← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 105

Sashe 52

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wasu abubuwa daga ciki ba ta zauna rike da littafin tana qoqarin dubawa wayarta ta fara ringing dan haka ta ajiye ta d auki wayarta kiran mahaifiyarta ne . Har karfe goma shadaya na dare maryam na zaune tana jiran dawowar ATA sai dai shiru bai dawo gida ba, karfe shabiyu daidai ya shigo tana jin motsin shigowar motocinsa ta zabura ta mike tare da adduar neman saa jikin labulenta ta qarasa cikin sauri taga yana tafiya har sanda ya nufi kofar shigowa ta saki labalen tana cewa ya Allah ka bani sa a akan maganin nan bakin kofar d akinta ta dawo ta labe tana kallonsa ya bud e kofar dakinsa ya shiga batare daya zare key ba wanda ga dukkanin alamu ya manta ne sadaf sadaf ta bud e kofar d akinta ta fito ta tura kofar d akinsa ta leka baya nan sai kayansa ta hango akan katifa alamun ya shiga wanka ta janyo kofar ta rufe ahankali sannan cike da tsoro ta cire key d aya acikin key n dakinsa tayi wuf ta fad akinta ta kulle tana dafe qirjinta da hannuwanta duka tare da furta. allah na gode maka da kabani wannan saar gobe da safe yana fice wa daga gidan zan shiga nayi abinda zanyi kai maryam mai yasa zaki dogara da irin wadan nan abubuwan wannan fa shirka ne qarara zaki aikata domin tukun yar tsaf ce ummah ta aiko miki dashi rayuwar nan fa babu tabbas babu yadda allah bazai yi ikonsa ba qaddara kuma tana fadawa bawa daidai yadda allah ya hukunto masa amman addua itace mafuta cikin ,rayuwar aurenki da Adam qaddara ce ki cigaba da hakuri zama dashi haka sarewa ta kalli mukulli hannunta kafin ahankali ta kira wayar mahaifiyarta ta koma can karshen dakin tana dauka tace umma abin nan kuwa zan iya sakawa yaya Adam shi ? bana son abinda zanyi na cutar dashi ,sannnan hakan nan wannan aikin yake bani tsoro tun da kika fad a min zai iya mance har mami tsoro ya shigeni ,rayuwar mami babu Adam akwai damuwa bugu da qari ta damqa min amanarsa idan na cutar mata dashi allah bazai barni ba ina so mana umma ina son nayi rayuwa mai dadi dashi domin hakan yana da mahimanci ga rayuwata ko sau daya ya soni ya furta ya kuma kula da rayuwata bangaren ummu kuwa cewa tayi tunda kina son faruwar haka ki manta da wata uwarsa Ke Kinsan irin nata mulkin datayi lokacin mahaifinsa ?tayi mulki kuma har yanzu tana kai haka kawai take juya kowa son ranta ?dan haka kiyiwa kanki adalci ki cire wannan tausayin Kiyi abinda ke gabanki domin raba zuciyarki da nauyi wallahi ummah ina jin zafi har acikin raina ace sai nayi asiri yaya Adam zai soni ta qarashe maganar tana zubda kwalla mai zafi bata jin zata iya daukar wannan nauyi dole kiyi tunda soyayyar da kike masa da biyyya tare da hakurinki bai yi miki amfanin komai ba ,ke bari na fad a miki wani abu ko Adam nason aurenku dole sai kin tashi tsaye akanshi dan irin masu taurin kansu sai da asiri ake samun kansu Kiyi qoqari kawai ki saka tukun yar nan da zarar ya kwanta aiki ya fara kenan sai dai wani Adam din bashi ba zai fad a wata duniyar ta dabam lokacin da zai dawo kin tara masa yaya masu yawa .tana gama fad ar hk ta katse kiran . Yana fitowa daga wanka cikin sauri sauri ya soma shiri dan tafiya ce ta samesa zuwa kasar ingila karfe daya da wasu yan mintuna jirginsa zai tashi bai sheidawa kowa ba har mami ya fito da wata yar qaramar jaka ya kama hanya ya fice ya bar gidan washegari maryam bayan ta gama gyara gida ta bud e dakinsa ,tana kallon dakin , da mamallakinsa na nan bata isa ta tsaya cikinsa cikin natsuwa ba gaban mirrow dinsa ta qarasa ta tsaya tana duban frame din hotonsa cikin hadadden suit baki idanunshi manne da farin glass ,tana kallonsa tana jin yadda zuciyarta Ke sake narkewa akan son shi wata irin soyayyarsa Ke ratsata bata ta ba son wani halitta kamar yadda take son shi ba . ta kai hannunta ta dauki freme din ta rungume ajikinta tana mai lumshe idanunta akanka na aikata manya manya laifi masu muni da tsayawa arai me yasa bazaka sauko ka karbeni ba ? wallahi ina sonka da sonka na rayu tun tsawon rayuwata soyayyarka bata misaltuwa yaya adam, a baya nayi babba kuskure a yanzu kuma zan sake tafka wani kuskure akan Kuskuren baya ka sausauta min zuciyata bazata cigaba da bugawa ba idan har babu kai ka soni batare da na aikata wani laifi ga mahaliccina ba Sorry maryam adam fa yayi nisa a qiyayyar ki bazai ta ba sonki ba karki mata kalamansa na shekaranjiya ai tunda kika nacewa aurena ni ne zanyi sanadin mutuwarki dan tun tuni naji rashin alkhairi akan aurenki kinga idan kin mutu ni kuma na tsinci kaina a prison hankalin ke da sweetheart zai kwanta amman tabbas ina ji