Sashe 28
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dabance acikin zuciyata Ina kallonta ina jin farinciki araina " hawaye dake makale acikin idanunta maryama suka zubo akan kuncin tayi sauri tasa hannunta ta goge yayinda zuciyar shukura tayi mata sanyi ta qara tabbatarwa kanta aikinsu yayi tasiri akanshi ta d'auko ruwan lemu ta tsiyaya a cup ta mikawa yusif tana cewa "ungo sha kaji sanyi aranka "yasa hannu ya kar'ba yana sakar mata murmushi cikin tsananin tashin hankali kausar tace "karka sa'ba alkwarin daka d'auka ,da maryama kawai kafi dacewa ba da wata shukura ba ka bud'e idanunka da kyau please ." cikin wata irin murya mai sanyi da tausasawa maryama tace "kausar karki d'aga hankalinki dan baya cikin hankalinsa da natsuwarsa hasalima bazai ta'ba fahimtarki ba a halin yanzu ,kiyiwa danuwanki addua dani da shukura duk abu d'aya ne bazan ta'ba bakinciki dan yusif ya canza ni da shukura ba fatana allah ya basu zaman lafiya tana cikin fad'ar haka taji an fasa kuka abayanta mai kukan tana fadin" lahaula wala kuwwata inna lillahi wa inna ilahi rajiun wannan wani irin massefa ne haka ? Duk suka juya umma suka gani tsaye cikin matsanancin tashin hankali "Shukura me maryama tayi miki kike shiga rayuwarta ?amman Kisani allah baya bacci kuma zai saka mata da kyakkyawan sakayya Ke kuma zaki ga muguwar sakayya dake da uwarki "idanu kawai yusif ya zuba mata ya kasa cewa komai "kiyi mata na malam yahuza ta hakura ta bar miki shi yanzu kuma yusif din kike so ?". "umma gashi nan ki tambayesa bani nace ina sonshi ba shine da kanshi ya canza dani " yi min shiru munafukar allah daga Ke har uwarki zaku girba abinda kuka shauka ,da izinin allah sai maryama ta samu wanda yafi yusif komai kausar ta bukaci umma tayi mata qarin bayani akan mlm yahuza batare da 'bata lokaci ba ta zayyane mata komai ." "uhmm lallai maryam kina cikin tashin hankali allah ya fitar dake kawai zan iya cewa sannan ta cire wayarta daga cikin fost dinta ta kar6i mukullin mota daga hannun yusif ta fice waje tana neman layin mumy yusif ya cigaba da yin shiru maryama ta juya jiki a sanyaye ta bar d'akin tana goge hawaye haka zalika umma kasa cigaba da tsayuwa tayi zuciyarta na tafarfasa ta shige d'akanta tana kuka ." yaya sadam dake tsaye yana waya ya hango fitowar maryama tana tafiya tana goge hawaye ya bita da kallo Kamar ya tsaidaita yaji damuwarta sai kuma ya rabu daita da zumar zai nemeta daga baya ya cigaba da wayar da yake cikin haka kiran umma ya shigo wayarsa daman what's app call yake ."ya katse kiran domin ya d'auki kiran ummah kiran ya katse ya lalubo qaramar wayarsa yayi mamakin ganin missed call dinta dayawa ashe a silet yake " ya kirata dan baya son ya shiga sai ya gama wayar da yake ,tana d'auka yaji muryarta can qasa tana kiran sunansa ya amsa yana tambayarta "lafiya ummah naji muryarki haka ?tace sadam kana ina ne ?ina cikin gida " tace ka shigo yanzu yanzu "okay! kawai ya fad'a ya soma tafiya cikin sauri ya shigo d'akinta."ya garasa inda take zaune yana cewa "lafiya umma meke damunki kamar ma kinyi kuka ?." wani sabon kukan ta fashe masa dashi tana zayyane masa abinda ya faru yace "ikon allah anya kuwa lafiya ?ina fa lafiya sadam kai ma kasan ba lafiya ba ,"yanzu dai sai a kira abba aji me zai ce ,ai wad'an nan mutanen abun nasu babu imani ai bazasu bar iyayensa ma haka ba duk abinda zasuyi dan su juyar da hankularsu zasuyi ." jikin yaya sadam yayi sanyi ya kasa cigaba da magana "wallahi da ina da inda zan kai maryama ta cigaba da rayuwarta da nayi dan ina son taji dadi, maryama tasha wahala a hannun mutanen gidan nan sam sam basa son ganin cigabanta .""Kiyi hakuri umma komai zai wace babu abinda yafi karfin addua maryama malama ce nasan zatayi addua ."ban ta'ba shiga tashin hankali irin na yau ba domin har ga allah naso auren maryama da yusif amman da izinin allah bazasu ci bulus ba duk abinda sukai mata bazai tafi a banza ba sai allah yayi mana maganinsa ." bayan fitarsu maryama yusif ya tattara hankalinsa kacokan akan shukura ita kuma sai faman zuba masa surutu take ,acikin zuciyarsa baya jin dadin hirarta amman kuma zahiri abun ba haka bane murmushi kawai yake sakar mata yana biye mata ."karfe biyu daidai suka fito tare da shukura sai ga baba gali ya shigo ."yana ganin yusif tare da shukura ya washe hakora yana cewa "a'a yusif ashe dai kazo?yusif ya gaishesa , baba gali ya amsa yana tmbyrsa "ina ita maryama take dana ganka da shukura ?yusif ya d'an tsotsa keyarsa yace "yanzu ta wuce tana kuka wai dan nace shukurace zabina ita zan aura "shukura kuma yusif ?yayi mgnr Kmr bai san komai ba "kwarai kuwa baba ita zan aura dan haka da zarar na koma gida zan