Sashe 40
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta gani a fuskarsa hankalin mami ya qara tashi wannan shine karo na biyu da taga d'anta na kuka a tun tasowarsa lallai adamcy baya son mrym ". "kiyi hakuri sweetheart ina 'bata miki rai hakika ban rike amanar da dad ya bani ba ki yafe min zuciyata ta kasa son mrym ki bani damar na auro wata please." nasani nasan baka sonta amman ina sa rai zaka sota wata rana ,ni ban hanaka qara aure ba ko kawo zabinka ba amman sai naga irin adalcinka ina son kasan mutunci maryam kasan daraja maryam ka bata kimarta da darajarta ta matarka ,ka bata matsayin mata acikin zuciyarka, ka yarda daita wannan shine burina kafin ka shigo da wata matar gidanka."adamcy maryam na da kirki tana da biyayya da hakuri ban maka zaben tumun dare ba na zaba maka abinda zaka yi alfahari ne ko bayan raina zaka yi alfahari daita fatana ka rike matarka amana na yafe maka na yafe maka na kuma janye fushina akanka allah yayi maka albarka allah ya azurtaku da samu zuria masu albarka ". Shiru yayi yaki amsawa da ameen "ina son maryam sosai Adamcy kai ma kuma ina son ka koyi sonta .."ya qara tsura mata idanunsa da sukai jazur "zaka min wannan alfarmar?zaka koyi sonta ?shiru yayi ya kasa furta komai "kayi shiru Adamcy ya kamata kace min wani abu ko zuciyata zata samu salama ta fad'a tana d'aura hannunta akan sumar kanshi yayinda hawaye ya cika idanunta ta rasa wani irin baqar zuciya garesa tun yana yaro take fama dashi idan ya tsani abu ya tsana kenan idan yace yana son abu shima haka ne, tasan da wahala ya so maryam kamar yadda take bukata. ta cire hannunta dake Kan sumar kansa ta tsurawa yatsun hannunsa ido hawayenta ne suka dinga diga akan nashi tafin hannun da sauri ya dago kansa ya sanya kwayar idanunshi cikin nata yana furta "why sweetheart me yasa zaki min haka ."? Hawaye ta cigaba da zuba aiko ya rude "wayyo allah na shiga uku ,mami ki taimakeni karki cigaba da zubar da hawayen nan idan dai ba so kike wani mummunar bala'i ya sameni ba "ya qarasa maganar cikin rawar jiki numfashi ta sauke ta janyo hannunsa mara ciwo ta zaunar dashi sannan ta zauna gefensa tana cewa "babu abinda zai sameka zakayi albarka da izinin allah domin kai ne komai arayuwata babu abinda zai sameka zan daina kuka amman kai ma kayiwa maryam adalci ka duba irin kulawar da take bani irin kulawar da take bawa yanuwanka da kowa naka ni mahaifiyarka ce na fi kowa sanin abinda ya dace da rayuwarka ka sake da maryam zata kula da rayuwarka dan dukkanin alamunta sun nuna tana so nka yanzu ,ganewa bakwa yi amman kun fi samun kwanciyar hankali a wajen matar dake sonku ,matan da kuke so kuma wahala suke baku ."shiru ATA yayi yana nazarin maganarta ." " kasan me yasa na had'a aurenka da maryam ?ya girgiza mata kai yana daura kansa a saman cinyarta ya natsu sosai ya bata dukkanin natsuwarsa "na had'a aurenku ne saboda ko byn raina maryam zata maye maka gurbina zata baka kulawar da uwa ce kawai zata baka, zata jurewa duk wani shagwa'ba da jin kanka,uwa uba hakuri gareta ,zatayi hakuri da duk wani iskancinka dan haka ina mai umartarka ka dauketa a matsayin mata zakaji dadin rayuwar aure daita". ta qarasa maganar tana shafa sumar kansa ya dago a hankali ya sake zuba mata idanunshi kamar zatai kuka "please sweetheart karki min haka karki bani umarni ,zanyi kokari na koyawa zuciyata sonta ta yadda zata bata matsayin mata amman ki bani lokaci ." ta numfasa taso ya fadi abinda yafi haka amman a hakan ma ta gode "na gode allah yayi maka albarka ta mike tsaye bari na turo maka maryam ta zuba maka abinci kasa ma cikinka ,kanshi kawai ya gyada mata tana barin d'akin ya sauke wani wahalallen numfashi yana tunanin maganganunta "ta ina zai fara bawa maryam matsayi mata ?" "matsayin mata da take nufi fa tana nufin wani abu ya shiga tsakaninsu kenan ?ya mike tsaye cike da sanyi jiki "tabbas abinda take nufi kenan idan dai haka ne ta ina zai fara ?a hankali ya shiga zariya acikin dakin yana ciza lip's dinsa at the same time yana hura hancinsa ." byn kmr minti biyar mami ta dawo d'akin hannunta rike da mrym tana bata umarni "maryam zuba masa abinci" ta fad'a tare da samun wuri ta zauna kusa dashi tana dubansu adamcy nah bari mrym ta zuba maka abinci kaci ka d'an kwanta ka huta kafin zuwa anjima ka d'auki matarka ku wuce gida kaji masoyina ."kallonta kawai yayi yana mai tausaya mata " maryam ta zuba masa abinci ta janyo qaramin table gabansa ta ajiye masa tana satar kallonsa aranta tace "rigimamme kawai da baya son zaman lafiya ." yayi shiru kawai yana kallon abincin kafin ahankali ya fara tsakura babu laifi ya d'an ci kad'an ya ajiye spoon alamun ya koshi mami ta tsiyaya masa ruwa