← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 105

Sashe 16

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

haka nake ji , suna tautaunawa mansor ya dawo hannunsa rike da textbook ya mikowa ata." Ya kar ba yace mansor ai yagewar ba wani mai yawa bane kayi hakuri kaji yarona kaiwa mamanku zata gyara maka yaron ya juya zuwa dakin amira sun jima suna tautaunawa har karfe shabiyu sauran sannan ata ya bar gidan zuwa gidansa dake lekki ." Ita kuwa maryam tana nan zaune har karfe goma sha daya ta wuce babu ango babu labarinsa ga tsananin bacci tana ji amman ta kasa ko kifta idanunta saboda tsananin tsoro jiki a sanyaye ta dauki wayarta ta kira mami "maryam ya akayi ya bakunta? adamcy ya shigowa kuwa ?"a matukar razane maryam ta dago ta kallon dakin ,sai kuma ta maida kanta qasa kamar tana gaban mami yayinda idanunta suka qara canza kala sakamakon qwallar data soma dan taruwa mata." cikin faduwar gaba mami tace "me ya faru maryam ko bai shigo bane ? "mami bai shigo ba gashi tsoro nake ji mai matukar azabar Idan bai shigo ba bazan iya bacci acikin gidan ni kadai raina ba " ajiyar zuciya mami ta saki"oh my god adamcy ,Allah yasa kar ya kasheni ,kawai dan anyi maka auren da baka so shine zai zama matsala ka dinga wulakanta mutane haka?maryam Kiyi hakuri nasan dole zaki ji babu dadi ko bama dan tsoro ba ki qara hakuri kamar yadda na fad'a miki bazaki taba bakinciki da auren nan ba ki barni dashi nasan yana sane zan sashi yasan aikinsa dan haka ki manta da adamcy kinji kiyi zamanki babu abinda zai sameki ga masu gadi nan bazasu ta'ba yarda wani ya shigo ba ,kinyi haquri ina tabbatar miki adamcy zai shigo komai dare ." Cike da girmamawa tace "to! mami na gode sosai allah yasa kifi haka allah kuma ya bar min Ke mami ina sonki "nima haka maryam bye take care."yana zaune a parlour n gidansa dake lekki phase 1 anjus avenue yana zukar sigari wayarsa ta soma ringing ya kai hannu inda ya ajiye wayoyinsa ya lalubo yana dubawa sunan sweetheart ya gani yana yawo a screen din wayar shiru yayi ya cigaba da kallon wayar yana zukar sigari gbdy yaji gabansa ya shiga faduwa dan bai san me zata fad'a masa ba idan ya dauka dan haka kiran na katsewa ya kashe wayoyinsa gabdaya ya kwanta rigingine yana kallon saman parlour'n yana cigaba da zukar sigari sai daya tashi da kwali daya sannan ahankali bacci yayi awon gaba dashi ." Bangaren maryam kam karfe uku na dare bata runtsa ba har garin allah ya waye bata ko kifta idanunta ba balle tayi bacci yadda taga rana haka taga dare tausayin kanta ya kamata shi kuwa ata ko tunaninta bai yi ba dan babu digon tausayinta acikin zuciyarsa karfe shida daidai ya tashi ya shige bedroom dinsa ya shiga bathroom yayi wanka yayi alwala yazo ya gabatar da sallah bayan ya idar ya koma saman gado ya kwanta idanunshi na kallon saman d akinsa cikin kankanin lokaci bacci ya daukesa ." Karfe takwas daidai a gidan maryam tayiwa mami direba bai gama daidaita parking ba ta fito tana addua" Allah na rokeka ka kawo min sauki acikin rayuwata ka kawo min karshen wannnan damuwar "ta qarasa fada tana dafe goshinta ta tsaya a bakin kofar parlour n tana kiran sunan maryam "maryam !! mami ta shiga kwalla mata kira da sauri ta miqe a rude ta sauko ta bude mata kofar parlour'n mami ta tura qofar ta shiga,yanayin fuskarta kawai ta kalla ta tabbatar mata ta sha kuka har gaji "ina adamcy yake ?cikin mutuwar jiki ta bud'e baki "ammm uhm baa gida ya kwana ba yanzu Ke kadai kika kwana a gidan nan ?ta gyada mata kai idanunta na kawo ruwan hawaye "ina masu gadi ?"suma tun jiya da misalin karfe goma ban sake jin motsinsu ba. mami bata san sanda ta fashe da kuka mai tattare da tausayinta ba ,da sauri cikin rawar murya mrym tace"dan allah mami kiyi haquri ki daina masa kuka sai wani mummunar abu ya samesa maganarta ta katse mata kukanta saboda yadda taga tashiga tashin hankali ta zubawa fuskarta ido, kawar da kanta tayi gefe tana qoqarin boye damuwarta dan hankalin mami ya kwanta kusan minti biyar kafin mami ta soma neman layin ata Karfe goma daidai ya tashi wanka ya sake yi ya shirya cikin kananan kaya ya kunna wayoyinsa yana gama kunnawa kiran mami ya shigo. jiki a sanyaye ya dauka yaji tace "ni kuwa uwar data kawoka duniya ce ?wani irin tsinanne yaro ne kai ? cike da tantamar ba mahaifiyarsa bace ta kira numbersa,amman dan ta tabbatarwa kanshi sai ya cire wayar a kunnensa ya duba yaga tabbas sunanta ne sannan ya kuma karawa a lokacin da muryarta Ke cigaba da fadin"wai ni kam sa'arka ce adamcy ? lallai na sakar maka da yawa kaga gadon barcina,wallahi sai na dauki