Sashe 22
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sanyaye ta mike ta soma d aga kafafunta tana zubar da hawaye har ta kai bakin kofa taji motsin takunsa alamun yana haurowa da hanzari ta koma da sauri tana jin fad uwar gaba tsayuwarsa ta gani a bakin kofar yana cewa Ke ina kwalin sigarina? muryarta cike da in ..ina tace amm uhm na ..na .. sai kuma tayi shiru ta kasa qarasa mgnr dan tasan tana fad a masa ta zubar a shara sai ta gane bata da wayo ya qara taku biyu ya shigo cikin d akin sosai yana mata wani irin mugun kallo wanda yasa hantar cikinta kad awa ina kwalin sigarina ?akaro biyu don t let me repeat my self . Na ..na zubar a shara ta fad a hawaye na ganga rowa bisa kuncinta what !? ya fad a a matukar tsawace tayi baya da sauri ta manne da bangon d akin tana bashi hakuri kayi hakuri dan allah . sigarin nawa kika zubar ashara saboda Ke dakikiya ce ?bansan cewar baka gama dashi ba amman kayi hakuri numfashi ya fesar tare da rike kugunsa ya taka ya isa bakin window ya yaye labulan window yana kallon haraban gidan masu tsaronsa ne suke shawagi da alamun sun gama shi kawai suke jira ya saki labule da karfi wanda yasa maryam ta firgita cikinta ya duri ruwa. fuskarsa a murtuke yace ki tabbatar kin nemo min sigarina kafin na dawo gidan nan idan ba haka ba wallahi wallahi ki kuka da kanki yana fita kamfani ya nufa . cikin hanzari suna isa ya fito. kai tsaye ya d auki hanyar comfrence room domin wata gagarumar matsala dake son kunno kai cikin kasuwancinsa kuma tunda ya sanarwa P.A dinsa yasan by this time shi kad ai ake jira yana shiga ya iske kowa kamar yadda yayi expecting har ma da ammar da hisham cike da girmamawa manya ma aikatan da dake zaune suka dinga gaishesa tare da qoqarin kashe wayoyinsu dan sun san dokarsa idan yana magana baya son jin motsin kowa bare qarar waya ya mikawa ammar hannu batare da ya kalli inda hisham yake ba shima kuma bai kallesa ba . ya samu waje ya zauna. sun dade suna tautaunawa da manyan ma aikatansa domin kawowa kamfanisa cigaba ahankali P.A dinsa mustapha umar hassan dinsa ya mike ya kawo masa coffe karfe biyu daidai ya sallame kowa shima ya fito tare da ammar suka nufi massalacin dake cikin kamfani yana bawa direbansa umarni cikin harshen tsadadden turancinsa su juya kan motoci fita zai yi da zarar ya fito . Ina kuma zaka ?zanje naga sweetheart dina ya fad a cike da jin fad uwar gaban da bai san dalili ba a natse suka qarasa wajen yin alwala suna magana kasa kasa ATA yace share maganar hisham kai bakasan abinda yayi min ba muddin kaga mun dawo kamar da to naga auta kuma naga kwanciyar atare daita bayan sun idar da sallah ammar ya rigasa fitowa ya tsaya acikin wata runfa rungume da hannuwan sa a qirji yana jiran fitowar ata yana tsaye ya hango bayan maryama idanunshi kyam akanta har sanda ATA ya qaraso ya tsaya kusa dashi yana cewa me ya d auki hankalinka da kayi concentre haka ?zubin halitta mai kyau nake kallo ya bashi amsa da haka kana ya cigaba da magana kalli can abokina ka gani tsayuwarta ma kawai abun burgewa ne . ATA yaja tsaki yana cewa nonsense ! ba tsaki zaka j ba ka kalla ka gani kai kanka zaka fahimci abinda nake nufi, yarinyar da nake fada maka ce, ata da yayi niyyar kallonta ya fasa ya cigaba da kallon ammar fuskar tashi nan babu wani annurin kirki sai dai bugun zuciyarsa ya qaru sosai fiyye da duk wani tunanin mai karatu maryama mai kyau !Ammar ya kira sunanta saurin juyawa ATA yayi yanayin bugun zuciyarsa bai saisaita ba, maryama kuwa juyowa tayi ahankali sanye cikin kanki bautar kasa ta nade kanta da qaramin hijab kayan sun matukar yiwa jikinta kyau mr ammar ta hango tare da bayan wani tsaye . Mai kyau qaraso mana mu gaisa tayi murmushi wanda yake qara tafiyar da imaninmu mutun ahankali ta soma takowa zuwa inda suke tsaye tana wata irin tafiya da mutane suke ganin tsabar yanga ce tayi mata yawa nan kuwa rashin kibar da bata dashi n ya janyo haka kalleta abokina gashi tana nufomu zaka fi qare mata kallo sosai wallahi yriyar ta had bazan kalleta ba tunda ta had u ka aureta mana ,duk kabi ka damu mutane Kmr wanda bai ta ba ganin mace ba bai fi sauran taku biyu ta karaso zuwa inda suke tsaye ba ATA ya soma d aga kafafunsa bai tsaya akoina ba sai a inda motarsa take tun kafin ya qaraso masu tsaronsa sun zagayesa . Murmushi kawai ammar yayi yana d auke idanunsa daga kallon bayan ATA mr ammar barka da rana ya fama da jamaa ?tayi mgn a natse cikin sanyayyar muryarta na kusan sumewa da wannan murya fa maryama ta d an zaro ido tana cewa wace ni dan allah ka rufa min asiri kar madam tasamu wannan labarin na shiga uku na mu shi