Sashe 65
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
gidan . Da misalin karfe shida na yammacin ranar da mami ta cike kwana biyar a gidan ATA ya tashi da rashin lafiya na ciwon kai mai tsanani wanda har sai da doctor dinsa yazo ya dubasa inda yayi wa doctor bayanin yadda yake jin ciwon Kan kuma koya sha magani baya masa sauki yadda yake buqata, doctor yayi gwaje gwaje ,a inda yace akwai kwayoyoyin da yake sha wanda sune suke haddasa masa wannan ciwon, dan shiru yayi yana tunani dan shi a sanin da yayi wa kanshi baya shan wata kwaya dama sigari yace itama yanzu ba koda yaushe yake shanta ba amman kwaya kam baya sha doctor bana shan kowani irin kwaya amman ko zaa iya duba wace irin kwaya ce ? eh zaa iya dubawa kuma zaa gano kowani iri ne amman dole sai kaajiye ayyukanka na gobe kazo hospital . ATA ya gyda kai alamun zai zo . tun zuwan doctor maryam ta fahimci bashi da lafiya ne dan duk sanda kagansa to rashin lafiya ne bayan doctor ya gama duba ATA maryam ta shigo dakinsa hannunta dauke da tray ta sameshi zaune akan doguwar kujera yana sanye da singlet da gajeran wando kallo d aya tayi masa ta dauke idanunta sakamakon yanayin data tsinci kanta d an kwantaccen sumar jikinsa kawai ya isa tadawa mutun shaawarsa ,taja dan karamin table din glass din dake tsakar dakin ta dora cooler din abinci a kai ta zuba mishi a cikin plet tasa spoon tace ga abinci shiru bai ce uffan ba ta sauke numfashi ta sake bud e bakinta akawo maka coffe ?ya girgiza mata kai kawai alamun baya bukata wani sanyayyen numfashi ta sauke a boye a raina tace alhamdulillah yau dai da alamun mutane kirki ne a kusa babu rashin mutunci,kamar baka jin dadi ?sannu allah ya baka lafiya meke damunka ?ba tare da ya kalleta yace ki kama kanki dan naga kina wani jin dadi dan kinga sweetheart atare damu kisani ba tabbata zatayi a gidan nan ba zata wuce idan ta wuce kuma kema Kinsan me zai faru ?tace babu abinda zai faru sai alkhairi allah dai ya baka lafiya baby nah tana rufe bakinta daya daga cikin wayoyinsa ta soma ringin zuciyarsa cike da mamakinta karo na biyu kenan da ta kirasa da wannan banzar sunan kamar ya tashi ya gaugaura mata mari amman jikinsa babu kwari shine ma yasa ya qasa tashi kuma yana jin yadda zai ce tabashi wayar maryam ta fahimci haka, dan haka cike da sanyi jiki ta qarasa inda wayar take akan katifarshi ta dauko ta duba fuskar wayar nan take gabana yayi wani mummunan faduwa sakamakon ganin hoton wata kyakkwar yarinya a fuskar wayar mijinta . yarinyar kyakkyawa ce duk da fuskarta kamar zane ce aranta tace ko dai wannna ce yarinyar mafarkin sa?kwakwaluwarta bata kai ga bata amsa ba tajiyo sautin muryarsa can qasan makoshi yace bani wayata jiki a matuqar sanyaye ta kai mishi sa an tace bari na wanke maka toilet shi dai bai ce mata uffan ba har ta shiga ta wanke ta fito yana cin abinci yace bani abinsha a fridge da sauri ta bude demsino na gwangwani ta dauko masa ta hado masa da ruwa nestle ta ajiye tana jin zuciyarta babu dadi duk da yarinyar mafarki ce amman abun ya damu zuciyarta zata cigaba tsayuwa ad akin yace please leave! simi simi ta fito daga d akinsa yaja tsaki tare da cewa nonsense mace sam babu class ,to wani aji zatayi wannan ?allah na tuba ai isasun mata n masu aji shi yaji ajikinsa muddin zai had u da princesa dinsa tabbas zata fita dabam acikin mata ranar da wuri ya kwanta bacci sakamakon maganin bacci da alluran da doctor yayi masa . waahegari kuwa karfe biyu a office din doctor tayi masa duk wani gwaje gwaje anyi masa, inda doctor yace zai zo gida ya kawo masa abinda suka gani daga nan kai tsaye gidan mb yace a wuce dashi sun jima tare,bashi ya dawo gidan ba sai bayan ishai. Da misalin karfe goma sha daya na dare maryam ta fito daga dakinta sanye da kayan bacci iya cinyarta sai dai ta daura zani a saman kayan baccin kai tsaye d akinsa ta shiga bata gansa ba dan haka ta sauko qasa cikin tsananin tashin hankali har zanin jikinta ya fita bata sani ba yaya Adam kazo mami bata iya numfashi sosai ,ai da wani irin mugun sauri ya zabura ya mike yayi wulli da remut din hannunsa bai san yaakayi ba sai ganinsa a dakin maryam yayi har tsakiyar gadonta ya daga kan mami ya daura bisa kafafunsa yana qoqarin tallabota ya sauko daita ta girgiza masa kai dan girman allah sweetheart wallahi baki san yadda naji a zuciyata ba ke tsayuwar me kikayi kije ki dauko min wayata yayi mgnr a tsawa ce yayinda maryam ta juya da sauri ta fita haba adamcy ka dinga sausautawa maryam mana .tayi maganar da kyar furzar da iska yayi yana kamo hannun mami cikin nashi adamcy nah! mami ta kira sunansa am sweetheart sannu gobe gobe nan