Sashe 103
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ka gani acikin hall din rike yake da takardunsa na makaranta wasu acikin jaka, wasu rungume dashi ,tun daga Kan matakin diploma har zuwa kan digree na biyu .bayan wani lokaci aka fara kiran suna daya bayan daya har aka kawo Kan maryama da addua ta shiga inda zaa mata interview tana shiga ta yaye nikaf din fuskarta kasancewar taga mace ce ,sectary ta sakar mata murmushin dan ita tun ranar data soma ganinta taji ta kwanta mata arai yarinyar tana da natsuwa gashi tana shiga ta mutunci ko yanzu duk masu neman aiki babu wanda yayi shigar mutunci kamarta ga guri ki zauna na gode maryama ta fad a a natse tare da zama tana ma kanta addaur samun nasara . bayan awa daya aka gama daita tare da daukarta aiki maryama hussein idan allah ya kaimu gobe zaki fara zuwa aiki amman wannna abun da kike rufe fuskarki dashi ba lalla sir ATA ya yarda dashi ba . shiru maryama tayi tana jin da kamar wuya ta iya fita babu shi a fuskarta domin ta rigada ta saba tsawon shekaru haka ta taso idan ma bata saka shi ba bata jin dadi muryarta can kasa tace zan dai gwada zuwa dashi idan ya bukaci na daina zuwa dashi zan kiyaye na gode sosai. ta fad a tana mikewa ta bar office din a wajen ma akatan ta jira yusira itama cikin ikon allah ta samu suka nufo gida cike da murna yanayinta ya tabbatar ma yan gidansu ta samu aiki ta rungume umma cike da farinciki. alhamdulillah umma mun dace kai masha allah masoyiya gsky naji dadi sosai da kyakkyawan albishiri da kika min ,zuwanki aiki zai rage miki damuwa sosai allah yasa ki fara a saa maryama ta qarasa ta rungume granny na gode matuka da adduarku da bani kwarin gwiwa ta shafa kanta babu komai maryama gabadaya parlour n umma ya cika da murna aunty da habib ma murna fal anan yusura ta wuni currr suna murna sai yamma tayi masu sallama ta koma gida da zumar sai sun had u gobe . Washegari da misalin karfe bakwai daidai a AGC company tayi masu babu bata lokaci aka nuna kowace office din da zata dinga aiki tare da basu file file da zasu fara aiki akansa basu kasance guri daya da yusura ba ,tare da sultana suka kasance a office daya sosai maryama ta dukufa aka aikinta tana Kan aiki sectary ta shigo ta mika ma maryama wasu file please ki cike yanzu ki kawo min office dina okay ma ! ta fad a tare da amsa ta ajiye aikin da take ta fara wanda aka bata . sultana kam ko ta Kan aiki batabi ba wayarta ma take opereting can ta soma magana da alamun vioce note take yi kinsan wani abu qawata gani zaune babu abinda nake takardun banza daakawo gasu agabana haka zasu karaci yininsu bazan cike komai ba kuma bazan zana komai ba dan ba abinda ya kawoni kenan ba. ta tura tai shiru tana murmushi can sautinta ya sake karade office din wa wannan mutumin ai bai yi ba wani office aka kaini dabam ba idan yake ba amman duk bata baci ba komai zai tafinmin yadda nake so ai bari Ke dai qawa mutumin nan ya hadu fiyye da tunaninki sai ma kin gansa a zahiri sai kin kusan sumewa . ta qarasa mgnr tana kam kamkame jikinta . alamun tana jin shauki akansa . Maryama na ciki aiki sai ga subai ta shigo office din hannunta rike da wasu file yayinda wuyata ke makale da ID card mai dauke da cikakken sunanta da tambarin Z&A da sauri ta qaraso gurinta tana dafa kafadanta wa nike gani haka kamar maryama ?maryama ta dago a natse tana dubanta a subaia wallahi nice ya kike ya kwana biyu ? lafiya kar dai kina cikin sababbin ma aikatan daaka diba?maryama tai murmushi tana gyada mata kai alamun eh ! kai gaskiya naji dadi dana ganki a matsayin maaikaciya anan . Maryama ta maida hankalinta ta cigaba da abinda take ai nasan daman allah bazai barki haka ba kullum ina sakaki cikin adduarta na gode sosai da taimakonki gareni kai karki damu ai yiwa kai ne fatan alkhairi thank you dear . har subaia ta juya maryam ta mike tana kiran sunanta ta tsaya Yauwa subai a ina ne office din madam some?muje na nuna miki suka fita tare tana sauke nikaf dinta suna qarasa fitowa ta nuna mata da dan yatsanta gashi can sai mu sake haduwa nima wani aiki ne ya kawoni sukai sallama ta karya kwana ita kuma maryama tayi kokari shiga office din data nuna mata ta tura kofar glass sannan ta sanya jikinta ciki adaidai lokacin da idanun ATA ke Kan cctv wacece wannan data shigo yanzu ?ya tmby yana dauke idanunshi ya maida kan fara takardar dake gabansa ya juyo mata compute daake ganin shiga da fitar mutane . Some ta sauke idanunta akan computer maryama ta gani muryar some na rawa tace maryama hussein! wace ce haka ? sabuwar maakaciya