← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 105

Sashe 95

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

saman goshinta da karan hancinta zagaye parlour'n ta shiga yi zuciyarta na tafarfasa tana cikin wannan halin taji sautin sanyayyiyar muryarsa kasa juyowa tayi ta kallesa dan zuwa lokaci hawaye sun qara cika idanuwanta "baby nah!"tana jinsa amman ta kasa juyowa ta kallesa dan bata son yaga rauninta "baby nah kukan me kikeyi diriricewa tayi tana qoqarin maida hawayenta "zo gareni !qoqarin juyowa take amman kukan da take yasa ta kasa sai numfashi da take fixgowa tana fitarwa da kyar "please baby nah maman abar qaunata ."still bata juyo ba ta cigaba da tsayuwa tana jan numfashi ahankali ya qarasa ya tsaya abayanta ya had'eta da qirjinsa ya daura hannunsa daya akan cikinta yana shafawa yana shakar kamshin turaren jikinta kusan second goma suna tsaye haka tunani tayi kar wani yazo ya samesu haka yasa ta zare jikinta kwayar idanunsa ya tsura mata yana jin yadda soayyarta ke sake huda zuciyarsa ." Ahankali ya riko tafin hannunta yayi taku biyu ya zaunar daita akan kujera mai zaman mutun daya ya dawo gabanta ya durkusa a gabanta tamkar mai neman gafara tare da kafeta da kwayar idanunshi yana kallonta yana nazarin yanayinta ahankali ta kawar da fuskarta gefe tana qoqarin sake danne damuwarta numfashi ya sauke da karfi tare da tsarke hannunshi cikin nata ya dawo da fuskarta garesa "am sorry baby !ya fad'a yana murza tafin hannuta cikin nashi" me kayi ?naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana sake damke hannunta cikin nashi sannan ya motsa labbansa "na haifar miki da damuwa "wani irin damuwa kuma ?ni babu wata damuwa daka haifar min?na haifar miki da damuwa mana nayi silar saka zuciyarki shiga qunci na tsaya na saurari nuzla alhalin ban nemi izini daga gareki ba nasan dole zakiji babu dadi aranki dan Allah kiyi hakuri ki yafe min ."murmushin tayi wanda yafi kuka ciwo "dan Allah ka daina fad'ar haka banaso meye aciki dan ka kula nuzla ?karfa ka manta ni matarka ce nuzla kuma yaruwarmu ce gabad'aya kana da damar aurenta ma ba kulata ba ,karka manta na baka wannan damar idan har yanzu kana raayin aurenta kofa a bud'e take bazan haramta halal din da Allah ya halallta ba sai ma nayi maku fatan alkhairi ta fad'a tana kallonsa shima ita yake kallo yana sake hango damuwa daga gareta ," gabad'aya fuskarta ta sauya hankalinta a matukar tashe take maganar da take amman kaji abinda ta fad'a dan karta haifar da damuwa atsakaninsu "ni dai Kiyi hakuri bazan sake kulata ba yau ma na tsaya na kawo qarshen komai ne a tsakaninmu sautin muryarta ne ya katse masa magana "tashi ka zauna please kar qafafuwanka sunyi ciwo ka daina damun kanka dan baka min laifin kome ba tana gama fadar haka ta mike da kyar tana cewa "bari na shiga dakin mami yanzu zan fito ta soma daga kafarta da kyar bayanta yabi da kallo yana mamakin hali irin nata da duka matan duniya haka suke kamar matarsa da baa samu wata damuwa a gidan aure ba komai nata dabam ne yasan tana da tsananin kishi akansa amman yanayin kishinta na daban ne kuma yana burgesa dan sau tari idan ya kira tana d'auka zata ce "an gaishe da mijin nuzla da nana hauwa'u tun abun na masa dadi har yazo