← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 105

Sashe 102

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wanda yake da iko akanka da kuma kamfani ya bata dama yanzu sai kayi duk abinda zaka.. ai bata kai ga qarasa maganarta ba taji saukar wasu lafiyayyun mari ji kake tass tass !! har guda biyu ajere akan kuncinta enough..!ya fad a a matukar tsawace gbdy mutanen da ke zaune a parlour n babu wanda hankalinsa bai tashi ba cikin tsananin tsoro da tashin hankali aunty abida ta tsaya cak dafe da kuncinta tana dubansa fuskarta da bayyanan ne mamaki Adam ka mareni ? an kika gani muddin bazaki daina shiga rayuwata ba ya fad a a matukar tsawace . Hankalin aunty shahida a tashe ta qaraso inda yake tsaye jikinsa na wani irin tsuma ta dafa kafad ansa tare da fad kana da hankali kuwa ? ka kusan wacce ka mara ?matar aure ce kuma matar shakikinka tana magana tana nuna masa aunty abida da hannunta .iskar bakinsa ya fesar yace nasan ko wacece kuma nasan matsayinta kuma itama tasan ko waye ni bana cikin irin wadan mutanen da zuciyarsu Ke jurar raini wallahi idan bata daina enter dinta ba wata rana dukan mutuwa zan mata zaro ido aunty shahida tayi jikinta na wani rawa kamar yadda na mami ke rawa kana hauka ne adamcy ? I don t know but I fell like na haukace wai meke damunka ne da kake abubuwa haka ? dan Allah shahida ki barni kin cika min kunne abinda ya kamata kiyi ki ja mata kunne ta fita hanyata ta daina shiga lamarina that s all yana gama fad ar haka ya haye sama da sauri sauri yake taka step . gabad ayansu da kwayar idanu suka bisa dashi har suka daina ganinsa . aunty shahida ta soma taku zata bisa mami tayi saurin riko mata tana girgiza mata kai karki bisa shahida kinsan halinsa an san halinsa mami amman shikenan sai a zuba masa ido ya dinga abinda yaga dama . ?ai daman ita ke daure masa gindin yin iskanci da wulakanci da taka duk wanda yaso dadin abun itama bai barta ba shegen yaro mara tarbiya kawai inna lillahi wa inna ilaihi rajiun abinda aunty shahida ta furta kenan alokacin da taji abinda baba qarami ya fad a tayi data sanin yin maganarta, da kuma tasan kalmar da zai fad a kenan da wallahi bazatace komai ba jiki a sanyaye mami ta nufi hanyar bangarenta aunty shahida ta juyo ta kalli baba qarami dake qoqarin mikewa tsaye zuciyarta na wani irin tafasa taso kwarai ta furta koda kalma daya ce akan kalmar shegen daya furta ga adamcy amman sai zuciyarta ta gargadeta domin a yanzu ma kuskurenta ne ya janyo ya fad a abinda ya fad a bazata so ta sake aikata wani kuskuren ba ranta a bace ta juya tabi bayan mami . Zaune ta isketa mami a baki gadonta tayi shiru idanunta na kallon sama d akinta ta samu waje kusa da qafafunta ta zauna cike da girmamawa ta kira sunanta mami ! mami ta sauke idanunta tana kallon aunty shahida fuskarta da alamun damuwa aunty shahida tayi kasa da kanta kana ta soma magana cike da biyayya dan allah mami kiyi hakuri bisa kuskurena sam ban ji dadin abinda baba qarami ya fad a ba domin idan mutun yace wa d anka bashi da tarbiya to kai yake son ya zaga ya fake da zagin d anka numfashi mami ta sauke tana cewa karki damu shahida idan da sabo na rigada na saba da halinsa kuma hausawa sukance dan kuka mai jawa uwarsa jifa duk wa ja min koda zagina yayi ?ni dai fatana allah ya canza adamcy allah kuma ya tsaresa daga sharrinsu Allah yasa kafin mutuwa naga canzawarsu aunty shahida ta share hawayen daya zubo mata menene kuma abun zubar da hawaye ?wallahi mami kalmar tayi min zafi bansan me yasa yanzu baba qarami yake nunawa adamcy kiyayya haka ba ,ji nayi kamar na tanka masa gara da baki tanka masa ba ai sai ya tabbatar da rashin tarbiyar da yace allah dai ya sawaka kawai zamu ce ahankali suka dinga tautaunawa wanda kusan duk akan adamcy ne . ******* On 28 cikin sauri sauri maryama tayi abinda zatayi ta shirya cikin riga da siket blue da ratsin yellow ta dauko after dres ta daura akan kaya tayi rolling din kanta da mayafin after dress din ta rufe koina ajikinta ga kyau ga qarancin shekaru wanda yasa tayi looking very attractive ta fito zuwa parlour n sai dai duk ranta babu dadi , da granny ta soma cin karo ta durkusa har kasa ta gaisheta barka da safiya granny barka maryama fatan kin tashi ? Lfy ina umma? bata rufe baki ba umma ta fito daga dakinta ta qaraso ta tsaya kusa da maryama ta dafa kafadanta har kin shirya masoyiya ? maryama tayi murmushin jin dadin sunan da umma ta kirata dashi tace na shirya umma barka da safiya kin tashi lafiya ?ta gyada mata kai tana cewa alhamdulillah gamu zamu yakin karshe grany ta matso sosai kusa daita maryama ki bi komai a hankali ki kiyaye banda shiga abinda