uku dai ya fad a had e da murmushi, cikin marairaicewa tace kaji ba ashe kaima tsoronta kake ji yasa dariya adaidai lokacin da motocin ata suka fice yayinda ammar ya cigaba janta Kmr yadda ya saba . kai tsaye abdullahi estate ata yace a wuce dashi ana gama daidaita parking ya fito ya nufi gidan mami tana daga zaune taji ana yunkurin bude kofar ta tsaida idanunta akan kofar dan ko baa fad a mata ba jikinta ya gama bata d an lelenta ne ke tunkarota a natse ya turo kofar ya shigo kana ya maida kofar ya rufe akan mami idanunshi suka fara sauka bayan ta kallesa ta d auke idanunta akanshi zuwa wani gefe tana jijiga kafarta tayi tmkr bata ji dadin ganinsa ba alhalin kuwa wani farinciki ne ya mamayeta domin tun da ta gansa tasan tayi winning yazo ban hakuri ne . Ahankali ya tako zuwa inda take zaune akan kujera wanda zuwa lokacin tunin ta runtse idanunta durkusawa yayi a gabanta yana sauke numfashi tare da d auran hannuwansa akan gwiwowinta Kiyi hakuri sweetheart ki yafe min nasan ban kyauta miki ba ,ban san abinda yasa na aikata haka ga mahaifiyata ba wacce bani da kamarta ,duk duniya itace take dani nake daita. nan da nan hawaye ya jike gashin idanun mami yanzu zagin wad an da suka manyanta a zamaninku ya zama wani abun ado shiyasa kayi min son ranka kuma agaban matarka , me kake tunani idan ba maryam ka aura ba ? kaga kenan ka siya min raini ne a wajenta ko kuma nuna mata kofar yi min abinda ta ga dama . sweet heart na aikata hakan ne abisa kuskure amman kiyi hakuri dan allah ta d aura hannunta a saman nashi kawai batare da ta sake cewa komai ba tana jin tsananin qaunarsa . Kiyi hakuri kiyi min addua sweetheart ko allah zai sa min son diyarki a zuciyata ko kad an ne , sweetheart har yanzu na kasa manta mafarkina ina tsananin sonta gashi bansan inda zan sameta ba sannan duk yadda naso na cireta araina na manta daita na kasa manta komai nata . bugun zuciyarta, numfashinta fuskarta da kamshinta idanuwanta murmushinta hawayenta sautin numfashinta sweetheart bazan boye miki ba na sha saduwa daita acikin mafarkina . Mami ta tsura masa idanunta tana kallonsa na fara shan sigari duk dan saboda ita haka zalika a qoqarin na manta daita ne na fara shan giya ina danne zuciyata akanta ,nayi iya yina domin na manta daita amman wallahi sweetheart abun yaki aiki har yanzu koina na juya ciwo nake ji acikin zuciyata mami tayi shiru zuciyata cike da tsananin tunani abu daya ne yayi mata dadi acikin magangunsa shine rokon adduarta na allah ya saka masa son mrym ko kad an ne wannan abu ya sanyaya zuciyarta kuma daman tana wannna adduar . Sweetheart nifa abun tausayi ne abun a tausayawa ne akwai ciwo mai zafi acikin qirjina bana buqatar tausayawar kowa sai taki kece kawai zaki tausaya min domin kece kawai kika san ciwona kuma kece kawai kike sona tsakanin da allah. mami ta numfasa tana cewa adamcy nah ina tsananin sonka da tausayinka kai ma ka sani .. na sani sweetheart amman akan yarinyar nan kin canza min koma nace kinfi sonta akaina,mami ta kallesa kawai sweetheart ki janye maganarki akaina zan cigaba da rayuwa daita Kmr yadda kika bukata amman batu na samammarta farinciki babu shi domin ni kaina zuciyata baa cikin farinciki take ba dan haka dan Allah ki janye magarki akaina . Ta girgiza kai alamun a sweetheart kin janye dan idan nayi kuskure kin bin umarninki wani abu zai faru dani idan kuma wani abu ya sameni kece kike da asara sam ita ba asararta bace kina ji kuma kina gani zata komawa wani ta bar miki d anki da rayuwar daya tsinci kanshi . muryarta a sanyaye tace babu abinda zai sameka adamcy kuma Ina rokon Allah ya kawo maka saukin abinda Ke damunka "ta qarasa fada tana rufe fuskarta da tafin hanunta hadi da rushewa da kuka . why sweetheart me yasa zaki min asarar hawayenki bayan kin min addua? addua nafi bukata daga gareki kuma kinyi min na kuma gode Kiyi haquri don Allah ki daina kuka ni dai kin janye furucin ki akaina na janye kai ma kuma kayi min alqawarin bazaka takura rayuwar maryam ba . dan allah ka barta tayi farinciki a gidanka wallahi bancin mutane zasu zageni da na raba aurenku kowa ya huta sweetheart babu mai zaginki kuma da zaki min haka wallahi da naji dadi da samun kwanciyar hankali uhmm adamcy taa girgiza masa kai kayi hakuri kawai adamcy zan maka addua kamar yadda ka bukata ya sauke wani numfashi yana mikewa ya zauna gefenta ya zauna yana kiran sunanta . sweetheart! ina jinka adamcy ina son zan qara aure bazan hanaka qara aure ba adamcy amman dan allah ka bari zuwa nan gaba kad an dan bazan ta ba yarda ka shigo da wata gidanka ba alhalin diyata bata da matsayin komai a wajenka