← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 105

Sashe 17

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

,wani hawaye ne masu zafi suka shiga turereniyar zubo mata ,kuka take sosai tana datasanin kiran mami datai a daren jiya ,dan tasan da bata kirata ba da hankalinta bai tsaidu akanta ba har tayi musu diran makiya da sassafe ba ." " wayyo allah nah ni maryam na shiga uku nah wannan duk laifina ne . ta fad'a tana toshe bakinta da hannunwanta duka dan kar sautin kukanta ya bayyana ." cikin tsananin fushi ata yace "okay sweetheart bazan bi umarninki akan wannan banzar yarinyar ba "ya fad'a atakaice yana furza da iska mai zafi daga bakinsa ." "Naji bazaka bi umarnina ba amman kasani daga yau babu ni babu kai ka cigaba da rayuwarka kai kad'ai har duniya ta nade " tana gama fad'ar haka ta nufi hanyar step tana kwallawa maryam kira da karfi "maryam !!! mrym ta qarasa saukowa da sauri ta tsaya cike da fad'uwar gaba tana duban mami "d'auko mayafinki muje "ina kuma mami ?tayi mata tambayar a matukar firgice ." "gida mana dan bazan tafi na barki acikin wannan gidan ba "kallon mami take cike da matsanamcin mamaki sannan ta waiga ta kalli ata dake tsaye taga yadda yake fidda numfashi har qirjinsa na sama da kasa wanda yake nuna tsananin tashin hankali". cike da tashin hankali ta shiga girgiza ma mami kai sannan ta soma magana "mami dan girman allah kiyi hakuri ki barni kiyi tafiyarki ni zan hakurin zama dashi haka ta fad'a voice dinta na rawa ". "dan ubanki zaman me zaki cigaba dayi dashi yana wulakantaki ?maryam tayi narai narai da idanunta tana damke hannuwanta cikin juna ,kin kuwa san babu wulakanci daya kai miji yaki kwana a gidan amaryarsa a daren farkonta zafi da ciwo ?"nasani mami dan ni kad'ai nasan halin damuwar dana kwana ciki jiya , tayi mgnr acikin zuciyarta tana qoqarin daidaita natsuwarta ." "Ya wulakantanki ya tozartaki ya qunsa miki bakincikin da bazaki iya mantawa dashi ba har abada amman ki tsaya kina 'bata min lokacin" mrym ta girgiza mata kai tana mai share hawayenta "amman bake ya wulakanta ya tozarta ba ni yayiwa kuma na gode masa amman kisani bazan tafi na barki cikin wannan halin ba dan haka ki hau sama yanzu ki d'auko mayafinki muje an gama wannan auren". mami ta fad'a cikin tsanani 'bacin rai. "kiyi hakuri mami duk laifina ne dana kiraki na d'aga miki hankali me yasa ma zan kiraki ? sannan me yasa zaki hukuntashi ? da kin barshi ni ki hukuntani mami akan abinda na aikata kina zaman zamanki na d'aga miki hankali " maryam ta fad'a hawaye na zubo mata ."you're very stupid so you're the one caused all this problems ? amman dan munafurci kizo kinawa mutane kukan munafurci ." " ina zaman lafiya da mahaifiyata aurenki ya shiga tsakanina daita sannan dan kin cika mahaukaciya ballagaza kika kirata kikace ban kwana gida ba ,dan ubanki idan na kwana a gidan uban me zan miki ? "ya fad'a a fusace ".?a matukar rikice tace "please am sorry I never know she wil act like this "ta fad'a hawaye na sake zubo mata, wani irin mugun kallo ya watsa mata sannan yay qoqarin qarasowa inda take mami na ganin haka tayi saurin taresa da hannunta dan ta lura baya cikin haiyacinsa "karka soma ta'ba min lafiyar yarinya mami ta fad'a muryarta na rawa bata ta'ba ganin yanayinsa haka ba ". "Yau sai na kashe yarinyar nan da uban daya haifeta ya fad'a cikin cigaba da takowa cikin isa da 'bacin rai jin abinda ya fad'a yasa maryam rungume mami ta baya tana wani irin kuka tmkr qaramar yarinya "mami ki taimakeni dan girman allah "weetheart ki bani hanya naci ubanta na ganar daita kuskurenta wanda har abada bazata sake aikawata wani ba bare ni "ka shiga hankalinka ita dai tashiga hankalinta adamcy banason abinda kake min dan babu laifinta ko d'aya idan hukunci ne ni dana mareka zaka hukunta." "please sweetheart ki matsa dan babu abinda zai hanani ban hukunta wannan yarinyar ba akanta fa sweetheart kika mareni yana qoqarin kamo hannun maryam mami ta sake sauke masa wasu marukan ji kake tas tass !! har biyu ajere ."wannan karon kam ata daskarewa yayi awaje d'aya yana kallon mami cike da tsananin mamaki abun yayi mugun girgiza shi "yau sweetheart dinsa ce tay masa mari har uku kuma duk akan wannan banzar yarinyar ".? maryam kam fashewa tayi da wani sabon kuka ganin abinda mami ta sake aikatawa " matsawar ka ta'ba maryam ban yafe maka ba tana gama fad'ar haka ta juya rike da hannun maryam sai dai abun mamaki mrym din taki biyota ta turje jikinta na kyamarrr , dole tasa mami ta tsaya ta juyo tare da zuba mata ido tana neman qarin bayani, amman mrym tayi shiru sai hawaye dake sauka akan kuncinta"kina ganin irin wulakanci da yayi min amman da yake ke baki da zuciya zaki ki biyoni wato ke gaki mai ..." kafin mami