← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 105

Sashe 23

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

why sweetheart ?mu bar wannan maganar adamcy muyi wata dan bana son jinta for now shiru kawai yayi yana mai runtse idanunshi shi kad ai yasan zafin da ciwon da zuciyarsa keyi . Sweetheart cikin satin nan in sha allahu zan bar kasar nan zuwa holland da sauri mami ta kallesa sam maganar bata mata dadi ba ,kuma tasan dan ya nisanta kanshi da maryam ne zaka bar kasar nan saboda maryam ko ?tayi maganar kamar zatayi kuka ko d aya sweetheart saboda me zan yi tafiya saboda ita ? kema kinsan tafiye tafiye yana cikin tsarin aikina mami tayi shiru ya riko tafin hannunta cikin nashi sweetheart! ta sake kallonsa ki kwantar da hankalinki nifa banki na daina tafiya zuwa koina ba saboda ke wa na ajiye a inda zani ? Me zakaje yi a hallond?yayi shiru yana kallonta naga duka yaushe maryam ta tare da zaka tsiro tafiya gsky nidai idan son raina ne ka bar tafiyar nan ka wakilta wani ka d an zauna da maryam shikenan sweetheart ya bata amsa da hakan cikin halin damuwa ya mike tsaye yana mata sallama murmushi ta sakar masa amman gida zaka wuce ko ? ya gyada mata kai kawai to allah yayi maka albarka ka gaishe min da maryam anjima manu direba zai kawo maku abinci to !kawai ya fad a a takaice sannan yasa kai ya fice daga parlour n massalacin ya nufa domin gabatar da sallar laasar . Hisham zaune akan kujera yana waya da nuzla eh har yanzu ina office , allah kuwa da gaske nike amman bari nayi sallar laasar na tura miki babu mamaki ma idan na tashi aiki zanzo na gaki kafin na wuce gida , sosai kuwa ya fad a yana murmushi kmr yana gabanta ,ahankali yaji ana Knocking din kofar office dinsa amman ya share yaki bada umarni shigowa ya cigaba da waya da nuzlah har kusan mintuna shabiyar sannan yace wa nuzla bari zan kiraki nan da minti biyar acan bangaren nuzla cike da shagwaba tace a ban yarda ba okay to shikenan zakiji komai da zanyi yana gama fadar haka ya bada umarni shigowa ga diyar aminin abbansa dake aiki akarkashinsa . Zakiya ta tura kofar office din ta shigo ahankali ta tsaya agabansa amman bai d ago ya kalleta ba ya cigaba da wayar da yake . a tsanake ta bude bakinta ta kira sunansa hisha yayi saurin d aga mata hannu yana cewa alamun tayi shiru dan da yasan itace bazai bada umarnin shigowa ba a abdull ne ya shigo akwai maganar da zamuyi dashi shiyasa nace ki bani minti biyar okay naji da zarar na gama dashi zan kiraki ya katse kiran sannan ya kalli zakiya yace yaya akayi ?sai data numfasa kana tace akwai matsala fa me ya faru ya budurwa zata zauna ta dinga tayar maka da hankali haka? nifa abokiyar aikinka ce kuma kusan yaruwarka wacce ko matarka tasan da zamana bata ta ba nuna damuwarta ba sai wata can . aa dakata zakiya banason haka matsayin nuzla dabam a wajena tana sama da kowacce mace a wajena ba wai wata bace kin fahimta ko ? kana nufin har matarka ? eh bakiji nayi generalizing ba nace kowa , tafi kowace mace dan haka bana had a maganarta data kowa ki kyaleni ke bani ma abinda ya kawoki ki bar min office menene ma ya kawoki mr Ibrahim yace ka tura masa idan ka gama naji zaki iya wucewa please ya fad a yana nuna mata kofar fita da yatsun hannunsa . Ta juya ranta a matukar bace yace idan kina shiga harkata zan iya sallamarki aiki , akwai wata mace ne bayan nuzla acikin zuciyata da zaki zo kina wasu surutan banza ?tsaki yaja ya fara duba file din data ajiye agabansa . tana fita daga office din hisham office din abdull ta shiga tana kiran sunansa abdull !! menene ?ya tmbyeta tare da barin abinda yake ya dago ya zuba mata ido wai me abokinka ya taka akan wannan