ajikina idan baki kasheni ba ni zan kasheki . Tabbas zai iya komai dan kawar dake a duniya saboda tsananin kiyayarsa gareki kiyayyarsa tun fil azal ce wato tun ran gini tun ran zane karki cutar da kanki gara Kiyi amfani da komai ya zama mallakinki na har abada ,amman kuma duk daren dadewa asiri zai karye maryam ga laifin asiri ga hakin mami akanki ko ba dade hakinta zai bibiyi rayuwarki ranar nadamarki na zuwa kuma alokacin nadamar bazata yi miki amfani ba jikinta yayi sanyi tana zubar da hawaye tana makale da hotonsa maryam ki bar wannan tunani a yanzu yadda yaya adam zai soki shine mafuta agareki ,ki dauko tukun yar ki saka ki kama gabanki jiki a sanyaye ta ajiye freme din hannuta taje ta d auko tukun yar ta daga katifa tasa sannan ta gyara masa d aki tsaf ta fito ta kulle ta zare key ta koma dakinta ta shiga yanat gizo . Maryam batasan da tafiyarsa ba ta dai zuba ido taga dawowarsa mami kam tun a daren jiya taji batun tafiyarsa ,ranta yayi matukar baci sakamakon rashin fad a mata da bai yi ba amman kuma hakan bai hanata yi masa addua da fatan alkhairi arayuwarsa ba , bangaren maryam kuwa hankalinta yayi matukar tashi ganin bai dawo ba har washegari batayi tunanin tafiya yayi ba ta d auka yaji yayi mata kamar yadda ya saba ,hankalinta a tashe ta kira mahaifiyarta ta sheida mata halin da ake ciki ki kwantar da hankalinki tabbas kaidarsa kwanaki uku ne zai tashi aiki amman akwai mafuta dan zaa iya yin wani sabon aiki irinsa umma? Eh mana irinsa zaayi wannan maganar ya kwantar da hankalin maryam ta cigaba da tsabgoginta tunda tana da wuta kuma tana da keyn kitchen a hannunta burinta ya dawo ya bud akinsa ya kwana akan gadon . Washegarin ranar da ya cika kwanaki bakwai nana hauwa u ta kirata ta fad a mata qawarsu safiya ta haihu har jibi suna dan haka jibi su hadu a gidan safiy daga suka hira inda nana hauwa u Ke tmbyata ko yayanta ya dawo ?bai dawo ba har yanzu ,sister kina ganin bancin na sace keyn kitchen ba niyyar kasheni yaya adam yayi ba kamar yadda ya fad ? nana hauwa u tayi murmushi bazai ta ba kashe common sauro ba bare mutun wannan duk fad a yake kuma tunda akwai waya a hannunki kuma akwai wuta a gidan duk zai zo da sauki ba kamar kwanaki ba koni da kaina zan dinga zuwa ina kawo miki abinci sun jima suna hira a tsakaninsu . Ranar da ya cika kwanaki goma cif sai gashi ya duro gidan tmkr mashi alokacin maryam na tsaye gaban madubi tana ta shek'a kwalliyar zuwa suna kamar wacce zata canja fuska, ta shafa wannan ta goga wancen ta dangwala wancen, ta d'auki lokaci me tsawo kafin ta gama,dan kwallinta ta d'auka ta d'aura, ta dauko takalmi hil tasa saida ta k'are ma kanta kallo ita kanta tasan tayi kyau dan ita bata ganin illar rashin tsawonta tunda akwai hil kuma duk tsadarsu tana siya sai dai idan bai mata ba tana murmushi ta d'auko mayafinta da jaka ta fito da zumar zuwa gidan suna a hanakali take taku kwas kwas saitin takalminta kenan tana gama saukowa qasa kawai taga mutun zaune a parlour n yana cire takalma ,a natse ya dago yana duban step sakamakon qarar takaliminta mai mugun tsini kallo d aya yayi mata gabad aya yaga ta canza shi da yake jiran ya ganta ta qanjame tsabar yunwa amman yaga tayi fresh . baki ya saki yake kallonta kafin ahankali ya kai dubansa ga kofar kitchen nan ya hango key kwaya d aya,wani irin tsoro ne ya shigeta nan take jikinta ya kama rawa wani irin numfashi ya sauke ya dawo da kallonsa gareta tun daga qasa ya sake daukar kallonta kafin ahankali muryarsa a can qasan makoshi yace "ke ina zaki? yau ne sunan wata k'awarmu da ta haihu shine zamuje tare da sister yana qarasa cire takalminsa ,ya mike tamkar zaki ya fara nufota yana cewa a ina kika samo extra key na kitchen?ganin yana nufota cikin wata irin tafiya mai daga hankali qirjinsa har wani dagawa yake duk wani taku da yayi sai zuciyarta ta buga da karfi . bai fi sauran taku daya ya qaraso gareta ba kawai ATA yaga tayi wuli da jakar hannunta ta saka wata razananniyar qara ta zube qasa tare da dafe kanta tana jujjuya shi cikin rashin jin tsoro ATA ya qaraso gabanta ya kai hannu da niyyar sauke mata mari yaji ta daka masa tsawa cikin wata irin kaukausar murya tana fadin kar ka kuskura ka taba mana godiyarmu. cak ya tsaya yana kallonta cike da mamaki hahhhh tashiga babbaka dariya cikin wata irin murya mai cike da ban tsoro tashiga fad wannan ba maryam bace daka saba duka kana wulakantawa nine aljanu gagare wato kai kullum tunaninka dukanta da wulakanta mana godiyarmu ,ka dauka bata da gata ne, ita din fa matarka ce ba baiwarka bace ,tana magana tana nufosa, ATA ya dan ja baya kadan yana qare mata
Chapter 52 · 0% Book details