tsatstsauran mataki a kanka kamar yadda yayana suka bani shawara "jin sunan yayanta kawai data ambata yasa shi dauke wayar daga kunnensa yana kiran sunan Allah yau shi sweetheart ta kira da kalmar tsinuwa wani irin tsinanen yaro ne kai ? ya sake maimaitawa kanshi cikin tsananin tashin hankali." tabbas akwai wani mummunar bala'i na daban dake son kunno kai cikin rayuwarsa ." Yana tsaye cikin wannan tashin hankali kiran mami ya sake shigowa jiki a sanyaye ya dauka "kazo ka same yanzu yanzu ina gidan ina jiranka, sha sha kawai da bai san ciwon kanshi ba ,iska kawai iya fesarwa daga bakinsa ya kwashi wayoyinsa ya fito masu tsaronsa na ganin fitowarsa duk suka mike ya shiga mota suka fice a guje tare da jiniya cike da mutuwar jiki ya shigo parlour'n batare daya kalli inda maryam take ba dan gaba daya idanunshi na Kan mami n wacce kallo daya yayi mata yasan tana cikin tsananin damuwa amman km zuciyarsa babu digon nadamar abinda ya aikata bare tausayin maryam sai ma tarin qiyayyarta data ninku acikin zuciyarsa ." "sweetheart ta kasa ganewa tursasa zuciyarsa da take akan yarinyar Ke sake hura wutar qiyayyarta acikin zuciyarsa ,ahankali ya samu waje ya zauan kusa da mami yana cewa "ina kwana sweetheart!dakata adamcy bana bukatar wata gaisuwarka" shiru yayi kawai yana kallonta yayinda yaji kanshi yana masa wani irin sara ,"ni zaka wa haka ko "? bai ce mata komai ba illa ya kalli inda maryam take zaune ya daka mata tsawa " ke tashi ki bar nan". ta mike da tsaye da sauri jikinta na rawa zata juya mami tace "Ke koma ki zauna " maryam ta girgiza wa mami kai hankalinta a tashe ." "ni nace ki koma ki zauan babu inda zaki , ai ya raina ne shiyasa tunda ina masa fad'a dole ya huce akanki "no sweetheart ni ba haka nake nufi ba but at least ai.. "na rantse da girman allah idan ka sake kwana a wani gida ba gidan nan inda matarka take ba babu ni babu kai har abada kuma ko mutuwa nayi karkazo Kan gawata zan sheidawa ya'yana kowa ya sani "haba sweetheart Kiyi hakuri mana "nace kayi min laifi ne bare ka bani wani hakurin banza ? "Ina baki hakuri ne dan kin janye maganrki "to bazan janye ,ba dai ka raina ni ba to wallahi bazaka qara jin dadina ba haka kawai ka dinga gana min azaba kana ganawa yarinyar mutane azaba, laifi ne dan ta rufa maka asiri ta aureka? "wace azaba kuma sweetheart yarinyar da babu abinda ya taba hadani daita ya qarasa maganar yana kallon maryam"ke nace ki bar nan ko ?"ta tsaya tana kallon fuska mami ya sake mata alamar ta bar gun akaro na biyu a matukar fusace ya mike tsaye "Ke kina hauka ne ina mgn kina zaune ? ya buga mata tsawa " "babu fa inda zata karki sake ki bar wajena matsawar bani nace ba "wai sweetheart me nene haka n ?ya fad'a yana sake kallon maryam dake qoqarin komawa ta zauna yace "wallahi kika cigaba da zama a wajen nan sai na canza miki kamani"maryam ta kalli mami cikin tsananin tashin hankali tace "mami dan girman allah kiyi hakuri ki barni na bar wajena" ai kafin mami ta sake cewa wani abu tuni maryam ta bace . mami tayi shiru ta zuba tagumi tana dubansa kawai domin ta rasa me za tayi har kusan mintuna goma sannan yace "sweetheart kinyi shiru kina kallona "me zance tunda kafi karfina ka rainani ka nuna min ban isa da kai ba ,duk lokacin da nace ga abinda zakayi bazakayi ba , amman wallahi bazanyi kaffara ba muddin baka cigaba da kwana a cikin gidan nan ba na rantse da girman allah babu ni babu kai har abada kuma zan cireka acikin ya'yana sai dai ka nemi wata uwar amman bani zulai ba ." Mmn sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 6 "Wai meye haka ne sweetheart ?"dan Allah ki daina fad'ar wannan maganar, karki manta nine fa d'anki wannan yarinyar kuma diyar wasu ce " me yasa zaki dinga fad'ar wad'an kalaman akaina?me yasa zaki min wannan hukunci ?ya fad'a cikin tsananin 'bacin rai tunda wannan hukunci kika zartar akaina ai gara ki kasheni kawai ki huta nasan bani da gata da galihu just kill me sweetheart ko kuma ki janye wannan hukuncin naki ." yayi maganar Kmr zai yi kuka ." "Okay haka ma zaka fad'a ko ?ta daka masa tsawa yana qoqarin sake bude baki mami ta zuba masa lafiyayyen mari tana cewa "kaji magana kawai sannan kayi abinda nace kuma bazan janye kudirina ba wannan umarni ne na baka wallahi idan ka kuskura ka sa'bawa umarnina zaka ji abinda yafi haka daga bakina." Maryam dake tsaye akan step a tun sanda ta bar wajensu jin saukar mari yasa da sauri ta dafe qirjinta saboda tashin hankalin data tsinci kanta ciki ,ta qara taku biyu idanunta ya sauka akan mami da ata dake huci tmkr zakuna
Chapter 16 · 0% Book details