← Book details Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 105

Sashe 33

Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dashi za'a d'aukesa a ranar ya samu damar buga kwallon kafa zuwa ogun state kenan ya samu promotion daga jahar lagos zuwa wata jahar Adaidai wannan lokacin maryama ta kammala bautar kasa tare da kawarta subai'a babu inda take zuwa tana zaune a gida abinda tafi tsana kenan zaman gida sam a yanzu bata son zaman gidansu gashi dai tana samun kulawa gata sangarta s qauna soyayya tarairaya daga mahaifiyarta haka ma habib sai ummah wacce sanadiyyar sadam yasa yanzu motsin kad'an tana bibiyar me take ciki komai ta samu ita zata bawa amman zaman gidan baya mata dadi saboda zuciyarta ta rasa abu d'aya wato mai d'ebewa zuciyarta kewa dan gabad'aya tunda akayi maganar aurensu da yaya sadam ta rasa gane kanta dashi karon kashi sadam din sai ma taga ya rage bata kulawar daya saba bata ada can baya ." **** A hankali ATA ya shiga office dinsa babban ma'akacinsa mai tantance ma'aikata na kamfaninsa Z&A na biye dashi abaya ,ya zauna a mazauninsa yana kallonsa batare da yace komai ba "good morning sir ? ya gaishesa cike da girmamawa "uhm ! yayi gyara murya kawai alamun yana jinsa yana maida hankalinsa Kan system "uhm amm sir ko zan iya magana yanzu "uhm ! ya fad'a a takaice "adadin mutane kimanin dubu dari uku ne suke bukatar aiki a karkahainmu ,sir wannan shekara ko zaa hada da masu degree ? Ko kuma daga master zuwa sama ne zaa dauka ."?" ka ma da kake maganar daga wani mataki ka fara aiki ?"sorry sir ya fad'a a tsorace "duk mutumin da aka tabbatar takurdunsa sunyi kyau ayi masa interview idan ya cancata a d'aukesa ." "sai abu na gaba kada a Kuskure akarba' kwabo du k wani mutun domin samar masa aiki a duba cancanta yana gama magana ya dauke idanunshi akan system zuwa wani bangare dabam yana cewa fatan" ka fahimta "yes sir sai kuma game da compaing dake kasar togo sun kira suna bukatar almustapha "me zance masu?" kai komai bazakayi da tunanin kanka ba sai ka tmby ? "am sorry sir"ya juya da sauri ya bar office din ." Ranar monday tun asuba da maryama ta tashi tayi sallah bata koma ta kwanta ba ta soma shirin zuwa wajen interview duk abinda tasan zaa buqata ta had'asu waje d'aya acikin jakarta hatta kayan da zata saka ta fito dashi sannan ta shiga wanka karfe bakwa daidai ta gama shirinta ta fito parlour'n ta hango aunty tsaye a kitchen ta qarasa ta rungumeta ta baya "good morning mumy "ta kai hannunta ta shafa gefen fuskarta morning my princess har kin fito ?yes !ta fad'a tana duba agogon dake daure da tsintsiyar hannunta "muje ki karya kafin ki fita "aunty da kin bar breakfast din nan Kiyi min addua kawai" bakince akwai wanda zai tsaya maku ba ?aunty ta fad'a tana fitowa daga kitchen maryama ta biyo bayanta tana cewa "akwai but bashi zai mana interview ba amman dai ina ji ajikina zamu samu nida subai'a "to Allah yasa a dace "Ameen !ta fad'a a lokacin da wayarta ta d'auki qara ta ciro ta duba tana cewa "aunty subai'a ce ." Tayi sauri ta d'auka tana "cewa hello suby okay gani nan fitowa mgnr second biyu sukai ta katse kiran tana cewa "aunty ni zan wuce subai'a har ta fito "kema yanzu zaki wuce ta kai cup din tea bakinta ta kurbi kad'an ta kai bread bakinta a haka ta shanye cup din tea tace "na gode sosai Allah bar min Ke mamana ina sonki ta kai mata kiss a kumatunta ta nufi kofar fita da sauri tana cewa aunty "bye ye sai na dawo "bye ta d'aga mata hannu tana kallon bayanta kai tsaye bangaren ummah ta shiga da sallamarta yaya sadam ta gani zaune Jiki a sanyaye ta gaishesa "yaya sadam ina kwana?"ya dago idanunshi ya kalleta sannan ya amsa da" lafiya !" ta nufi hanyar dakin ummah sai ga umma ta fito"maryama har kin fito ?na fito umma to Allah yasa a dace tace Ameen " ina zata ?ya tambaya batare daya kallesu ba "interview ! ummah ta bashi amsa da haka "aiki zatayi kenan ?" to meye amfanin karatunta idan batayi aiki ba ya dan yi shiru can yace "nifa gsky bana da wannan raayin yana gama fad'ar haka ya mike yana cewa " ni na wuce tsaya ka sauke min ita "bai ce komai ba ya fita maryama tabishi da kallon mamaki dan bata ta'ba tunanin zata samu matsala dashi akan aiki ba ganin shima dan boko ne ita kam akan aikinta zata iya hakura da auren dan sam aure baya ranta a yanzu mutuntakan umma ne ta duba da tausayin mahaifiyarta bawai son aure take ba ,ganin yadda yanayinta ya canza yasa ummah tace "karki wani damu zakiyi aikinki "amman ummah alamunsa ya nuna baya so "gsky ne sadam bai son amman zai yarda