ya fara jin zafin abun dan tun yana amsawa yazo baya amsawa sai dai kawar da maganar ya shigo da wata ,mata mu sani wannan d'abia ta nana hauwa'u d'abia ce mai kyau mu dinga kawar da idanunmu da hankulanmu akan mazajen mu ,mu basu dama kada mu saka ido dayawa akan lamuran su most especially akan mata domin Allah ya halatta zuciyar maza da son mata dayawa yayinda zuciyar mata take son nmj kawai mu san irin salon kishin da zamuyi idan kayi mijinka kawaici tabbas zai dinga jin kunyar aikata wasu abubuwan." "Tun dazu nake binka akan maganar sultana Adamcy fa sam sam yaki yarda ya dauketa aiki akarkashinsa amman kaki kayi komai akai aunty abida ta cigaba da bin yaya ibrahim abaya tana masa magna amman bai ce mata komai ba "yanzu shikenan babu abinda zaka iya yi akai ?ta fad'a adaidai lokacin da suka tsaya suna fuskantar juna "na rasa meke damun taunainki kina yi kamar baki san halinsa ba tsawon shekaru kina cikin gidan nan kuma babu abinda baki sani akansa ba , kinsan yadda halinsa yake "haka ne nasan komai amman ni nasan yadda zanyi wanda shi kansa bazai ta'ba tunanin zan iya aikatawa ba ai tunda har nayi niyyar sultana ta auri adamcy kamr anyi auren nan an gama muddin ina raye "wannan shine dalilinki naso ta kasance kusa dashi ?ta gyada masa kai alamun "eh! "kina tunanin Adam zai amince da wannan hadin naki ?" ka tsaya kasa ido kaga ikon allah muddin ina raye sai ya aureta "numfashi ya sauke "gsky da kin canza shawara kina kallon yarinyar da mahaifiyarsa ma tayi masa umarni ya aura da kyar ya yarda yayi mata biyayya a qarshe ma sai daya saketa bare wata sultana can ,dama baa acikin family's dinmu take ba ". "kai dai ka tsaya kasa ido kayi kallon abinda zanyi tunda shi har yanzu bai fahimci menene dalilin da yasa nake son sultana ta kasance a kusa dashi ba dan haka zanyi komai akai tunda kaima har yanzu kana bada umarni a kafani kamar yadda yake bayarwa ko..."dan allah malama ki bar wannan shirmen naki tun wuri ki dawo hankalinki idan ba haka ba zaki aikata katoton kuskuren da zai jawo miki matsala tabbas ina da iko akan kafanin adalili mahaifina kuma shima mahaifina nawa a koda yaushe cikin bin bayan adamcy yake akan komai he always supporting Adam nayi imani ko wannan tsarin daya kawo baba babba yasan da komai dan haka a matsayina na mijinki zan baki umarnin ki cire hannunki ki fita cikin lamarinsa idan ba hk ba duk abinda yabi yo baya babu ruwana ya qarasa mgnr yana nunata da dan yatsansa sannan ya kama gabansa shiru tayi tana kallon bayansa tana ystsina fuska ." Maryama zaune a kusa da mahaifiyarta cikin halin damuwar data tsinci kanta, kullum qoqarin raba kanta da tunani take amman ta kasa domin da zarar ta runtsa idanunta yaya sadam dinta take ganin cikin tashi hankali yanzu hk ma jan hankali mahaifiyarta take mata "ki fahimceni princess wannan matsalar gabadaya ta shafemu ko nace na fiki shiga cikin damuwa da tashin hankali mai tsananin akan mutuwar sadam amman me zamuyi daya wuce hakuri mu barwa allah komai hatta mahaifiyarsa ta hakura ta barwa allah mai yasa Ke bazaki hakura ba "nasan akwai ciwo sosai amman ki dauka haka taki qaddarar take bawa kuma bai isa ya canzawa kansa qaddararsa ba ,bamu sani ba ko wani mijin Allah zai kawo cikin