Sashe 93
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fad'a tare da juyawa ya samu waje ya tsaya suka biyosa suka tsya kusa dashi suna dubansa bakinsu na son furta wani abu "salma ki rabu dasu kawai mu dai muyi yadda zata dawo daidai kafin wannan yarinyar ta gama takaba araba gado ,aunty salma ta saki murmushin jin dadi burinta zai cika "kai wallahi ina cikin farinciki saboda kaso mai yawa zaka samu sosai kuwa dan kaso biyu zanci tunda ni nmj ne "ya qarasa maganar cikin tsananin farinciki wannan kuma haka ne bari kama gabanmu su kuma suje su qarata da kukansu hawaye ne yayi masu yawa" wallahi nima allah allah nake lokaci yayi araba abani kasona inji cewar aunty hasana baba gali ya saki murmushi "ni Allah yasa a mallaka min kamfanin burodi gbdy aunty salma tasa dariya murna kmr su rungume juna a wajen ."baba gali da aunty salma suka fice suna dariya aunty Hasana ta shiga kitchen domin daurawa umma abinci dan tun daaka nemi sadam aka rasa kusan rabin yininta anan take yi ." Umma ta kai hannu ta shafa sumar kan maryama "allah yayiwa rayuwarki albarka ,allah ya qara mana hakuri, muyita hakuri da sannu allah zai mana sakayy.. qarar wayar umma ce ta katseta maryama ta mike da sauri ta shiga duba inda wayar take "gashi can a karkashin pillow ta fad'a tare da d'auko wayar ta mika mata cike da ladabi ta d'auka "assalamu alaikum, wallahi alhamdulillah mun godewa allah ya kunfan jiki Aa da kanki ai da kinyi zamanki hjy ba sai kin wahalar da kanki ba to shikenan allah ya kawoki lafiya sukai sallama " umma waye zai zo ?granny ce "shiru tayi tana tunani , tashi muje parlour'n tare suka fito zuwa parlour umma na kiran sunan "hassana "kanwar hajiyata na nan zuwa in sha allahu gobe ,hasana ta fito daga kitchen tana goge hannunta tana cewa "kai allah ya kawo mana ita lfy ta kalli maryama ta galla mata katuwar harara "maza ki d'auke wad'an mugayen idanunki akaina mu dai wannan yarinyar ki zame mana balai a danginmu wai aunty yaushe zata bar bangaren nan ne ta koma can gurin uwarta kar muma ta lashe mana kurwa ?wallah duk san dana daura idanuna akanta ina jin kamar na kasheta ta mutu kamar yadda ta zama silar kashe min dan danuwana dan girman allah ki sallema ta bar bangaren nan mu huta da jaraba "ke dan Allah ya isa haka ina zata alhalin tana cikin takaba? wallahi hassana banason abinda kike wa yarinyar nan yana matukar kona min rai dame kike son yarinyar nan taji ?Ko ance miki ita ta kashesa n ?Kiyi hakuri aunty in sha allahu na daina umma ta juya mata baya tana danne hawayenta ".amman Aunty ya kamata ki fito da kayan sadam tunda yanzu ya zama na magada sai bawa yara su yi amfani dashi tunda ya mutu kafin wannan mayar ta gama takaba araba gadonsa .." "sadam bai mutu ba"maryama ta fada da iyakacin karfinta tana juyowa ta fuskanceta tare da dafe qirjinta "tabbas sadam bai mutu ba ta qarasa mgnr tana kuka "yanzu ke hasana har kina tunanin abinda ya mutu ya bari sun zama na magada ku kenan ?dan kune magadansa sai ni da matarsa maryama nan nan idanun umma suka cika da kwalla ta shiga girgiza kai "wallahi hasana ki bani mamaki sam banyi tunanin haka daga gareki ba "idan ma kiyi hakuri ni da kaina zan nemi araba duk abinda ya bari domin allah ne yace araba gado ni ban isa nayi jayayya da hukuncinsa ba amman at least kunyi hakuri ku daina daga hankalinku ,baku barni na huta ba baku bar yarinyar mutane ta huta ba wai me yasa haka n ?karki manta maryama jininki ce domin kinfini kusanci daita dan diyar yayankice uwa daya uba daya wallahi naso sadam ya rayu kodan ya kula min daita ya gatanta min ita ya bata kulawar da duk wani miji yake bawa matarsa ."ta qarashe mgnr tana kuka ". maryam ma ta fashe da kuka ."Umma ko zaa raba abinda sadam ya bari dan Allah a d'an jirkinta tukun har zuwa wani lokaci saboda har yanzu police suna Kan invesgetion idan ya zamo yana raye fa bai mutu ba kuma an rigada an raba komai nashi ni dai a nawa shawarar kar a ta'ba komai nashi hatta suturarsa abarshi tukun nan." da wani irin mugun kallo ta d'auketa dashi " yanzu ke maryama kina tunanin yana raye ? " bai raye yana raye ya kamata abari hukuma ta gama bincikenta alabashi komai zaa yi sai ayi amman for now abar komai gsky Tunda tasoma magna Aunty hasana tayi shiru tsaye tana mka maka mugun kallo, da ashariya daga cikin zuciyarta "kaji min tsinanniyar shegiyar yarinya suka jiyo muryar aunty salma gabadaya suka juya bayansu suna kallonta ahankali ta dinga taku har ta qaraso inda suke "lafiyarki ma kuwa maryama ?gsky akwai alamun kin zauce ayi hanzari akaiki asibitin mahaukata a duba lafiyar kwakwa kuwarki,"kece fa da kanki kika tabbatar mana yaro