← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 105

Sashe 67

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

suna taka step, kallonsa kawai aunty shahida take zuciyarta cike da matsanancin bakinciki da tausayinsa ,bakincikinta saboda yadda yake janta, tausayinsa kuma saboda yanayin da yake ciki dan yanayinsa kawai zai tabbatar maka da baya ciki natsuwa da kwanciyar hankalinsa . kai tsaye d'akin maryam suka nufa inda suka iske maryam zaune rike da hannun mami tana zubar da hawaye nan da nan hankalin ATA yayi matuqar tashi , jikinsa har rawa yake ganin yadda maryam take hawaye ,ba iya jikinsa ba hatta zuciyarsa rawa take .jin motsin shigowa d'akin ne yasa da sauri maryam ta d'ago tana duban kofa idanunta ya sauka akansu ta share hawayenta da sauri ckin muryar kuka tace "aunty shahida ina kika ajiye wayarki ?" mami tana cikin wani hali har ta fita haiyacinta numfashinta baya sauka da kyau please aunty shahida ki taimaka banason wani abu ya samu mami ."ta qarasa maganar tana wani irin kuka ." Jin ba mutuwa mami tayi ba yasa ATA yayi mata wani mugun kallo tare da yi mata alama da ido ta fita ta basu wuri ."babu musu maryam ta mike ta sauko daga kan gadon cikin mutuwar jiki ta biyo ta ra'ba ta gefensa ta fita tana kuka .bayan fitar maryam jingina bayanta tayi da bango corriedor tare da sake fashewa da wani kuka mai ta'ba zuciyata "mami bana son na rasaki ,domin kuwa ke din babbar jigo ce ga rayuwata da kuma rayuwar aurenta allah ya baki lafiya allah ya tashi kafad'arki".cikin taku mai tattare da damuwa da tashin hankali ATA ya matso inda mami take kwance numfashin ta na fita ahankali ,kafin ya bawa aunty shahida umarni ya tsurawa mami idanunshi tare da zama a gefenta yana qare mata kallo yana jin kamar ya fashe da kuka ya d'auki zazzafar qaddara rasa mahaifinsa na tsawon shekaru yanzu kuma idan ya rasa mahaifiyarsa a halin da yake ciki na tarin damuwa da matsalolin rayuwa ya zai yi ?"yaja zazzafan numfashi tare da sa tafin hannunsa ya share hawayen daya d'an cika gefen idanunshi . duk yadda mami take jin idanunshi akanta batayi kuskuren bud'e idanunta ba tana jira daga garesu ,lallausar tafin hannunsa ya kai saitin wuyan mami yana jin saukar numfashinta yana jin d'umin jikinta ahankali mami ta bud'e idanunta tana cewa "adamcy nah har ka dawo ?ina shahidar take kai ya gyad'a mata tare da kallon inda aunty shahida ke tsaye yace "ya kika tsaya dan allah ki fara aikinki mana "ya fad'a kamar zai fashe mata da kuka alokacin ya d'auke hannunsa akan wuyan mami ganin bata da alamun qarasowa yace "wai meye haka dan allah naje na taho dake da kyar yanzu kuma kinzo kin ja kin tsaya kin zuba mana ido kodan kinsan idan wani abu ya sameta ni ne zan fi kowa shiga damuwa yasa kike min haka ?.yayi mata tamabyar a rud'e yana zufa "wai ..."mami tayi saurin katse shi ta hanyar cewa "adamcy nah zan sha tea "da sauri ya mike tsaye ya fita cikin tashin hankali yana fita maryam tayi wuf ta fad'o d'akin ,sai dai abun mamaki mami ta gani ta dawo haiyacinta ba kamar sanda ta barota ba tana kallon aunty shahida, bata gama mamakin ta ba taji fitowar muryar mami rasa. "zo nan maryam" ta yafitota da hannunta ta nuna mata kusa daita tana cewa "shahida