ta qarasa maganrta mrym ta zube kasa gabanta tana kuka tana bata hakuri .""Kiyi hakuri mami wallahi ba haka bane, ba kuma abinda kike nufi bane ,nayi nadama dan allah mami kiyi hakuri ki yafe masa ki daina fad'a masa kalamai haka marasa dadi ,kuma ni babu inda zan biki zan zauna a gidan mijina,da dad'i da babu zanyi hakuri dashi "tana gama fad'ar haka ta sunkuyar da kanta kasa ganin irin kallon da mami take mata mami tayi shiru kawai tana kallonta gbdy taji kwarin gwaiwarta yayi kasa ." Jin mami tayi shiru hankalin mrym yayi mugun tashi rawar da jikinta yake ya qaru ta d'ago kanta ahankali taga ita din mami take kallo har lokacin muryarta a sanyaye tace "kiyi hakuri mami kece fa kike bani hakuri da kwarin gwiwar da har muka kawo matakin maaurata ,to me yasa akwana d'aya kawai da nayi a gidansa zaki d'auki zafi akansa alhalin kin fi kowa sanin waye shi ."? nan kuma jikin mami yayi sanyi ta tsaya kawai tana cigaba kallon mrym , shi kuwa ata zuba masu ido kawai yayi yana jin zallar 'bacin rai na ratsashi yaji tsanar mrym ya sake qaruwa da mamaye duk wani sansar jikinsa "wallahi bancin mami dake tsakaninsu da shi kad'ai yasan irin azabar da zai gana mata amman duk da haka bata tsira ba zai ganar daita Kuskurenta ,runtse idanushi yayi yana cizan lip's dinsa na kasa da karfi yayinda hawaye ke bin kuncin maryam , tsaki yaja sannan ya juya a fusace ya haye sama cikin tsananin fushi yake taka step ." Yana shiga d'akin daya zamo nashi ne ya soma zariya aciki he's thinking of if someone else did what his mother did to him today da wallahi allah ne kadai zai rabasu amman sweetheart rayuwarsa ce yana matuqar qaunarta, yana son duk wani abinda take so wajen had in aurensa da wannan bazar yarinyar ne kawai raayinsu ya sha bam bam tsaki yayita ja tare dafe goshinsa dan wani irin sara kanshi ya cigaba da yi ." "Maryam ta kamo hannun mami ta zaunar daita akan kujera sannan ta durkusa kasa gabanta "kiyi hakuri mami kema fa kinsan halinsa Kmr yadda kike cewa zai canza nima haka nasa araina wata rana idan allah ya taimakemu sai kiga ya canza, nayi miki alkwarin zan zauna dashi har tsawon rayuwata sannan kiyi min alkwarin bazaki sake kai hannunki fuskarsa ba sannan ki daina fad'ar kalamai marasa dadi akanshi nima kona kiraki karki saurareni akan kowacce matsala ki bani hakuri kamar yadda kike bawa sauran ya yanki." Mami ta qirgiza mata kai alamun bazata iya ba please mami do the same thing to me bafa zan zuba ido ba maryam ,dole nayi mgn idan ma baki fad a min ba dole zan san komai please!.. bafa zan zuba idanu yayi miki wulakanci daya ga dama ba domin Ke din amana ce a wajena kuma duk abinda yayi miki dole ne ya dameni ko bakya adamcy ya aura ba dole ne nasa ido a gidansa idan naga zai cutar da yar mutane bare ke da kika kasance jinina "duk da haka dai mami Kiyi min alkawarin bazaki sake damun rayuwarsa akaina ba mrym ta fad'a tana sakar mata murmushin dole wanda kana kallo had'e yake da tarin damuwa. "Shikenan bazan sake ba mami ta fad'a tana kukan tausayinta dana tilon d anta data san haka auren zai kasance wallahi data hakura tun farko daya nuna baya so ."ahankali maryam ta kai hannunta tana goge mata hawaye tana cewa "mami ki bar kuka . zubar da hawayenki akanshi maseefa ne a gareshi "ta d'aga mata kai kawai dan batasan me zata ce ba dan kukan ne ya fiyye mata sauki akan mgnr da zatai " daga nan mrym ta cigaba da kwantar wa mami da hankali ."zuciyar mami tayi sanyi ta sake amanna maryam itace mace d'aya da zata kular mata da rayuwar tilon d'anta." murya a sanyaye mami tace "tashi kije ki kirashi yazo ya bani hakuri "maryam ta zaro ido tana kallon mami a matukar firgice "wallahi mami bazan iya ba he wil beat me to the exetended sai kin koka min kina kallo fa if bancin kina nan da yanzu ba wannan labarin ake fad'a ba ."allah bazan ta'ba iya tunkarar sa ba kawai Kiyi hakuri ki yafe masa "mami am so much in love with your lovely son amman bani da wannan kwarin gwiwa ." ta fad'a aranta hawaye na gangaro mata ." hankali ta dora kanta akan cinyar mami tana zubar da hawaye ."tana matuqar sonshi and she don't want to loose him at all, she don't know what's happening to her brain, dan tana jin idan ya saketa ko idan mami ta raba auren zata iya mutuwa for real mami tace "kiyi hakuri mrym ki daina kuka nasan adamcy baya sonki shiyasa kikaga bana tuna duk wani halin da zai shiga nake yanke hukunci akanshi ta fad'a tana shafa kanta ." "Ni kuma kinga bana son abinda kike masa " mrym ta fad'a a fili tana sheshekan kuka "baki so ?"mami ta tmbyeta ahankali tace "eh mami bana s ina jin ciwo a zuciyata sosai kinga sakamakon abinda kika yi yau ya qara d'aukar zafi dani tsanata ya sake qaruwa a zuciyarsa
Chapter 17 · 0% Book details