← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 105

Sashe 30

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tasan idan ba tsanarta da aunty fati tayi ba babu yadda zaa yi tace ta auri d anta domin ko ita take da diya kamarta tayi imani bazata dauketa ta bawa muktar aure ba mutumin da idan yayi shaye shayensa har kwata yake fadawa haka maryama ta koma gida tana cika tana batsewa duk ranta a dagule ." Aunty ce ta fito daga kitchen tace "lafiya kuwa naga har kin dawo yanzu ?hawaye maryama ta share tace" aunty laifin me nayi da allah ya qaddaroni cikin wannan dangin ?basa sona basa qaunar cigabanna idan akwai wacce suka tsana a duniya t nice suna jin kamr su kasheni wallahi suzo su kasheni su huta da muguwar tsanar da suka min na rasa me nayi masu arayuwar nan da suka tsane ni."aunty ta zauna kusa daita jikinta na rawa tace "me ya faru maryama ?"na gaji da wannan rayuwar aunty fati so take ta kasheni dan Allah ku barta ta kasheni ni yanzu nafi bukatar mutuwa da rayuwata akan dai ta hadani da muktar . ta qarasa maganar tana kuka . kwantar da hankalinki kiyi min bayani da kyau ban fahimceki ba ta hadaki da muktar kamar ya ?" "Wai ya aureni !"numafashi aunty ta sauke cikin rarrashi tace "haba maryama ki daina daga hankalinki tunda ga maganar yusif nasan baba gali zai yi mata bayanin komai maryama ta fashe da wani sabon kuka dan ta ta bo mata wani ciwo ne data binne "babu wannna auren bilkisu . muryar umma suka jiyo daga bakin kofa aunty ta juya da sauri qirjinta na bugawa fiyye da kaida ummah ta gyada mata kai "haka n abinda kikaji na fada shima an canza masa tunani har ma dana iyayensa ahankali ta tako ta dafa kafandan aunty dake kallonta a tsorace cikin tsananin tashin hankali ." Ummah ban gane ba me kike qoqarin fad a min ? abinda kika ji shi na fad a miki balkisu yusif ya koma wajen shukura inna lillahi wa inna ilahi rajiun shi kawai tayita fad a tana maimatawa nan da nan yanayinta ya sauya ta zauna shiru taji duk wani kuzari na jikinta yayi kasa tsawon mintuna talatin sannan ta bud e bakinta da kyar tace shima yusif din ya koma wajensu "Ki kwantar da hankalinki babu abinda allah bazai iya ba kuma in sha allahu allah zai kai maryama matakin da ba'a s allah yasa hakan shine mafi zama alkhairi arayuwarta ummah ta zauna ta dinga tausar aunty da maryama tana bata baki har aunty ta saki ranta sai dai hawaye yaki tsayawa umma ta qara da tabbatar masu duk runtse maryama bazata auri muktar ba Maryama ta rungume ummah ajiknta na gode umma dan allah karki bari a aura min shi wallahi na hakura da auren ma har abada bazaki hakura da aure ba akan wani dalili domin duk dan sunah baya gudun aure yadda akayi aure aka haifeki in sha allahu kema zakiyi aure har ma da ya ya da jikoki ummah ta fad a tana shafa bayanta suna cikin wannan hali habib ya shigo aunty tayi sauri ta goge hawayenta tana daidaita natsuwarta ganinsu haka ya fahimci akwai damuwa dan haka da hanzari ya qaraso ya riko hannun aunty cikin nashi yana tmbyarta lafiya na ganku haka ?babu komai aunty ta basu amsa ya babu komai ?ya kalli ummah fuskasa dauke da tambaya . Me yasa zaku boye masa yana da kyau ya sani ko babu komai zai taya yaruwarsa addua nan ummah ta fad a masa komai shiyasa nace ta hakura da batun wani aure ,bafa dole sai mutun yayi aure zai shiga aljanna ba kul kar na sake jin ka fad a haka zatayi aure musa aranmu dukkaninsu babu mijin aurenta acikinsu mu godewa allah da yasa har tana masu sonta baa barta haka ba babu abinda zai zo da bazai wuce ba wata sai labari ahankali ummah ta shawo kansu suka shiga wata hirar , ****** Kwanakin dari kenan da auren su maryam wanda yayi daidai da kwanakin sabain da tarewar maryam a gidan ata acikin lokacin babu wani abu da yayi sauki acikin zaman auren mai dadi a tsakanin maryam da ata duk abinda maryam zatayi domin ta cire kiyayyarta a zuciyar ata tayi amman ko a jikinsa domin dai yaki sakewa daita ."shiyasa damuwarta ta qaru zamansu babu wani shaawa dan ata yaki rungumar marym sai ma kyma da nuna ko in kula ." Sosai motocin jami'an tsaro guda hud'u dake gaba da bayan motar da ata ke zaune aciki ke falfala gudu akan titi kamar suna gasar tsare baka jin komai sai jiniya mai tsanani domin a kauce abasu hanya sosai motocin dake Kan titi suka dinga komawa gefe suna basu hanya wanda adaidai wannan lokacin maryam na can tsaye acikin kitchen tana kwashe abinci tana zubawa a kuloli ." Bayan ta gama ta jerasu akan table duk abinda take cikin hanzari take yi kar oga ata ya shigo bata gama ba duk da ba abincinta yake ci ba sai maakatan gidan