bai shafeki ba allah ya baki saa a dukkanin abinda kike sa gaba .murmushi maryama tayi tana cewa Ameen angama kakata ta kaina zan kula da duk abinda kikace, ta juya bangaren umma tana kallonta sai ku tayani da addua, in sha allahu zakiyi nasara amman kamar kinso kiyi late ? Aa banyi latti ba zamuyi daidai sai na dawo umma ai baki karya ba ta fad a tare da mikewa ta janyo hannuta bata tsaya koina daita ba sai inda ta ajiye mata plet din abincin data zuba mata ta zaunar daita ta soma bata abinci a baki tana ci tana duba mata lokaci har ta koshi ta sha ruwa ta mike tsaye tare da jiran adduarta fatan alkhairi diyata karki sawa zuciyar karaya ki karfafa zuciyarki kisa aranki matsalarki tazo karshe da yarda allah ki kula da kanki please in sha allahu ta kalli inda Aunty Hasana take zaune akan kujera wacce ko kallon inda take batayi ba a tun sanda ta fito daga daki sai man karanta wani littafi take . jiki a sanyaye kamar kartace mata komai tunda tasan ba fatan alkhairi take mata ba amman dai ta barwa allah komai kuma ko babu komai kanwar mahaifinta ce sai datai adduar samun nasara akanta sannan ta bude bakinta da kyar tace aunty hasana ni zan tafi interview fuskatar ta babu yabo babu fallasa ta dago tana cewa in sha allahu bazaki samu aikin nan ba yadda kika fita da murna in sha allahu da bakinciki zaki dawo gidan nan kinyi sanadin kashe mana d a amman Ke har kin manta kin fara neman aikinyi jikin maryama yayi sanyi hawaye ya cika kwarnin idanunta hasana bai kamata ki dingawa diyar danuwanki haka ba to mama ni meye nayi mata bayan gsky na fad a aiki ne a gabanta ko zama tayi tunanin abinda Ke damun rayuwarta muddin kina son zaman lafiyarki damu ki kiyaye takurawa yarinyar nan kinji na fad a miki ai daman nasan duk kun tsananeni akan wannan yar iskar yarinya irin tsiya irin jaraba kawai masu mugun jini taja tsaki ta dauke kanta akansu . Shiru maryama tayi tsaye ta kasa kwakkwaran motsi tana duban Aunty hasana cike da sarewa gbdy sai taji zuwa interview din ma ya fita ranta domin tana ji ajiknta kotaje bazatai nasara ba granny ta janyota zuwa jikinta maryam ki maida hankali lokaci na tafiya fa karki damu da maganar wannan mayar in sha allahu zaki samu aiki okay granny na gode sosai abinda granny ta fada in sha allahu haka ne zai kasance karki manta cewar hasana ba itace takawoki duniya ba dan haka babu abinda bakinta zai miki inji cewar umma idanun maryama suka kawo kwalla muryarta a raunane tace ni dai ku bata hakuri idan wani laifi nayi mata ta yafe min dan banason tana fadar mummunar kalamai akaina umma idan kin sani bayan babu ran iyayenka addaur yanuwansu tamkar adduar iyayenka ne haka ne amman ita mummunar adduarta bazatai tasiri akanki ba saboda baki mata laifin komai ba ai baza ta bawa yiwa diyar cikinta mummunar addua ba Aunty ki daina hada diyar cikina da wannan yarinyar ita din ba diyata bace ya kamata ki fahimta allah dai ya ganar dake gsky dan ni banga amfani kiyayyar nan ba , idan uwarta tana da laifi dan ta auri danuwanki ai danuwanki ma yana da laifi daya nace sai daya aureta . inji cewar granny Ni wallahi umma da nayi zamana dan ina ji bazaki zauna ba kuma babu abinda kike ji sai alkhairi maza kama hanya ki wuce fatan alkhairi allah yayi miki albarka Ameen ta juya cike da sanyin jiki take daga kafafunta . Ganin haka yasa umma ta mike ta biyota tana cewa ki shiga wajen Auty ku gaisa kafin ki wuce amman kiyi sauri karki yi latti kinji masoyiya maryama tace to umma na wuce sai na dawo to sai kin dawo allah ya tsare fatan alkhairi maryama allah ya bada saa ta fito bangaren mahaifiyarta ta shiga bayan ta gaisheta tayi mata sallama itama fatan alkhairi tayi mata aunty ina after dad?yana ciki yana bacci okay ki fad a masa na tafi interview ku tayani da adduar samun nasara tana qoqarin fita daga part din aunty ta kira sunanta princess ! ta tsaya cak tare da juyowa ta fuskanci mahaifiyarta tana mai gyara zaman Jakarta a kafadarta kinyi breakfast kuwa da kike kokarin fita ta qaraso gabanta hannunta rike da cup din tea mai kauri tare da bread bata tsaya jiran mai za tace ba ta kai cup din tea bakinta bude bakinki ki sha ko kadan ne bana son kina fita batare da kin sakawa cikinki komai ba . ahankali ta bude bakinta tace naci abinci daga hannun umma kuma na koshi amman bari naci daga hannunki ta soma kurban tea ba wani mai yawa ta sha ba tace ya isa haka na gode sosai ta rungumeta tare da yi mata sallama tana fitowa daga part dinsu ta rufe fuskarta da qara min nikaf . ******** Babban hall ne aka tanadar masu ,suna zaune gefenta yusura ce itama sanye cikin shiga ta kamala kowanne
Chapter 102 · 0% Book details