Sashe 34
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
murmushi ya kwace masa a saman fuska wa zai same kamar maryam yace bai so ? sai dai wani dalili na dabam ya haifar da hakan ,sam ya manta a inda yake sai da yaji mutane ana masa hon a she fa motoci ya tare duk suna tsaye suna jiransa murmushi yayi sannan ya kama gabansa yayinda maryama tuni ta shige cikin ma aikata bata ma san lokacin da yaya sadam ya wuce ba . tana shiga sauran abokan aikinta suka qaraso suna mata magana suna shirin shiga inda zaa wa masu neman aiki interview amman ita maryama hankalinta bai garesu yana kan neman inda subia ta shige ,tunda tasan a tun lokacin da sukai waya daita ya cancanci ace tana wajen koma anyi mata interview an gama . taja ta tsaya tana cewa kuje zanzo na sameku daga baya .ta bud e jakarta ta ciro qaramar wayarta ta shiga neman layin subai a ,ganin an bud ewa ammar mota ya fito yana nufota yasa ta sauke wayar daga kunnenta tare da kashewa gabad aya ya iso har inda take tsaye yana gama qarasowa wayar hannunta ya amsa ya rike ta kallesa tana murmushi sannan tace barka da safiya ? Barka ! me ya tsayar dake da sai yanzu kika qaraso ?ya tmbyeta yana duba screen din wayarta sunan wacce ya gani ne yasa ya mika mata wayar wallahi wanda zan aura ne ya bata min lokaci tayi maganar cikin salon jan hankalin duk wanda yake tare daita, ammar kasa magana yayi kafin daga baya da kyar cikin fad a yace wato har zaki iya fad a min wanda zaki aura ne ya bata miki lokaci ? tayi shiru tana wasa da yatsun hannunta dan batayi tsamanin zai ji haushi maganarta ba ganin babu komai a tsakaninsu sai mutunci da girmamawa amman ki sani wannan ba mutuncinki bane ko nace zaki zubda mutuncin family d inku ne . Ai shima family dinmu ne da mahaifinsa da mahaifina the same mother the same father wani irin kallo yayi mata mai cike da tunhuma,itama kallonsa tayi numfashi ya fesar yace shi kuma mijin da nayi miki fa ya zanyi dashi ?tayi murmushi tana cewa allah sir ka daina min haka wallahi kana d aga min hankali ,kai kanka kasan kafi karfina bare wanda kake fad a wannan sai dai na qara dagewa da aikin ibada wata killa na samu irinsa a aljanna yayi murmushi yace muje Ahankali suke takawa yayinda mutane suke gaishesa wasu ya amsa wasu kuma ya d aga masu hannu kefa ko anyi miki interview ko ba ayi miki ba dole zaki yi aiki damu sure tunda inda kai ba ,ai sunanki na can tuntuni kinga office dinki can ta kalli inda ya nuna mata woow gsky naji dadi sosai kinga ga office dinki ga na mijinki in sha allahu tayi murmushi kawai tana cewa subai a fa ?nifa nafi son naji kana magana kana had awa daita zai yi magana kenan, wayarsa ta d auki qara sauti ,ya soma qoqarin d auka bata tsaya jiransa ba ta cigaba da tafiya dan daman da kyar take iya jirawa dashi da sauri ta qarasa tana shiga aka kira sunanta . Sai da tayi addu a sannan ta shiga office din ta gaishe da mutumin data gani zaune mai suna wale yana duba wasu fararen takardu,ya d ago ya kalleta a natse sannan ya sake kiran sunanta maryama hussein ! tace yes sir ! sai daya bata izinin zama sannan ta zauna a natse tana wasa da yatsun hannunta wanda ya zame mata jiki ,ya d an saci kallonta yana mamakin matsayin da aka bata ,domin kujera ne da suka dade suna neman wanda zai maye gurbinsa , sai dai lokacin daya fara auno mata tambayoyi akan kasuwanci da kuma matsayin da zata taka ya ajiye mamakinsa a gefe domin kuwa ta cancanci ta hau matsayin kuma irinta mai kamfanin ya dade yana nema . bata wani jima ba ta fito har da award aka bata sakamakon aikin da tayi dasu daman kuma sun ajiye ne domin rana irin ta yau congratulations sauran abokan aikinta suka shiga yi mata tana amsa masu da thank you tare da rungumar mata daga cikinsu duk wannan farinciki da take ciki bai kawo mata natsuwa ba saboda rashin ganin subai a da batayi ba ta ciro wayarta ta soma nemanta tana tafiya ahankali har ta fito haraban ma aikatan subai a ta d auka tana kuka hankalin maryama ya sake tashi sosai ciki tsanani tashin hankali tace subai a kina ne na shigo har an d aukeni aiki banganki ba ? tana shirin sake yin magana ta hangota a bayan wata bishi tana qoqarin fitowa . Da sauri maryama ta qaraso ta tsaya tana qare mata kallo tsab hawayenta yasa zuciyar maryama tsananin bugawa me Ke faru dake subai a ?kukan me kike yi ?muryata cike da kuka tace na rasa aikin nan ,da yawa wad an da suka d auka alfarma ne yanzu bansan ta yaya zamu cigaba da rayuwa ba daman da allah da aikin nan na dogara gashi ban samu ba muddin sai da wata alfarma zan