nan ya mutu tunda a gabanki kika ce an binnesa da ransa amman ki kekashe kasa akan bai mutu ba " wallahi aunty bai mutu ba dan ina ..."ke jaira kiyi mana shiru anan kafin na zuciya na soma yar yar fa miki mari sadam ya mutu kuma bazai dawo ba har abada idan ma zaki ci re hkn aranki ki cire ki fara tunanin wata rayuwa." ta fad'a tana huci wallahi bai mutu ,kuma babu mai raba gadonsa hasalima babu takabarsa akaina ina nan ma tsayin matarsa har tsawon shekaru hudu lallai hasashena ya tabbata yarinyar nan ta samu tabin hankali to tsaya kiji da kyau duk macen da mijinta ya bata ne zatayi dakon aurensa na tsawon shekaru hudu sannan bayan haka tayi idda idan kin haukace ne gara tun wuri musani amman rabon gado tabbas zaayisa acikin gidan nan inji cewar aunty salma . Mmn sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 28 Kwanciya maryama tayi a kasa tana wani irin kuka mai ta'ba zuciya da ban tausayi sai dai duk wannan kukan da take sautin muryarta bata fita sosai ,tana jin ina ma sautin kukanta ya fito fili da hakan zai fiye mata sauki fiyye da rashin fitowarsa bugu da qari ko yasa yan'uwan mahaifinta sun sauko daga tsatsauran raayinsu su tausayawa rayuwarta ta jurewa kowance irin jarabawar da Allah yayi mata amman ta kasa jurewa wannan jarabawar, ta kasa jurewa jarabawar rashin miji da kuma d'anuwa gareta."meye tarin zunubina?tayiwa kanta tambayar hawaye na sake gangarowa akan kuncinta "ya Allah ka sausautawa rayuwata domin idan abubuwan dake faruwa akaina suka cigaba da faruwa zuciyata zata buga ."idanun umma dake cike da ruwan hawaye ta zubawa aunty salma tana kallonta cikin wani irin yanayi na tsananin damuwa da bakincikin mummunan kalamanta ga maryama ."cike da tsananin tausayawa maryama umma ta qaraso gareta ta durkusa ta riko tafin hannunta cikin nata cikin yanayin tashin hankali tace "kukan ya isa haka maryama kada kanki yayi ciwo ." "mai yasa abubuwa suke zuwa min haka umma ?"ya zanyi da wannan rayuwar ? ya Allah ka d'auki rayuwata na mutu na huta da wannan duniyar da babu komai acikinta sai tarin bakinciki ya Allah ka d'auki rayuwata tunda haka rayuwar duniya take "daga wannan tashin hankali sai wannan tashin hankali meye laifina ?nan take tausayin maryama ya sake ninkuwa acikin zuciyar umma tare da jin wani irin tarin qaunarta mara misaltuwa "kiyi hakuri maryama ki daina furta wad'an nan kalaman haka rayuwa take cike da kudirorin ubangiji ,sannan dukkan rayuwa d'an adam rubutaccen al'amarin ne daga Allah,na shafa fad'a miki duk mutumin da Allah yake so shi yake yiwa jarabawa." wani sabon kuka ta fashe dashi tana jin kamar ranta zai fita ya bar gangar jikinta aunty salma ta kwa'be baki tana duban umma da maryama a kaskance kafin ahankali ta cigaba da cewa "da dai kin daina wannan kukan munafurci da kike yi da bazai ta'ba miki maganin halin da kike ciki ba, mutuwa ce da bakinki kika ce agabanki aka binne sadam da ransa to me kuma yayi saura ?Jin haka ya qara sa ran umma yayi matukar 'baci ta d'ago idanunta cikin zafin rai ta kira sunan aunty salma "salma !" Yanayin yadda ta kira sunan cikin tsawa ya d'aga masu hankali gabad'aya sukai tsuru suna kallonta domin wannan shine karo na farko da suka ga tarin damuwa da 'bacin rai acikin kwayar idanunta,"salma karki bari 'bacin raina ya sake ninkuwa akan wanda nake ciki ,nayi ta qoqarin na danne zuciyata akanku amman naga alamun so kuke sai na nuna muku fushina da 'bacin raina"me maryama ta tsare maku ?wani irin numfashi mai zafi umma ta fesar kamar an tsikareta haka umma ta tashi daga gaban maryama "wallahi wallahi !!kunji na rantse akan maryama zan iya 'batawa da kowa dan haka ku shiga hankalinku ku san irin magangun da zasu dinga fitowa daga bakinku saboda kuma kuna da naku ya'ya,allah yasa mata kuka haifa dayawa kusani duk mugun nufinku ga maryama kanku ko kan ya'yanku zai dawo domin allah baya zalinci kuma baya son mai zalinci amman nasan rashin ilimi ke damun rayuwarku domin da kusan dukkan rayuwar rubutaccen lamari ne daga rabbi, kilan da baku tsaya ' batawa kanku lokaci ba gurin matsawa kanku da hassada da hankoron neman duniyar da wani ba ." aunty salma ta kalli umma wacce har lokacin kwayar idanunta na kanta cike da tarin 'bacin rai sannan ta waiga inda baba gali da aunty hasana suke tsaye suma cike da mamakin umma .aunty salma ta daure zuciyarta da maganar umma tace "irin fatan da zaki mana kenan ?"irin fatan dai da kukewa kanku kenan." da sauri umma ta bata amsa da haka sannan tana cigaba da cewa " maza ku fice min daga parlour bana son ganinku kuma wannan ya zamo karo na farko dana qarshe da zaku shigo inda nike kuyi lamarinku nayi nawa bana