zan bar kasar nan dake duk inda zaka kai ni bazai hanani mutuwa ba ,dan haka ma gara ka barni kawai a kasata idan mutuwar ce allah ya bamu ikon cikawa da imani ta qarasa maganar da kyar tana sauke numfashi kinji abinda naji kuwa sweetheart da kikayi zance mutuwa nan dan girman allah ki daina fad a min haka to adamcy mutuwa ai dole ce maryam ta shigo ta mika masa waya ta hawo har saman gadon ta riko hannun mami cikin nata suka sakata a tsakiyarsu mrym tana mata sannu yayinda ATA Ke qoqarin kiran layin Aunty shahida karka kira shida ka daga mata hankali sannan kiranta bazai hanani mutuwa ba idan mutuwar ce. saurin runtse idanunshi yayi . Bai kula maganar mami ba ya cigaba da kiran layin shahida sai dai kiran na shiga bata d auka daga adamcy har maryam duk suka zubawa mami ido hankalinsu a matukar tashe maryam adamcy ku yafe min had aku aure da nayi haba mami dan allah kiyi shiru numfashi ki har yanzu bai daidaita ba kuma aurenmu da kika hada baki mana laifin komai ba inji cewar mrym idan Ke ban miki laifi ba ai nayiwa adamcy ki kwantar da hankalinki mami shima baki masa laifi ba muddin muna raye zai faranta miki har ma bayan ranki shi kam ATA gabad aya ya nemi natsuwar ya rasa dan har layukan mijin aunty shahida ya kira bai zuwa haka ma layin likitan dake dubasa yana qoqarin durowa daga kan gadon mami ta riko hannunsa ya dawo ya zauna cikin tsananin tashin hankali dan allah sweetheart karki bari sanadiyar careless dinki na rasaki,wallahi bazan iya daukar zafin jarabawar nan ba yayi mgnr kamar zai yi kuka haka rayuwa ta gada adamcy kuma ita rayuwa cike take da qaddarori da jarabawa iri iri sai dai idan baka cikin duniyar nan, yau dadi ne gobe kuka dukkanin rayuwa rubutattacen lamari ne daga rabbi da d an adam yana gane wannan da bazai tsaya batawa kansa lokaci ba kamar yadda ka kasa ganewa tana gama fadar haka idanunta suka juye numfashinta ya soma qoqarin tsayawa . sweetheart sweetheart!! Kawa yake iya kira yayinda maryam ma ta dinga kuka tana kiran sunanta atare suka nemi durowa daga kan gadon suka jiyo sautin muryarta can kasa maryam bani ruwa kishi nake ji . ya dawo da sauri yana cewa shikenan sweetheart mutuwa zakiyi ki barni ,dan allah karki min haka sweetheart, dan girman allah karki min haka ya allah ka d auki rayuwata ka bar ta mahaifiya ta ya fad a yana damke hannunta cikin nashi gam wasu hawaye masu zabi suka gangaro masa adamcy Nah kuka kake yi ?ya sauke numfashi yana kai hannunta bakinsa inda hawayensa ke diga kayi hakuri haka rayuwa ta gada ,kana cikin jin dadi sai allah ya jeho jarabawa cikin rayuwarka ka rike yanuwanka adamcy saboda kai ne kamar babba agaresu ,ka kyautata masu ,ka tsaya masu a dukkanin lamarinsa dan allah sweetheart ki daina fad ar haka dole fa zan mutu adamcy fatana allah yasa mu cika da kyau da imani . Tayi shiru can ta motsa bakinta ka min wani alfarma adamcy ya d ago ya tsura mata ido yana sake damke hannunta cikin nashi me kike so sweetheart just tell me matsawar zakiyi farinciki ki dawo daidai ka ta ba kusantar maryam ne amatsayinta na matarka ?shiru yayi yana duban mami zuciyarsa na bugawa da karfi ganin haka yasa mami ta soma tari wanda da kyar tarin yake fita sweetheart sannu ya furta yana kwallawa maryam kira ki kawo ruwan mana ko dan ba uwarki bace kike westing time cikin yanayi na ciwo mami ta cigaba da magana na tambayeka baka bani amsa ba a sweetheart babu abinda ya ta ba shiga tsakaninmu yanzu ka kyauta kenan adamcy ?wata shida kenan da aurenku amman ka kasa sauke wannan nauyin kana ganin allah zai barka haka n ?shiru yayi yana daura hannunsa a goshin mami me maryam ta tsare maka adamcy ?ta fad a tana wani irin numfashi mai zafi idan laifi ko haushi ne nawa zaka ji domin nice silar komai . Kiyi hakuri sweetheart ya fad a adaidai lokacin da maryam ta shigo hannunta rike da roban ruwa ya fixge da karfi idan mutuwa ne tuni ta mutu kawai kije ki kawo ruwa kinje kinyi zamanki saboda ba mahaifiyarki bace cike da rawar jiki ya bude murfin roban yana mai tallabo kan mami ya kai goran ruwan bakinta ta sha sosai sannan ta kawar da bakinta tana cewa maryam koma d akin adamcy zai zo ya sameki kinji allah yayi miki albarka, jiki a sanyaye ta juya ta bar dakin sai dai ta qasa shiga dakinsa ta tsaya corriedor ta jingina bayanta da bango tana zubar da hawaye. yanzu idan mami ta mutu ya zan yi da rayuwarta ?tayiwa kanta tmbyr tana fashewa da kuka . Kayi min wannan alfarmar adamcy baka sani ba ko iya alfarmar da zan nema kenan daga gareka ya matso da kunnensa daidai bakinta dan yaji alfamar da take so sweetheart ki fad a min abinda kike bukata in promise you zanyi