a glass cup ta bashi ya sha sannan ta mike idan ka tashi ka d'auki matarka ku wuce gida kanshi ya gyada mata batare da yace uffan ba , ta juya har tayi taku biyu taja ta tsaya "batun hisham kayi hakuri kabar auta ta koma d'akinta zai yi magana tace "alfamar na nemar masa a bashi dama ta biyu stil bai yi magana ba ta fito ta bar maryam tana tattara wajen ."da yamma mami ta kira hisham yazo ya d'auki matarsa bayan tayi masu nasiha mai ratsa jiki ." haka ma maryam tabi mijinta suka wuce. gidan ya saura daga mami sai yayanta wad'an da suke shirin tafiya ." Akan hanyar su nana hauwa'u ta koma gida tafiya ce sukai tamkar kurame hassalima bata kalli inda yaya hisham yake ba ta juyar da kanta gefe tana kallon tsirarrun motoci dake wucewa akan titi saukar hannunsa taji akan nata wani irin yarrrr taji a gbdy ilahirin jikinta, sai dai bata juyo ta kallesa ba ta cigaba da kallon titi "auta !" ya kira sunanta yaushe rabon da ya kirata da wannan sunan ?sai daya sake kiranta sannan ta juyo da kyar ta zuba masa idanunta ya kwantar da murya sosai "kiyi hakuri da abubuwan da suka faru a tsakaninmu shiru tayi Kmr bazata yi magana ba sannan ta motsa labbanta tace "babu komai ,komai ya wuce ,"Kinsan ko wanene ba haka halina yake ba ." "Nasani shiyasa nayita mamaki wai yaya hisham mai tausayi da kulawa ne nake rayuwa dashi cikin fargaba da nadamar da tsoron kasancewata dashi yadda baka son auren nan haka nana hauwa'u bata s ,alfarma tayi ta sadaukar da farincikinta, na dauka yadda nayi zai sa na kasance masoyiyarka tare da tunanin zaka fi kowa jin dadi da sona amman sai naga sa'banin haka wallahi nayi mamaki yaya hisham ban ta'ba tunanin haka daga gareka ba". ta qarasa mgnr cikin rawar murya ya kamo hannunta ya tsarke cikin nashi" yana murzawa ahankali yana jin canjin yanayi a sansar jikinsa ,yayinda soyayyarta ke sake huda zuciyarsa "kiyi hakuri hisham zai dawo miki fiyye da yadda kika san shi a baya ,bazan sake yunkurin cutar dake ba ."wani sanyi dadi taji yana bin jinin jikinta ahankali ta dinga jin gurbin daya fara samu a zuciyarta yana qaruwa ." Washegari ATA na barin gida aka kira maryam sakonta ya iso take ta shirya ta fita batare da neman izininsa ba ta karbo magani cike da farinciki ta dawo gida ta kira mahaifiyarta ta sheida mata ta kar'bi sakon ,yini ranar cikin farinciki da murna maryam tayisa da yamma ATA ya dawo gida cike da kulawa ta tarbesa da abinci ,bai kalli inda ita da abincinta yake ba ya haye samansa wanka yayi ya sauya kaya ya bar gidan gbdy .hankalinta a tashe ta kira mahaifiyarta tayi mata bayani "umma ki tambaya ko zan iya zuba masa cikin abun shansa dan baya cin abinci sai coffe da ruwan gidan kawai yake sha?to shikenan sai najiki ." ***** Bangaren maryama kuwa zaman gida ya soma damunta yayinda subai'a tuni ta fara aiki da kamfanin Z&A dan haka ta fara neman aiki sai dai duk inda taje ba'a daukarta aiki tun abun baya damunta yazo ya fara damunta tayi tunanin tayi chart din ammar ko zai taimaka mata dan haka ta shiga what's app dinta tayi masa sallama ya bude amman bai bata amsa ba. ta sake aika masa still ya bude amman babu amsa dan haka tayi tunanin kiransa WhatsApp call bai dauka ba sai ma sakonsa ta gani "lafiya !?kiran me kike min ?"Jikina na rawa ta soma typing "dan allah oga ammar kayi hakuri akan abinda nayi, yanzu nasan nayi kuskure mai girma "ta tura masa." jin kad'an sai ga amsarsa ta shigo " bakiyi kuskure ba tukun sai anan gaba karki manta don't ever call me again or chart me "inna lillahi wa innna ilahi rajiun allah ka gani taimako nayi allah karka barni da iyawata kabi bayana akan dukkanin lamurana ." tun daga wannan rana maryam bata kuma wani sukuni ko walwala ba ,har mamakin kanta takeyi dan bata d'auka abun zai dawo ya dameta ba kullum cikin damuwa take da neman aiki bata wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane halin da take ciki a gida sai dai kowa ya tambayeta sai tace bata da lfy ne aunty salma kam kirikiri take mata dariya tare da cewa "an gama boko anyi bautar qasa babu riba dole a zaman gida tare damu ." azumi da nafilflii kullum cikinsu take domin allah ya kawo mata mafuta da samu aikin, abun duniya ya ishi Aunty dan yar magana da take ma yanzu ta rage Ta sake dawowa shiru shiru ga rashin aiki ga aurenta da yaya sadam na matsowa ranar monday ta shirya zata neman aiki aunty tace kar taje koina "me yasa Aunty ?"bazan iya kije ki dawo baki samu ba ki kwanta rashin lafiya nafi bukatar lafiyarki akan aiki ida ma zaki iya muje Asibiti a duba min lafiyarki dan wannna ramar ta isheni" muryarta a sanyaye tace "nifa lfy ta kalau "ina wani lafiya ana ?Kiyi hakuri aunty ki barni naje ." "Ni baki min laifin