Sashe 46
Mar’adam’s Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*AYSHA A BAGUDO* WATTPAD @HAUESH AREWABOOKS USERNAME AYSHAABAGUDO bismillahirrahmanirrahim Wannan littafin na kudi ne mai bukatar karantashi byn na kammalashi zai biya 1000 ta wannan account number din 1438775094 Aishat abdullahi access idan an tura sai a turawa wannan 09136918331 alert domin tabbatar da an tura domin sauraron littafaina a tuntubi chaneel dina (Hausa bakwai ) a YouTube. Page 14 Da sauri maryam taja baya hankalinta na sake tashi yayinda MB yay sauri ya shiga tsakaninsu yana shafa qirjinsa alamun ya kwantar da hankalinsa inda sautin muryar umma ya cigaba da fitowa cikin munanan kalamai masu zafi yaji da maggie ne kawai suka yi yawa cikin abinci ka wani d aga wa mutane hankali , tana sane zata aikata hakan ne ? babu wanda ya wuce ya samu irin wannan problem din a girki ,zai iya faruwa akaina ,zai iya faruwa akan uwarka hakazalika zai iya faruwa akan kowace mace .rawar da jikin maryam yake ya qaru taji qafafuwanta suna barazanar kasa d aukarta lokaci guda taji zuciyarta na barazanar tarwatsewa shikenan umma ta kasheta da ranta dan tasan yau mai kwatarta a hannun yaya Adam sai allah. shawul da salim mikewa sukai suna dubansu cikin tsananin kad uwa da tashin hankali zasu iya cewa yanayin da suka ga ATA a yanzu basu ta ba ganinsa cikin irin yanayin ba enought is enough Adam maryam ba baiwa bace ta fad a a tsawace sannan ta cigaba da magana inda ya kamata a d aukar mata masu aiki bilaadadin suyi mata hidimar gidan amman ita ta hakura ta kwantar da kai tana bauta maka bayan ta gama bauta wa uwarka shine zaka zo ka saka min yarinya a gaba ? to wallahi kaji na rantse bazan d auka ba, rashin mutuncinka ya tashin akan maryama ya dawo kaina wallahi adam I can t take it any more duk kuma abinda ya samu yarinyata bazan duba sanayya dake tsakaninmu ba kotu ce zata rabamu da kai idan kuma kana ganin babu abinda zai faru dan girman allah ka gwada idan kace kai surukin zamani ne to ka had u da surukar zamani kuma daidai da kai . Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun shikenan umma kin sake sakani cikin tsaka mai wuya me zai miki ?kima kwantar da h nkalinki babu abinda zai miki umma ta kira sunanta a rud e tare da wani irin kuka mai karfi dake fitowa daga qarqashin zuciyarta so take ta cigaba da magana amman kukan da take ya hanata ,bata ta ba tsintar kanta cikin tashin hankali irin na yau ba, wani dogon tsaki ATA yaja sannan yay discounting din kiran alokacin da umma take qoqarin son cigaba da magana ya yiwa MB alamar ya matsa daga gabansa domin ya isa ga maryam dan girman allah karka mata komai "oh my god MB ka matsa daga gabana nayi ma yarinyar nan abinda uwarta zata kai ni gaba da kotun koli ". ka natsu muyi magana first no way ! ya fad a a fusace tare da d aga hannusa salim da shawul har da mb suka matsosa tare da rikesa suna bashi hakuri wanda dole tasa ya kasa aiwatar da nufinsa yayi shiru kawai sai dai ilahirin jikinsa rawa yake yayinda maryam ke kallonsa ,banda kuka babu abinda take tana bashi hakuri amman wani sabon tashin hankali take hangowa a tattare dashi a matukar rikice ta kallesu dan girman allah ku kira mami ita kad ai ce zata.. wani mugun kallo ya d auketa dashi da idanunshi wad an da gbdy sun canza kala adam ! wai me yasa baka iya control din fushinka ne ?! ATA bai iya cewa komai ba sai ma zuba masa rinannun idanunshi da yayi yana dubansa .layin mami salim ya soma kira domin dai shi kanshi ya tabbatar ita kad ai ce zata iya sauko dashi daga fushinsa yayinda MB yayiwa maryam alamu da idanunshi cewar ta bar gurin . babu musu maryam tabi umarnin MB da sauri ta haye sama jikinta na rawa ta shiga d akinta ta d auki wayarta ta soma kiran layin mahaifiyarta