samu aikin nasan har abada bazan samu ba . ta riko hannunta maryama tana cigaba da kuka ta soma rokonta dan girman allah maryama karki barni haka ki taimakeni ki bar min aikin nan nasan zaki samu wanda yafishi gabad aya idanun subai a sun rufe har sai da maryama ta kira sunanta sannan ta tsaigaita kukanta ki kwantar da hankalinki ki bar kuka nan haka amman ta yaya babu sunanki bayan .. sai kuma tayi shiru ta janyo hannuta zuwa ciki zo muje . maryama na gaba subai a na bayanta har suka qarasa bakin office din james ta nemi izinin ganinsa aka bata damar shiga ,wanda ta samu wannan damar ne saboda ammar domin yadda yake mata yasa mutane dayawa d aukar sonta yake maryama ta shiga tare da subai a dake kuka har lokacin . bayan ta gaishesa cike da ladabi tace dan allah ina neman wata alfarma agareka ya kalleta dan shima ta burgesa yadda ma akatan suka dinga yaba kwazonta tun kafin tazo kuma zuwanta wale ya sake tabbatar masa iri irinsu basu dayawa a duniya dan tunda ya sheida masa ya kira mai gidansa seun ya sheida masa muryarta a matukar sanyaye ta soma magana kamar zatayi kuka dan allah sir wannan yaruwa tawa nake son ta maye gurbina ma ana acire sunana a saka nata . ya kalleta a tsanake domin yasan yadda ake shan wahalar neman aiki yanzu da kudinka ma baka samu Saboda allah zakayi karka tsaya tunanin komai ni inda aikin da zanyi domin tallafa rayuwata for now ,ita kuma bata dashi da wannan aiki Kawai ta dogara ga mahaifinta ya rasu ko da yake nima marainiya ce amman dai tafini bukatan aikin nan saboda tana da kanne dayawa da mahaifiya mara lafiya dake karkashin kulawarta itace komai nasu da wannan maganar ta karyar da zuciyar James ya kalli subai a cike da tausayawa yace sorry oo ! zan iya miki wannan alfarma sai dai bazata maye gurbin kujerarki ba tayi shiru tana tunani abinda zata ce kafin tayi magana ya cigaba kujerarki ke kad ai ake bukata sakamakon oga ammar sunanki ya bayar gashi yanzu kinzo da wata magana karka ji komai a saka a duk inda zaa sakata nidai burina ta samu aikin ni zuwa gaba in sha allahu zanyi aiki daku amman a yanzu burina subai a ta samu aiki . Mr James ya saka sunan Subai a ya cire sunan maryama suka fito zuwa gindin wata bishiya maryama na cewa subai congratulations na tayaki murna kawata yanzu kin zama cikakkiyar maaikaciya ta fad a tana murmushi subai a ta rungumeta cike da farinciki na gode na gode maryama allah ya saka miki da mafifincinsa nayi imani zaki samu aikin da yafi wannan da kika bar min tana kuka tana gode mata haba subai ki daina kuka kawai dan na sadaukar miki da aikina kike wannan godiya da kuka haka ? ta goge mata hawaye tana cewa ni na zan bar ki na wuce gida nasan akwai abubuwan da zaku yi kafin ku wuce ina miki fatan alkhairi allah yasa ki fara aiki a saa ta juya a hankali ta soma taku subai a tabi bayanta da kallo hakika bazata ta ba manta alkhairinta gareta ba . Da wuri maryama ta dawo gida koda ta shigo kai tsaye bangaren ummah ta shiga ta sheida mata amman ta isketa a dakinta tana bacci dan haka ta fito ta shiga bangarensu ta zauna a parlour n tana sauke numfashi tare da dafe goshinta ko cikakken minti biyar batayi ba ,Aunty ta fito da mamaki take kallonta lafiya naga har kin dawo ?lafiya aunty nan ta zayyane mata komai sosai ran aunty ya baci kamar ta rufeta da duka musaman data lura ko ajikin maryama dan babu alamun damuwa atare daita me yasa zaki bada aikinki bayan Kinsan muma muna fama da kanmu ? aunty kiyi hakuri kin sani ni zan iya cigaba da aikin zanena kafin na samun wani aikin ita fa ?bata da wani sanar hannu da zatayi kuma rokona tayita tana kuka saboda bata da hanyar da zata kula da kannenta da mahaifiyarta fatana allah yasa ya zame min alkhairi ta qarasa mgnr muryarta na rawa alamun kuka Aunty ta samu waje ta zauna kusa da ita tana cewa shikenan allah yasa ki samu wani wanda yafi shi muryarta a raunane tace Ameen ko da ummah da habib suka ji suma abun bai masu dadi ba amman babu yadda suka iya tunda ta bayar sai hakuri da fatan alkhairi . washegari tana zaune a parlour n su tare da aunty kiran ammar ya shigo ta tashi ta koma dakinta sannan ta d auka tana dauka ya rufeta da fad kin kyauta saboda shakuwa da qaunar da nake miki yasa na tsaya lallai Ke zaa bawa wannan matsayin saboda ina son shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninki da Adam amman kika zuba min qasa a ido ,ina ganin idan shakuwa ta shiga tsakaninki dashi zai taimaka kwarai wajen janyo hankalin gareki shine kika bar wata . sanyayyen murmushi tayi kamar tana gabansa to