kinji wahalar karatunki bazai tafi a banza ba ,yana ma daga cikin abinda yasa ban bari an daura maku aure ba nafi son shiga da aikinki". kanta kawai ta gyada mata "maza bishi ya saukeki ." Mmn sudais MAR'ADAMS *AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 11 Jiki a sanyaye maryama take taku gabad aya kuzarin jikinta yayi kasa , aiki zatayi kenan nifa bana ra ayi ? maganarsa ta shiga yawo acikin kwakwaluwa da zuciyarta , tana tafiya tana tunanin maganarsa , a qalla yaya sadam ya kusan minti shabiyar zaune acikin motarsa yana jiranta , ya dubi agogo a karo kusan na shabiyar yaja qaramin tsaki a lokacin da wayarsa ta soma ringing ya kai hannu ya d auka ya duba yaga sunan ummanshi ke yawo akan screen din wayar. numfashi ya sauke sannan ya d auka cike da girmamawa sadam ! ta kira sunansa ya amsa da ina son kaso maryama tun daga qasan zuciyarka ,sannan zaka iya zama madadi ko ka cike gurbin abubuwan da maryama ta rasa a rayuwarta na shekaru baya. ina jin ciwon da qunci abubuwan da sukai ta faruwa daita amman ina fatan kai ne zaka wanke min wannan quncin ya dawo farinciki na har abada naji ummah in sha Allahu zan yi iyakar qoqarin na kawo miki wannan farinciki dan allah sadam ka son maryama yayi murmushi kawai yana sosai keyarsa yayinda idanunshi ke kallon hanyar da maryama zata bullo . ahankali yaga tahowarta a natse take yin komai nata kamar bata son taka kasa koma yace tausayin kasar take nayi magana ba kace komai ba ? duk abinda ummanah take so ya zama dole naso ya fad a yana sake tsaida idanunshi akanta na gode maka allah yayiwa rayuwarka albarka yadda kayi min biyayya kai ma allah ya baka ya yan da zasu maka biyayya Ameen ya hayyu ya qayyum qirjin maryama na tsananin fad uwa ta qaraso bakin titin unguwarsu har ta tsaya jikin motarsa bai iya d auke kwayar idanunshi akanta ba ,jikinta a matukar sanyaye ta bud e gaban motar yaya sadam ta shiga yayinda zuciyarta Ke bugawa da karfin gaske ta zauna tare da rafka tagumi cikin rashin sanin madafa madadin taji yaja motar sun wuce sai taji yayi sallama ya ajiye wayar hannunsa ya kunna music yana bin wakar ahankali . Kanta taji ya sara mata ganin bashi da niyyar tafiya ga lokaci na wucewa ya sata kallonsa kamar mai shirin yin kuka tace yaya sadam ! tamkar ba magana take yi masa ba haka ya cigaba da bin wakarsa babu alamun damuwa ko nadama a fuskarsa hannu ta mika hakan yasa sukayi daf da juna wanda da zata qara matsar da hannunta zata iya yin masauki a jikinsa, a natse ta kashe wakar ta sake kallonsa tace i am talking to you yaya sadam me kike son na yi ?ya fad a a sanyaye kayi hakuri dan allah idan wani laifi nayi maka lokacin na tafiya gashi naga baka da niyyar tafiya wannan aikin shine rayuwata bana son rasashi . ya d an matsota yana cewa ni dana zauna jiranki tsawon mintuna shabiyar bani da aikin yi ne ? ko bani da wajen zuwa ne? ko kuma aikina bashi da mahimanci ne ? yayi mata tambayar ajere yana sake kunna wakarsa . sake kashe wakar tayi ta kallesa a marairaice sannan tace am sorry duk maganarka ce ta rikitani har yasa kuzarina yayi kasa wallahi da kyar na kawo kaina bakin titin nan shiru yayi yana kallonta fuskarsa a d aure tmkr wanda bai ta ba dariya ba ka d an saki fuska nan dan fushi baya maka kyau ta furta cikin wani irin salo da sautin murya mai sanyi huci bakinta da numfashinta duka na dukan wuyansa wanda sanadiyyar hakan ya haddasawa tsigar jikinsa mikewa ya kuma qara bugawar da zuciyarsa take . ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani iri a ilahirin jikinsa saboda nace bana ra ayin aiki ? wallahi duk shi ya sanyayyar min da jiki da dai zaka amince zanyi farinciki da hakan bai sake cewa uffan ba ya kunna motar ya soma tafiya kamar wasu kurame haka suka cigaba da tafiya . qarfe tara saura wasu mintuna suka isa bakin tafkeken get din Z&A yaja ya tsaya batare daya kashe motar ba cikin siririyar muryarta tace yaya sadam na gode sosai allah ya kai lafiya ta fad a tana qoqarin fitowa daga cikin motar adaidai lokacin da hancin motar ammar ta sanyo kai Ameen ki kula da kanki I will !ta fad a tana sakar masa murmushi duk da bawani sonshi take ji ba amman taji dadi sosai kuma zata iya rayuwa dashi muddin rai .ammar yana kallo sukayi bankwana da sanyi jiki ta shige cikin sadam ya cigaba da tsayuwa yana kallon bayanta har ta ,bace masa sannan ya lumshe idanunshi lokaci d aya kuma ya bud oh my goodness god ya furta a can qasan zuciyarsa ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimci abinda yace ba .
Chapter 33 · 0% Book details