kankanin lokaci yasa wannna lamarin ya faru "numfashi maryama ta sauke mai hade da saitin kuka" dan allah kiyi hakuri ki daina fad'a min haka babu wani aure da zanyi na gama aure har abada ."ta jingina bayanta da abun gado ta daga idanunta sama hawaye na zubo mata "you better eat enough with all this cry cry ..."bazan iya cin komai ba aunty ." "Common bude baki na baki abinci kinji my princess wasu sabbin hawaye ne ya zubo akan kuncin maryam ta dube mahaifiyarta gabadaya ta fita haiyacinta adalilin damuwar data sameta " aunty kin cikin abinci ne ?banci ba ina son sai naga kinci ne taya zan iya cin abinci alhalin princess dina tana kwance kwana uku kenan bata sakawa cikinta komai ba ,maryama ta sauke naunayen ajiyar zuciya ta dauki karbi spoon din hannun mumcy ta dibi abinci ta kai bakinta "kici abinci sannan naci batai mutsu ba ta bude mata baki ta kai lomar abinci bakin mahaifiyarta, bata kai ga cire spoon din ba aunty ta dibo abinci da hannu ta kai bakin maryama." Maryama na hawaye mahaifiyarta hawaye aunty tana matukar tausayawa kanta da rayuwar yayanta "ina rokon allah yayi min sausauci domin zunubina yake shafar yayata da basu baji basu gani ba wasu hawaye masu ciwo ne masu zafi sukai zuba a idanunta "in sha allahu zan koma ga dangina zan rokesu gafara "dan allah Allah ki daina damun kanki nima na daina damuwa na yarda da qaddarata "aunty ta rungume maryam " yauwa princess ki kula da kanki kinji ,karki ji komai aunty in sha allahu zan kula miki da kaina ." "Me zaki ce da rana ?kinga aunty ba sai kin wahalar da kanki ba wannan abincin da naci ma ya isheni har gobe aunty ta dan ware idanunta waje "a'a ki fad'a min kawai duk wahalarsa zan girka miki maryam tai murmushi bata ce uhm ba bare umh uhm sai ma ta daura kanta akan cinyar aunty yayinda ta saita idanunta akan takardun zanen jamaa dana kayan sawa a hankali tayi zurfi cikin tunanin makomar rayuwarta ta rasa komai ta rasa aikin yi duk inda ake bukata zanenta yanzu an daina nemanta ko tayi ta kai masu ma basanuna alamun ma yayi masu bare su karba dan mijin datasa mu ya tafi ya barta me kuma ya rage mata yanzu ?mutuwa !zuciyarta ta bata amsa da haka ta runtse idanunta gam saboda batason mahaifiyarta ta fahimci damuwarta aunty ta daura hannunta akanta hular kanta ya zame nan kwantaccen gashin kanta ya bayyana "princess dan Allah ki barwa allah komai kinji da sannu allah zai yaye mana komai numfashi ta sauke tana riko hannun aunty cikin nata "na gode sosai mamana allah ya tabbatar mana da alkhairi ." Zaune suke a babban parlour'n hajiya zulaihert baba babba da babba qarami da uncle jay sai fahad gabansu kayan motsa baki ne aka kawo masu kowannensu cikin shiga ta alfarma acikinsu babu wanda bai taba abinda aka kawo masu sai baba qarami wanda yake cika yake batsewa sannan yake allah allah Adam ya sauko ."ahankali ATA Ke saukowa daga matattakala jikinsa sanye da kaya light blue kansa sanye da facing cap fari sol haka ma kafafuwansa wasu hadaddun silifas farare ne sanye dasu sai kamshi turaren REED ne Ke tashi ajikinsa a natse ya qarasa saukowa ya qaraso inda suke ya gaishesu gabadaya yana tsaye bai kai ga zama ba babba qarami ya zabura ya mike a matukar fusace ya soma
Chapter 95 · 0% Book details