sai kuma kika ga wannan rigimemen yarona yazo d'aukarki ?. wallahi kuwa mami ,da yake nasan shirinki shiyasa nayi masa wulakanci, yana fad'a ina fad'a har muka baro gidan mami tayi murmushi kawai"amman fa ya bani tausayi sosai ,da fatan dai komai ya tafi yadda muka shirya ? t ya dai ce min ya aikata amman bansani ba ko karya yayi min duk da nasan karya ba d'abiarsa bace idan bai yi ba ,zai ce bai yi ba " mutuwar zaune maryam tayi agurin tana dubansu a matuqar gigice saboda tsananin tsoro "kenan ciwon mamai shiri n dan yaya adam ya kusanceta ? Ita kuwa wani irin s mami take mata haka ?kwakwaluwarta bata kai ga bata amsar tambayoyin ba taji sautin muryar aunty shahida tana cewa "ke maryam !"maryam tayi saurin d'agowa ta kalli aunty shahida a gigice "wani abu ya shiga tsakaninki da adam n ?maryam tayi shiru alamun kunya "kinga karki 'bata mana lokaci idan kinsan babu abinda ya shiga tsakaninku a canza wani shiri ?"ahankalai ta gyd'a mata kai kawai "ki bud'e baki mana ki min magana ita kam bazata iya amsa wanan tambayar agaban mami ba fahimtar haka yasa aunty shahida tace "zan yi magna idan wani abu ya shiga tsakninku ki gyada min kai idan bai shiga ba kuma ki girgiza min kai. mami kam maganar aunty shahida kusan dariya yaso bata ,dan haka ta kawar da kanta gefe tana murmushi "wani abu ya shiga tsaknain ku ?maryam ta gyad'a mata alamun "eh "alhamdulillah ! ta furta a fili tare da cewa yanzu kuma sai muyi fatan allah yasa ya zame mana alkhairi " in sha allahu zai zama alkhairi fara dubani kafin ya shigo ya gane shiri ne kinsan halinsa da shegen ganiyar tsiya ". Inji cewar mami batare da 'bata lokaci ba aunty shahida ta bud'e qaramin jakar kayan aikinta ta soma duba jikin mami suna magana qasa qasa."otsin shigowa d'akin maryam taji hakan yasa tayi saurin waiwayo wa ATA ta gani yana qoqarin shigowa hannunsa rike da cup din tea ganin ana duba mami ya ajiye cup din akan bedside ya tsaya idanunshi kyam akansu ko kifta idanu baya yi ,burinsa kawai mahaifiyarsa ta samu sauki . yayinda maryam take kallonsa kawai ta rasa abun yi saboda jin ciwon mami duk shiri ". wani irin numfashi mai zafi ya fesar kamar ance ya kalli inda maryam take zaune yaga shi take kallo wani mugun kallo ya bita dashi mai tattare da tsana taga irin kallon tsanar da yake mata amman tayi kamar bata fahimta ba ta cigaba da kallon faukarsa har alokacin tana cikin yanayi na damuwa da tashin hankali ,mami kuwa hankalinta na kansu addaua take masa acikin zuciyarta "allah yasa qarshen wahalarsu ne yazo, allah ka dubeni ka shirya min adam ka fidda shi acikin halin da yake ciki ka dauke masa tunanin mafarkinsa ka mantar dashi komai akanta ka daidai tsakaninsa da matarsa ."kamar wanda aka tsinkara haka yayi kanta yana cewa "kallon iskanci me kike min ?".wani irin tari mai karfi mami tayi tana kiran sunansa da yafitosa da hannunta dole tasa ya dawo da sauri ya rike yatsun hannunta gam yana mata sannu amman idanunshi na Kan aunawa maryam mugun kallo da harara har tsawon mintuna talatin aunty shahida tana Kan aikinta sannan ta samu numfashin mami ya dawo daidai ta mata allurar bacci sannna taja baya kad'an ta tsaya tana yiwa mami sannu ."yauwa shahida allah yayi maku albarka