← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 105

Sashe 27

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mmn sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 9 "Yusif ya d'an yi dariya kad'an sannan yace "saboda kuma kawai a garin mahaukata ake sai ku maye gurbinta? " maye gurbin maryama ko mace' yar kasar england ce maryama tafi gabanta awajena ." Jikin a sa'bule suka d'an yi shiru daga bisani shukura tace "amma baka san cewar akwai wanda yake son maryama ba har ma ana shirye shiryen kawo kudin auren ta?"wani mugun harara yusif ya buga mata yana d'aga kafad'unsa alamun ko ajikinshi ." Ta sake bud'e baki zatai magana a fusace yace,"Ku dan Allah ban son sakarci da iskanci banza ku ta shi kuje ku sanar da maryama dominta kawai na zo gidan nan ba dan wasu 'yan iska ba ,ta yi sauri tazo ta samar da nutsuwa acikin raina ita kad'ai zuciyata Ke muradin son gani baku marasa kamun kai ba" sakina da shikura sukai shiru suna kallonsa tare da jinjina girman wulakancinsa, yayinda zuciyar shukura ke qara lissafo mata abinda zata sake fad'a masa amman ta kasa domin tsoron amsar da yusif din zai bata "lallai wannan ba wanda zasu zo suyiwa wargi bane, dole sai mahaifiyarsu ta sake shiri akanshi atare suka tashi jikin babu kwari suka fice daga d'akin cike da 'bacin rai ." Aunty salma na zaune tana tunanin ya yusif zai kar'bi ya'yanta sai gasu sun shigo mata rai 'bace ajiyar zuciya ta sauke sannan ta mike tsaye da sauri cike da fargaba duk da dai bata da j akan aikin malaminta tsayawa tayi tana kallonsu d'aya bayan d'aya kafin daga baya tace "yana ga kun dawo min jiki a sanyaye .?" "wallahi mama wannan mutumin mugun d'an wulakanci ne na bugawa a jarida nan shukura ta zayyane wa aunty salma komai daya faru cikin 'bacin rai sakina tace ,"ni dai gsky mama ki hakura ki barwa maryama yusif ta aura tunda ya nuna ita din dai yake so bashi da abinda zai yi damu ita kuma shukura sai ta auri malam yahuza " .bayan aunty salma ta gama jin abinda ya faru tas da abinda sakina ta fad'a tace "bazaa hakura abar mata shi ba wannan auren muddin ina raye sai anyisa da d'aya daga cikinku ." "to gsky mama ni dai banda ni sai dai ki aura masa shikura taje can su qarata dan bazan iya da wulakancinsa ba "na gode sosai yar'uwa dan dama zuciyata tana cikin d'ard'ar ne kar shirin mama yayi tasiri akanki gashi daman dani yafi dacewa tun dana d'aura kwayar idanuna akanshi na kamu da matsanancin qaunarsa "inji cewar shukura ". "yauwa shukurata nasan bazaki ta'ba bani kunya ba daman kuma kamaninmu d'aya "haka ne kuma dole halinku yazo d'aya ba" sakina ta fad'a acikin ranta sannan fili tace "yar wahala sai kije kiyita fama amman kisani bazaki ta'ba daraja acikin idanunshi ba karshe ma ki qarasa rayuwarki a wahala "tana gama fadar haka tasa kai ta shige d'akinsu ta barsu tana jin babu dadi aranta duk da ahalin yanzu babu wani shakuwa da soyayya a tsakaninta da maryama amman a wasu lokutan tana jin babu dadin abinda mahaifiyarta take mata ." "Kece yar wahala daga nace ina son shi sai Kiyi min mummunar fata in sha allahu akanki zai qare "aunty salma taja hannun shukura zuwa cikin d'akinta tana cewa "manta da sakina muyi abinda Ke gabanmu "ta saki hannunta ta qarasa gaban wasu kwanuka ta bud'e d'aya daga ciki ta d'auko tandun kwalli ta mikawa shukura tana cewa "ungo nan shukurata maza ki shafa wannan kwallin idanunki" shukura ta kar'ba ta soma qoqarin shafawa yayinda aunty salma ta juya da sauri ta sake d'auko wani qaramin gwan gwani wanda Ke d'auke da wani bakin magani ta sake dawowa inda shukura take tsaye ta miko mata hannunta d'aya tana cewa "bani kwalli ki bani tafin hannunki idan yasan wata ai bai san wata ba zai san dani yake ". Cike da farinciki shukura ta mika mata tandun kwallin sannan ta mika mata tafin hannunta kamar yadda ta buqata cikin sauri ta zuba mata bakin maganin tana cewa "ki fad'i sunansa sau uku sannan ki fad'i duk abinda kike son yayi miki idan kin isa gabansa ina mai tabbatar miki bazai sake miki mutsu akan komai ba sai akan abinda kika fad'a masa zai yi aiki dashi kuma zai bi umarninki ." nan da nan shukura tayi abinda aunty salma ta umarceta"ki lashe kije zaki ga irin tarbar da zai miki sannan zaki ga irin tarbar da zai yiwa maryama zabinsa ,matsawar kika ga tarban da yayi miki bai miki ba ko ya had'a da tozarci ko cin fuska karki 'bata ranta ki dawo kawai amman kuma wallahi wallahi sai nayi masa abinda sai ya wulaqanta akan soyayyarki sai ya dawo yana kuka akanki, ke sai yayi sambatu akanki sai ya fifitaki akan uwar data kawo shi duniya ". "yauwa mamana shiyasa nake mugun sonki allah dai ya bar min mamana ."maza kije garesa cike da Kamala da