sheidawa dady da mumy agaugauta azo a nemar min aurenta ta zama mallakina ". "Ikon Allah haka kuma abun ya kasance ?kai kuwa yusif me yasa zakayi haka?" idan wani abu tayi maka sai ka sanar ayi mata magana bawai ka canzata da shukura ba ya fad'a haka a fili amman a bad'ani murna yayi yace abu yayi kyau aikin salama yayi tasiri daman yasan zata iya fiyye da hakan muddin akan biyan buqatarta ne "babu laifin da ta min kawai dai bana sonta ne yanzu shukura zan aura "to to shikenan allah yayi maka albarka Allah yasa ayi damu ." Yasuf ya amsa da "ameen !ya tura hannunsa cikin aljihu ya ciro bandir din yan dubu ya mika wa baba gali "ga wannan baba "kai yusif har da wata hidima ai da ka barshi ni murnar auren shukura ma da zakayi ya wadatar dani sukai sallama da baba gali ya wucesu yana murna yasuf ya kira kausar tana dauka yace "Ke kina ina ne ?ina tare da maryama ne " ta bashi amsa da haka "to ni zan wuce idan kin shirya ki fito mu wuce idan kuma na wuce ne na barki to ?ok minti biyu kawai na baki tare da maryama suka fito tana kwantar mata da hankali " kausar kenan karki wani damu dani fa idan da sabo maryama ta rigada ta saba kawai Kiyi wa dan'uwanki addua in sha allahu nima zan tayaku yi masa addua ki gaishe min da mum kice ina matukar qaunarta "tana gama fad'ar haka ta juya ta soma taku a natse kausar ta bita da kallo hawaye na zubo mata ."tunda maryama ta juya hawaye ke turereniyar zubo mata qirjinta banda bugawa babu abinda yake ta kasa shiga bangarensu ta wuce bayan d'akinsu tana kuka tun daga kasan zuciyarta " ko kallon shukura kausar batayi ba ta fice daga gidan cike da tausayin maryama suka wuce ." alhamdulillah aunty salma ta furta cike da yalwataccen farinciki wannan magana itace mafi dadi acikin zuciyata "wallahi mama kin gama min komai arayuwata kinga yadda ya rikice yace ma nan kusa zaa daura auren "haba wa ai ni din bata wasa bace ai muddin baku auru ba to wallahi babu mai zuwa ya kwashe wannan banzar yarinyar.""baba gali yace "ai baki ta'ba faranta min rai ba kamar yau na dauka fa abun bazai yuwu ba ashe shi yafi komai sauki a wajenki dan allah kisa ayi aikin da zaayi auren kamar yadda ya fad'a "kai dai ka zuba ido kawai kayi kallo wannan auren kamar anyi an gama ." "Kinga bari na kira fati na sheida mata ta soma shirinta "ya fad'a yana lalubo wayarsa "wani shiri kuma gareta ?aunty salma ta tambayesa "ai muktar dinta ke mutuwar son maryama tun kwanaki dana je gidanta take sheida min nace ta d'an jinkirta muga me zai faru kinga yanzu dama ta samu",lallai kam dama ta samu daman shine daidai da aurenta" aunty salma ta fad'a tana kwashewa da wata mahaukaciyar dariya zaa qare auren dan giya " kai salama baki da dad'i wallahi bakaji dadin da naji ba ai nan duniya bana qaunar maryama yarinyar kamar aljana ga kyau ga shiga rai suje su karata da muktar, shi din ma bazata auresa ba sai ya'yana sun bar gidan nan ." Cike da murna da farinciki baba gali ya kira aunty fati ya sheida mata komai ai kuwa tayi murna dan muktar din ma ya dameta kullum bashi da magana sai na maryama hatta shaye shayen da yake yace zai daina muddin zaa bashi aurenta" da kyar maryama taja kafafunta ta shigo parlour'nsu tana mai danne damuwarta sai dai kallo daya zaka mata ka fahimci tana d'an cikin damuwa aunty ta dubeta tace "Kuna fita aunty fati ta kira waya wai kizo gobe da safe tana son ganinki "to !kawai maryama ta fad'a ta shige d'akinta dan bata son tayi doguwar hirar da har zai s mahaifiyarta ta fahimci wani abu duk da tasan dan dole tasani amman ba da wuri haka ba "safa da marwa ta shiga yi acikin d'akin tare da cure hannuwanta waje d'aya" tsawon shekaru aunty salma na bibiyar rayuwarta ." "laifin me tayi mata ? me ta tare mata? idan wani laifi tayi mata ta fad'a mata ta nemi yafiyarta ta barta ta huta "? wasu hawaye masu ciwo suka gangaro mata a yanzu ba kanta kad'ai take tausayawa ba har da mahaifiyar yusif da yaruwarsa dan ita tsakaninsu dasu aunty salma da baba gali da ya'yanta allah ya isa ne bazata ta'ba yafe masu ba ,domin cirewa kanta damuwa Kan kujerar zanenta ta nufa ta zauna ta zaro farar takarda ta ajiye agabanta ta d'auki pencil ta tura cikin bakinta ta fara tunanin me zata zana ?". Babu abinda yazo cikin kwakwaluwarta sai fuskar kausar murmushi mai hade da damuwa ya bayyana akan fuskarta "kausar zan zana domin dai nasan shikenan ni da ita kuma sai wani ikon allah ."ahankali ta soma bada shape din fuskarta tunda ta zauna bata tashi ba sallah laasar n kawa ya tashita koda ta idar ma Kan aikinta ta koma ta cigaba ranar a d'akin maryama ta qarasa niyyinta da misalin karfe bakwai aunty ta shigo d'akin ta isketa tana gabatar da sallar magrib ." Ta