gabad'ayaku da ya'yanku allah yasa ina da rabon ganin ya'yan adamcy da a uta "in sha allahu mami zaki gani allah dai ya baki lafiya "wani mugun kallo ATA ya watsa mata yana jan tsaki "da fatan dai baku sheidawa kowa halin da nake ciki ba ko ?nasan babu wanda d'an naki ya sheidawa dan nasan daya sheida masu da yanzu sunzo ko sunyita kira a waya amamn yanzu zan kira khadija , zabiba da auta na sheida masu halin da'ake ciki sai su zo gobe su duba jikikin zazzafan numfashi ya sauke dan kuwa babu wnada ya sheidawa cewar mami ta kusan mutuwa ya kai hannu ya d an d ago mami yasa mata pillow ya jingina bayanta ya d'auki cup din tea din daya shigo dashi ya kai bakinta yana bata tana kur'ba ahankali rud'ewarsa bai bawa mami mamaki ba dan tasan halinsa akan ya rasata zai iya aikata fiyye da haka dan duk iskancinsa idan zai ga 'bacin ranta ko rashin lafiyarta yanzu n hankalinsa zai tashi ,bai son ya rasata gashi kuma mutuwa tana Kan kowani bawa dole watan wata rana zaa wayi gari a sheida masa ta mutu ko ta mutu a hannunsa allah dai ya bata ikon cikawa da imani shine fatanta ". bayan ta gama sha tea ya gyara mata kwanciya yana mata sannu tare da lullu'be mata jiki ya zauna a gefenta hannunsa na rike cikin nata yana jin qaunar mahaifiyarsa fiyye da komai, ahaka bacci ya d'auke mami ,ya tsura mata ido "ya allah ka bani karfin zuciyar yiwa mahaifiyata biyayya ba komai ya hanashi son abinda mahaifiyarsa ke so ba illa soyayyar princess daya ma zuciyarsa mummunar kamu ."hannun maryam aunty shahida ta kamo suka fito daga cikin d'akin,ahankali suke takowa zuwa parlour'n qasa "maryam ina tayaki murna allah yasa ku samu rabo a wannan had'uwar farkon da kukayi da adamcy." cikin yanayi na tashin hankali maryam ta sauke numfashi tana jin sabon tashin hankali na shigarta "abinda basu sani ba ai wannna had'uwar itace kusan ta biyar a tsakninsu dashi har bakin mota ta raka aunty shahida tana karfafa mata gwiwa ta bud'e mata gidan baya ta shiga ta zauna "allah ya tsare min aunty nah zaki shigo gobe n ?sosai kuwa zan zo gobe ai idan ban zo ba wannan muskililin zai iya kiran likitansa kuma zai iya gano komai allah ya kai mu gobe aunty shahida ta wuce gida ta barsu duk da taso tayi magana da adam amman ganin yanayinsa akwai tsananin damuwa koma tace haushinta yake ji . Acan d'akin kuwa a hankali ATA ya runtse idanunshi tare da motsa labbansa "princess you want to kill me ba ?kina son sonki ya kasheni ba ?duk tsananin soyayyarki ne ya hanani yiwa mahaifiyata biyayya why kika kasa bayyana min kanki a zahiri gashi komai zanyi sai da tunaninki ".ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya da numfashi atare ya tuna lokacin da yake saduwa da maryam karfin tunaninta ne yayi tasiri a zuciyarsa har mazakun tarsa ta mike if not da bazai iya aikata komai daita ba "nima ina sonka sosai zuciyata da gangar jikina kai kad'ai suke jira saboda zuciyata da gangar jikina mallakinka ne har abada ,yaji sautin muryarta acikin dodon kunnensa suna masa kuwa ahankali ya bud'e idanunshi yana kallon d'akin .wani naunayen ajiyar zuciya ya sauke yana furta "why princess ?ina son na ji sautin muryarki a zahiri kullum sai dai naji a bad'ini ya fad'a da
Chapter 67 · 0% Book details