ke ciki kuma idan tayi lattin ganawa yaci ubanta ,qarar jiniya taji alamar dawowarsa dan zaro ido tayi tare da daga kai ta kalli agogon dake manne a parlour'n karfe takwas da minti ashirin cikin sauri ta haye sama ta shiga dakinta wanda ya sha gyara gwanin burgewa. ta cire kayan jikinta ta daura towel sannan ta nufi bayi ." Cikin jin isa ya turo kofar parlour'n tare da shigowa babu kowa a parlour'n jakar dake hannunsa ya ajiye akan kujera da wayoyinsa sannan ya nufi sama yayinda zuwa wannan lokacin maryam ta fito tana tsaye a gaban madubi tana shafa lip's dinta byn ta gama ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka can zuciyarta ta bata umarnin ta saka marasa nauyi tun sanda ta tare a gidan tsawon sati tara kenan atamfa da dogayen riguna take sakawa ta sanya kaya marasa nauyi masu yanayi dana bacci yana tsaye a dakin yaji an turo kofa bai juyo ba ." cike da faraa ta tsaya a gabansa tana cewa "oyoyo baby sannu da zuwa "wani kallo yayi mata a dage yana sake tamke fuska tmkr yaga wani mugun abu cike da sanyin jiki ta kallesa ganin yadda yayi mata kallon kaskanci "leave my side ya fad'a yana nuna mata kofar fita yayi maganr cikin bacin rai bata wani damu ba tunda idan da sabo ta saba da halinsa "ga abinci "bana ci kina tunanin zanci abinncikin ne ko me ? kayi hakuri please kaci ko kadan ne na sha wahala sosai kafin na gama bai ce mata komai ba ya juya ya bar parlour'n. Wani bakinciki ta dinga ji acikin ranta "oh ni maryam me zan yiwa wannan bawa naka na canzashi?gani bata da abinda zatayi yasa taja kafafunta ta koma dakinta ."ta fad'a kan katifa wasu hawayen bakinciki na zuraro mata nasihar sister ce ta fado mata "maryam kinsan yadda akayi auren nan hakuri zakiyi da Adam idan kina son kici riba ,auren da kayi dan soyayya ma hakuri kake yi bare wanda iyaye suka had'a zaman aure dan hakuri ,gidan aure makaranta ce mai girma ba zaka gane hakan ba sai ka shiga, akwai darussa kala dabam dabam sai kin zauna acikinsa zaki fahimta."wasu hawaye suka qara tsiyayo mata yanzu haka zata qare rayuwarta cikin hakuri "tunda kina son shi dole zakiyi hakuri dashi ."zuciyarta ta bata amsa da hakan . Mmn sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 10 Ahankali ta yunkura ta mike tsaye kamar wata mahaukaciya ta soma zariya acikin d'akin tana sambatu "yanzu me zan masa na kawowa kaina kwanciya hankalin acikin gidan nan ?tayiwa kanta tambayar tana mai qara shiga tashin hankali "babu abinda zaki iyawa wannan mai shegen taurin kan da zaki burgesa ,komai zaki masa a banza ne a wajensa "tayi shiru na minti biyar tana tunani kafin ahankali ta qarasa inda wayarta take ajiye, ta kai hannu ta d'auka tana tunanin kiran d'aya daga cikin yan'uwansa wani tunani tayi sai kuma ta fasa kiran domin dai tasan kowa a cikinsu abu d'aya yake fad'a mata shine hakuri hakuri !! kuma yanzu da zata kirasu hakurin dai zasu bata ." "bana son wannan hakurin gashi kuma hakurin dole zanyi tausayin kanta ya kamata tana mai jin kamar duk ita ta jefa rayuwarta cikin matsala a dalilin zunzuruntun qaunar da take masa da taki auren tun farko data zauna da rayuwarta lafiya ."yanzu me zanyi ?ta sake tambayar kanta tana cure hannuwanta waje d'aya "idan da hali ki sake zuwa wajensa ki kwantar da kai tunda kece a kasansa "da sauri ta girgiza kai alamun shawarar bata yi mata ba "wallahi da zan cire kulafucinsa nayi hakuri na bar rayuwarshi da komai zai zo min da sauki "ta sake bawa kanta wannan shawara "amman ina bazata iya ba dan tana da kulafucinsa tana mutuwar son shi kamar yadda yake mugun kinta murmushin takaici maryam tayi tana cewa "Allah kasani ina wa adam wani irin so mai girma, allah ka nuna min ranar da zai soni kamar yadda nake sonshi dan zan s faruwar haka." "burina a koda yaushe mu kasance a matsayin miji da mata kamar sauran ma'aurata dan haka maryam karki gaji da halin mijinki kije ga mijinki baki san abinda allah zai yi ba wata rana sai labari ga kuma alqawarin da kika d'aukarwa mahaifiyarsa kuma mami ta yarda dake shiyasa ma ta baki amanarsa da wannan shawar ta fito daga cikin d'akin cike da sanyi jiki ."bayansa ta hango yana taka step ahankali yayinda hannuwansa duka ke cikin aljihun wandonsa kunnensa manne iPod ."kai tsaye bayansa tabi yo tana kallon yadda yake taka step yana wani rangaji." alamun taku yaji abayansa ya waiwaya ya kalleta sannan ya juya ya cigaba da taku ,yana gama sauka ya samu waje ya zauna akan d'aya daga cikin kujerun parlour'n ya d'aura kafarsa d'aya akan d'aya yana cigaba da wayarsa "karka qara min damuwa ammar akan
Chapter 30 · 0% Book details