ce baki fada mata baa zuwa mana da irin wannna shigar bane ? na fada mata sir !yayi shiru yana maimaita sunan acikin zuciyarsa maryama hussein sannan yana sake kallon cctv tabbas itace yarinyar wannna ba yarinyar da muka bukaci zanenta bane watanin baya ba ? muryarta na rawa tace ita itace sir . what ! ya fad a tsawace nan take jikin sectary ya dauki rawa dan allah kayi hakuri sir itace yarinyar da akayi interview akan kasuwanci daita , yarinyar da take da kwarewa sosai akan zane itace yarinyar da kace anemo ta watanin baya kenan the same person ce ? ya fad a yana ciza lips dinsa da karfi yes sir duk mutun daya ce itace take zane but sir yarinyar tasan kan aikinta duk a rud e take masa wannan bayanin. shiru yayi yana jin wani irin mummunar faduwar gaba from no where sai dai bai dago ba ya cigaba da typing din da yake cikin zafin rai . kana kallon yadda yake daddana keyboard din system din kasan baya cikin natsuwarsa bana ce kar a Kuskura a dauketa aiki ba ?kuma kikayi son ranki har ma kina min dogon bayani akan yadda ta wulakantamu sir !sir !!kayi hakuri nayi ta kokarin na fada maka saboda gudun faruwar haka amman kaki bani dama me kke nufi ni ban fad a miki ba karta samu aiki har karshen rayuwarta ba bama a wannan company din ba har other companies?Ke ma kinsani bana bawa kowani irin mutun second chance dan haka kije ki sallameta bana son ganinta acikin company din nan oya go out ! ya nuna mata hanyar fita jikinta na rawa ta fito . tana fita ya zabura ya mike tsaye ya daura hannunsa daya akan hannun kujerar daya tashi gabansa na wani irin mummunar faduwa zuciyarsa na tuttukin zafin kamar ya dakatar da some amman bakinsa ya kasa furta komai . ya bar wajen ya koma jikin window yana kallon haraban maakatan yaso kwarai ya samu nasara sake ganawa daita amman ina bazai iya daukar iskancinta ba har kamar shi ya sauke girmansa ya kirata amman taki daukar wayarsa har ma da kashe masa waya ga mummunar sako data fadawa james bayan haka ya nemi ganawa daita a ogun shima batayi masa abinda ya bukata ba sai ma qara masa damuwa datayi jin abun yayi kamar alokacin ya faru babu wani sausauci da zai mata wanda ya wuce ya koreta daga karkashinsa . da sauri sectary ta fito zuwa office dinsu tana shiga ta isketa zaune da farar takadar agabanta tana zana mutun sanye da suit da wondo har ma da takalmi acikin mintuna da basu wuce ashirin ba ta tsaya tana sauke numfashi, ganin ita kadai ce a office ta qaraso sosai ta tsaya akanta tana tunanin yadda zatai mata magana dan sam babu dadi ka samu aiki ranar da ka fara zuwa ace an koreka tsayuwarta batasa maryama ta dago ba dan bata ma ji alamun shigowarta ba kokari take ta kammala aikin da ta fara dashi amatsayin aikin farko . muryar some a sanyaye ta kira sunanta maryam hussein ! maryama ta dago da sauri tana cewa yes ma ,akwai wani aikin da zan miki No you re fared cak numfashin maryama ya nemi ya dauke sakamakon jin mummunar labarin datayi nan take dakin ya dinga jujjuya mata wani irin tashi hankali tashig mara misali kafin a hankali ta janyo numfashinta dake kokarin barinta ta dawo dashi gangar jikinta ta fuskanci sectary sosai hankalinta na qara tashi wannan hukuncin MR ATA n Hukuncin Mr ATA . ?ta furta da karfi t kaifin me nayi masa nida yau na fara aiki anan ?tayi mgnr Kmr zatai kuka cike da tausayawa sectary ta dafata sai dai ta kasa cewa komai ko zan iya magana dashi dan haka kawai bazaa dakatar da mutun batare da wani laifi ba ?tayi mgnr a fusace . no no !! ba sai kingansa ba ,dan ni kaina a halin yanzu ina cikin matsala dan allah ki bar nan yanzu kafin ya shigo ba maganar na bar nan bane ko kina cikin matsala ina son nasan dalilin da zai sa akoreni tunda nasan sai da dalili akewa mutun irin wannan korar lallai sai nasan meye matsalar kafin na bar maakatan nan , ki natsu please maryam sir bazai ganki ba a yanzu . Kema kiyi hakuri kiyi min iso Ke bari ma naje da kaina . fuuuuu ta nufi kofar fita da sauri some ta biyo bayanta tana kiran sunanta maryama ki tsaya karki sake yin wani kuskure ta riko hannunta cikin zafin rai bazai yuwa ma ki shiga inda yake ba wannan ya sabawa doka . Doka wani doka kuma ?wallahi kusani kun tafka babban kuskure na korata ,bari ma kiji bani nayi applied din aiki a kamfaninku ba yi min akayi dan haka yanzu ma ban damu ba kije ki fad a masa ko bansamu aikin a anan ba zan samu aiki adalilin baiwar da allah yayi min kuma bare ma zan samu aiki da takarduna dan allah kiyi hakuri nima ba laifina bane . shiru maryama tayi kafin ahankali tace madam some ko zansa