."ATA na gama juyo idanunshi ya sauka akan mami tsaye ,cikin tsannain tashin hanakali take kallonsa muryata na rawa tace "me ka aikata haka adamcy ?yanzu sweetheart har za a had a baki dake a cutar da rayuwata ?ban shirya yin rayuwata da wannan yarinyar ba saboda me zaa min karya da ciwonki ?numfashi mami ta sauke tana kallonsa "dan haka na saketa saki uku dan bazan qara zama daita ba gabad aya babu wanda bai furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ba har mami dan kam sai data dafe qirjinta dan wani luguden bugu yayi . nana hauwa'u ta qaraso inda yake cikin rud ewa da rawar jiki ta riko hannunsa ya fixge "har ke ban cireki acikinsu ba kuyi rayuwarku nayi tawa tunda bakwa sona nima na hakura daku har abada zabiba ta bud'e baki ta soma magana cike da in ina "ni ..ni dai yaya wallahi banda ni dan ba dani aka shirya komai ba hasalima yau din nan nasan komai aunty kahdija ta ta'bata alamun tayi shiru amman ta zame jikinta "dan allah yaya karka mana haka wallahi muna tsananin sonka muna qaunarka ta durkushe kasa tana jan gwiwowinta zuwa garesa ya tsaidaita ya juya ya haye sama a matukar fusace yake taka step ."wani irin naunayen ajiyar zuciya suka sauke atare "mami ta kallesu daya bayan tace "garin yaya kuka yi wannan kuskuren ?yaakayi kuka bari yasan komai ? tayi masu tambayar ajere cikin tsananin tashin hankali,gbdynsu sukai shiru dan basu da bakin magana ta sake sauke ajiyar zuciya "ina maryam take ? tana waje ! nana hauwa u ta bata amsa cikin kuka kai tsaye kofar mami ta nufa ta bude inda taci karo da maryam durkushe tana zubar da hawayen mami ta kai hannunta ta d'ago ta ta rungumeta ajikinta tana shafa bayanta . jinta ajikin mami yasa ta sake fashe da wani sabon kuka mai ta ba zuciya " dan allah mami ki fad awa yaya bani da masaniya akan komai ,kuma allah danasan shiri ne ciwonki da bazan ta'ba amincewa ba gara na cigaba da rayuwata haka dashi "kukan ya isa haka abinda ya faru ya wuce ba kuma zai gogu ba ta zareta ajikinta suka koma parlour'n ta zaunar daita akan kujera sannna ta zauna a gefenta tana rarrashinta "yanzu mami ya zaayi kenan ? "ku da kuka tona asirin komai sai kusan yadda zakuyi dan babu ruwana ,ban da son jawa mutane tashin hankali meye abun baje hira a gidansa alhalin kusan halinsa? Kiyi hakuri mami ki yafe mana inji cewar aunty shahida "mami dan allah kije ki shawo kansa ya janye sakin ya maidashi d aya Ke kadai ce zaki iya shawo Kan yaya nana hauwa u ta fad'a tana share hawayenta "da sauri maryam ta kalli inda take zaune sister saki ukun yayi min kenan ?nana hauwa u ta gyad a mata kai alamun eh!ahankali ta runtse idanunta gam tana jin wani irin rad i da ciwo acikin zuciyarta wallahi tayi wa kanta alkawari muddin ba ita ce acikin gidansa ba babu wacce zata zauna cikinsa cikin jin dadi, duk inda ake zuwa dan biyan buqata zata domin ta hanashi jin dadin rayuwa kuma duk runtsi sai ta dawo gidan zaman lafiyarsa ya janye sakin kamar yadda sister ta bada shawara bata gama fita daga wannan tashin hankalin ba taji muryar aunty zabiba ta karad e parlour gsky mami ya kamata mu ajiye son rai a tsaya a duba lamarin yaya shima tunda ya nuna baya son aurenta kar a wani maidashi a hakura kawai allah ya hada kowa da abinda yafi zama alkhairi . da sauri maryam ta bud e idanunta ta kalli inda take zaune qirjinta na wani irin bugawa "bayan ya gama maidaita qaramar bazawara zaki fad'i haka ? aunty khadija ta fad'a a fusace "to meye amfanin wannna auren tun kafin ayisa yace bai so ?tunda akayi auren nan ku fad'a min rana daya wanda muke da kwanciyar hankali ? kullum zuciyarmu cikin fargaba take, yin aure halal ne haka barinsa halal ne idan ma zai gare rayuwarsa haka abarshi mana matsawar bazai dinga biye biyan mata ba , tunda suka fara magana a tsakaninsu mami bata ce uffan ba har Qarfe uku ATA bai sauko ba gabdaya cikin damuwa da tashin hankali suke most especially maryam wacce har wani rama tayi nana hauwa u dake kusa da maryam ta dinga kwantar mata da hankali sister karki d aga hankalinki yaya zai janye sakin da yayi miki yanzu fa kin rigada kin zama jinin jikinsa jininsa gauraye yake da naki wata killa ma akwai ajiyarsa ajikinki shiru kawai tayi dan bakinta bazai iya furta komai ba dan hatta miyon bakinta ya qafe idan tayi qoqarin had iye wa jinsa take tmkr mad aci ." Da misalin karfe biyar ne mami ta mike ta haura sama ta shiga dakin ATA ta iske shi zaune akan kujera kwaya d'aya dake dakin yayi baya da kujerar yana kallon saman d akin ganin shigowarta ya runtse idanunshi gam .da sanyin jiki mami take qarasowa inda yake stood ta janyo ta zauna gabansa ta zuba masa ido tana kallonsa tana nazarinsa dakin yayi shiru tamkar babu kowa aciki har tsawon minti goma mami na zaune agabansa yadda batayi magana ba haka bai bud e idanunshi ba ta kira sunansa "adamcy nah! shiru ne ya sake biyowa baya ta kai hannunta ta kamo hannunsa ta kai bakinta tana sheshekan kuka saukar hawayenta yaji a hannunsa ya d an bud'e idanunshi akanta tabbas hawaye ya gani yana sharara akan kuncin mahaifiyarsa abinda ya tsani gani kenan naunayen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske sannan ya kai dayan hannunsa yana d auke mata hawayen fuskarta dake kwarara sannan ya motsa lips dinsa da kyar "why sweetheart?Bata ce masa komai ba illa cigaba da zubar da hawaye "da fatan ba Adam bane yayi sanadiyar zubar hawayen nan ?ahankali ta gyada masa kanta alamun shine. numfashi ya sauke yana son sanin dalilin kukanta "adamcy kana son saka sweetheart dinka kuka,baka jin damuwa yadda kake saka sarauiyar dad dinka kuka ?mami ta furta tana dago da idanuwanta ta zuba masa da matuqar damuwa "ina cikin damuwa adamcy !"nima acikin damuwar nake jin sautin muryarsa cikin tsanani bacin rai ya qara d
Chapter 69 · 0% Book details