banzar yarinyar nuzla ne da zai iya ciwa kowa mutunci akanta wai me tafi sauran mata ne ?kaga irin wulakanci da yayi min yanzu saboda suna yin waya daita kinsan me ?ta girgiza masa kai alamun tana jinsa hakuri zakiyi zakiya dan wannan yarinyar itace muradin ransa dan ko matarsa baya sakewa daita akan wannan yarinyar kuma bata son yana muamula da kowace mace ai kuwa wallahi tayi kadan dan bata isa ta hanashi muamula da kowa ba . Ita din me ? sannan akan me ?to sai dai idan a gidinta zai tare ko kuma ya cicibota ya dawo daita office dinsa inyaso duk abinda yake tana gani ko kuma ta dinga binshi duk inda za shi . yayi murmushi yace ko dai kina kishi daita ne naga duk kin damu ? kishi ?meye tsakanina da hisham da zanyi kishi akanshi bayan aiki da kuma dangantar dad dinsa da nawa ? kawai dai wallahi naji ina tausayin matarsa ne yarinyar kirki ce ga hankali ga ladabi shine kawai nake tausaya mata saboda nasan duk lokacin daya auri wannan banzar yarinyar ina tausayawa rayuwar matarsa duk da nasan yarinyar nan bazata yarda ta auresa ba wata manufa gareta . Me yasa kika fada haka ?ince guduwa tayi lokacin da zaayi aurensu dashi sannan yanzu ta dawo masa ai kasan akwai abinda take nufi dashi wallahi , wakilla haushi taji dan ya auri nana hauwa u kawai ta dawo ta hanashi zaman lafiya da matarsa kuma tasan idan batayi amfani da karfin soyayyar da yake mata ba bazata yi galaba akanshi ba shi kuma dake qaramar kwakwaluwa ce dashi yake wani biye mata yarinyar daya kamata yaci ubanta laada waje Abdull ya sake yin murmushi wanda dagani na takaici ne kinsa me ? kije kawai Kiyi aikinki zai fiyye miki amman hisham kam bai ji bai gani akan nuzla bancin nasan gidansu nuzla basa biye biye da ni kaina nace anyi masa wani abu ne gsky kam amman ni matarsa nake ji ka duba kaga ranar d muka je gidansa baka ga yanayinta ba kamar tana jin tsoronsa komai a dar dar take yi shi kuma ko kallon biyayyar da take masa baya yi sai ma wayar da yake da wannan banzar yarinyar ina ma ni ya samu da naci ubansu daga shi har ita gsky nana hauwa u bazata iya ba Ke dai zai fi kiyi abinda Ke gabanki sarkin shiga abinda babu ruwanta kana ji ko abdull dan allah Zakiya kije na gaji da mgnr hisham nayi masa mgn har na gaji idan zai canza ya canza idan bai zai canza ba tare dani allah zai wa hukunci ba daga haka bai sake cewa kala bata juya ta bar office din cike da takaici . Qarfe biyar daidai motocin ata suka shigo gidan yayinda maryam ke zaune a parlour n kasa cikin tsananin tashin hankali tana waya da nana hauwa wallahi sister duka fa kwanaki biyu ne kawai nayi acikin gidan nan amman ji nake tamkr a makabarta nike zagi kuwa acikin kwanakin nan sai dai kawai nace Alhamdulillah ,shi kawai baya ganin abubuwan da yake min kuskure ne shi kawai kanshi ya sani eh ko jiya ya sha yanzu haka ma cikin matsala nike dan daren jiya na kwashe kwalin sigarin na zubar a shara ashe da saura aciki kuma yace lallai sai na dawo masa da abunsa ,ni yanzu tashin hankalina na aika a siyo masa sigarin baa samo exactly irin wanda yake sha ba Shiru tayi sakamakon turo kofar parlour n da akayi idanunta data zubawa kofar suka sauka akanshi sanda yake qoqarin takuwa ,sosai ya dauki hankalinta koda yaushe fuskarsa tashi a daure take kallo daya yayi mata ya janye idanunshi akanta sannu da zuwa ta fad a a matukar tsorace tana qoqarin mikewa ta bar parlour n tun kafin ya soma cin ubanta , bai amsa ba yace me na fad a miki ?bana ce karki sake na dawo na ga wannan fuskar ba ? ya qara taku biyu taja baya da sauri dan allah kayi hakuri ta fad a cikin tsananin tashin hankali .ina sigarina ? Mmn sudais MAR'ADAMS
Chapter 23 · 0% Book details