mutuntaka da kamewa ki shirya duk wasu kalamai masu sanyi da sanyaya zuciya da zakiyi amfani dashi allah ya bamu sa'a wani irin numfashi shukura ta sauke tare da rungume aunty salma ajikinta tana furta "ameen !sannan ta saketa ta juya da sauri ta bar d'akin ta nufi d'akin da yusif yake ." ahankali ta shiga d'akin bakinta d'auke da sallama yana nan zaune kamar yadda suka fita suka barshi sai dai idanunshi a runtse suke suna kallon saman d'akin sallamar daya ji anyi ne yasashi bud'e idanu tare da sauke idanuwanshi abakin kofar d'akin suka sauka akan shukura dake tsaye tana kallonsa fuskarta cike da fara'a do cikin ido suke kallon juna ." Wasu abubuwa ya dinga ganin suna fitowa daga cikin kwayar idanunta suna shiga nashi nan da nan ya gyara zamansa sosai yana cigaba da kallonta cikin wani irin farinciki mara misaltuwa tamkar lokacin ya fara ganinta arayuwarsa cike da tsananin farinciki yace "ya kika tsaya qaraso gareni zuciyata Ke take muradin son gani "cike da karairaya shukura ta dinga taku har ta qaraso ta zauna kusa dashi ya zuba mata ido kawai yana sakar mata tsadadden murmushinsa cikin shukin qaunarta daya ji daga sama "yaya yusif !" Ta kira sunansa cikin wata irin murya idanuwanshi kawai ya zuba mata batare da yace mata komai ba " akace daya daga cikinmu zata maye maka gurbin maryama a wajenka me ka gani ."?murmushi yayi kawai "gabanta ya shiga fad'uwa amman data tuna irin tarban da yayi mata a yanzu sai taji wani sabon gwarin gwiwa ya shigeta "ina son na maye gurbin maryama acikin zuciyarka me zaka iya cewa ?"ai wannan ba komai bane na amince dake dan ma kin fita dacewa dani ". ta lumshe idanunta kana tace "amman kace domin maryama kawai kazo gidan nan ba dan wasu yan iska ba ?tayi masa tambayar tana mai kafesa da idanunta yayi shiru yana kallonta qirjinsa na wani irin bugawa da karfi "maryama kad'ai zuciyarka ke muradin son gani bamu marasa kamun kai ba ?ya kai hannusa ya riko hannunta gam cikin nashi yana matsewa "yaushe na fad'i haka ?ni babu wacce zuciyata ke muradin gani sai ke murmushi tayi kawai aranta tace "aiki yayi tasiri kanan "ta qara damke hannunsa dake cikin nashi "baka ci komai da'aka kawo maka ba". "na koshi domin ganinki ma kawai ya kosar dani "ya fad'a a daidai lokacin da kausar ta shigo hannunta rike dana maryam ."wani irin bugu zuciyar kausar yayi da karfi sakamakon ganin yanayinsu dan ita maryama daman ta rigada ta cire samunsa acikin ranta ganinsu haka ma bai d'aga mata hankali ba ." cikin wani salon jan hankali shukura ta tsura masa ido tana kallon kwayar idanunshi tana jin wani irin shaukin sonshi na ratsata yayinda maryama ta zame hannun ta cikin na kausar ta samu waje ta jingina bayanta da bangon d'akin Tare da sunkuyar da kanta kasa tana kallon zara zaran yatsun kafafunta dan bata son ganinsu bancin darajan kausar ma da ko hanyar d'akin bazata biyo ba ." cike da tashin hankali kausar tace "yaya meye haka kuma ?"mai nayi kausar ?shima ya tambayeta yana jin kamar ana soka masa allura a gabad'aya ilahirin jikinsa "jikin maryama ya qara yin sanyi rauninta ya soma bayyana idanunta suka fara ciccikowa da ruwan hawaye "shikenan shima an gama dashi "ta fad'a acikin zuciyarta "dan Allah malama ki sakar masa hannu"kausar ta fad'a tana zabga mata harara shukura tayi murmushin mugunta tana zare hannunta cikin nashi tsaki kausar taja sannan ta soma zayyane masa duk abinda maryama ta fad'a ". Amman da mamakinta sai ji tayi yace "sai me idan ta fad'a miki haka ?ta sake kallonsa a matukar tsorace tana cewa "yaya me kake nufi da fad'ar haka ?ina nufin yanzu shukura nike so kuma ita zan aura "ya salam yaushe wannan alamarin ya faru ?amman ko akan hanyarmu ta zuwa nan babu wannan tsarin a zuciyarka ? maganar maryama kake tayi babu tsarin auren wata shukura arayuwarka "to yanzu na canza raayina ita nake so kuma ita zan aura " a kan me ma zan auri wannan yarinyar? ya fad'a yana nuna maryama da babban yatsan hannunsa ." "kausar ta rikice ta gigice ta waiga ta kalli maryama dake tsaye shiru tana ciza lips dinta na kasa "haba yaya me yasa zakayi haka ?me yasa zaka sa'ba alkwarin da kayiwa mumy ?me yasa ka furtawa maryama cewar kana sonta zaka aureta yanzu kuma kazo da wata magana da hankali bazai d'auka ba "why why !!? yaya dan allah karkayi haka,ka dawo haiyacinka karka yiwa maryama haka tayi maganar cike da tashin hankali idanunta na kawo ruwan hawaye ." "Duk yanzu na daina jin komai akanta sai dai ko a cikin masu mana aiki a gidanmu zan bawa wani shawarar ya auri wannan yarinya,amman yanzu sai shukura itace zabina a halin yanzu ma na kagauta na d'auketa daga wannan gidan dan ta fi karfin zamansa ita din ta
Chapter 27 · 0% Book details