tana d auka tasa mata kuka . haba umma haba ummah!! mai yasa zakiyi min haka ?wallahi idan kinyi haka ne dan ki kwatar min yanci to kisani kin sake jefa rayuwata cikin mummunar bala i ne daga can bangaren umma ta fusata kenan tashin hankalin mijinki kike jin tsoro akan abinda yayi min ?maryam tayi shiru tana goge hawaye gif haka ATA ya zauna saman kujera yana qoqarin runtse idanunshi cikin murya mai cike da tashin hankali yake furta muddin ban canzawa yarinyar nan kamani ba to shege ne cikin uwata da ubana kayi hakuri dan allah itama fa kamar mahaifiyarka ce karka manta danganta dake tsakaninku ko babu maryam atsakaninku ita din matar kanin mahaifiyarkace amman ai kunji irin maganganun ta gareni da kuma mahaifiyata ?munji amman kai ma ai abinda kayi bai dace ba ,bai kamata ka kirata kana fad a mata son ranka ba ya d ago kwayar idanunshi yana duban MB wanda shima tashin hankali ya nuna a fuskarsa lokaci guda ATA ya cigaba da fad but MB how dare her talk to me like that ?mahaifiyata fa ?yanzu sweetheart ta cancanci haka ?ya mike tsaye yana girgiza kai yana duban MB da salim dake rike da waya da karfi ya shiga jijiga MB MB Mahaifiyata fa ?! zagin ma ya wuce kaina har mahaifiyata she could have kill me akan cin mutuncin uwata da tayi. yadda yake maganar zaka fahimci yana cikin tsananin damuwa . kamo kafad unsa MB yayi ya zaunar dashi a saman kujera yana qoqarin calming dinsa plse ATA try to calm down d ago idanunshi yayi wad an da gabad aya a rikice suke, kau da kai gefe ATA yayi yana sake tariyo abubuwa da ummah ta fad a masa lokacin guda ya dunkule hannuwansa yana murzasu waje d aya . shawul ya qaraso ya kamo hannun ATA yana dubansa cike da tausayawa dan gsky shima bai yi sa ar samun suruka ba ,sam sam bai yi exepeting haka daga mahaifiyar maryam ba ,yadda yake kallon maryam ya d auka mahaifiyarta zata fita saukin kai a she abun ba haka bane . ATA huci mai zafi ya furzar sannan ya mike ya isa jikin window ya zuba hannuwansa duka cikin aljihun wondonsa cikin rashin sanin abinda zai yi. suna tsaye cirko cirko mami ta shigo cikin tsananin tashin hankali tana kiran sunansa where s adamcy ? Kasa juyowa yayi sai dai jin muryarta ya soma qoqarin saisaita kanshi ,MB ya numfasa wanda har lokacin yana tsaye ya tsurawa waje d aya rinannun idanunshi, dafashi yayi yana fad try to calm down ga mami tazo karkayi abinda zai bata mata rai duk kuna nan zaune aka dinga ciwa mahaifiyata mutunci babu wanda ya taka mata burki ,kodan dan ba mahaifiyarka aka zaga ba ? MB yayi shiru yana dubansa daman kuma haka yake duk sanda ransa ya baci he can talk nonsense. ya sake dafashi yana qoqarin cigaba da magana don t ever ask me to calm down again . yayi maganar jijiyoyin goshinsa na sake fitowa sosai gumi na kuma tsatsafo masa kafin ATA ya sake cewa wani abu mami tace wai meke faruwa ne ?!. salim tunda ka kirani jikina ke rawa haka ma zuciyata bugawa take fiyye da kaida ina maryam take tukun ?shiru sukai gabad ayasu kunyi min shiru ,ku fad a min abinda Ke faruwa mami ki zauna first zan miki bayanin komai inji cewar salim ina maryam take ina son nasan halin da take ciki kafin komai ? maryam tana lafiya babu abinda ya sameta tana sama ya fad a yana kamota ya zaunar daita akan kujera yayinda MB ya janyo hannun ATA ya zaunar dashi bai d ago kanshi ba sakamakon zafin da zuciyarsa keyi masa tunda yake babu wanda ya taba ciwa mahaifiyarsa mutunci sai yau . Ku sanar dani abinda Ke faruwa tun kafin zuciyata ta tsaya ta daina aiki gabad aya MB ya bud e baki zai yi magana kenan ATA ya d ago tare d aga masa hannu ya janyo wayarsa ya shiga recond dan tunda ya fahimci rashin mutunci ummah zatai ya danna record ya kunna ya tura wayar gaban mami nan take sai ga muryarta ta bayyana ,mami tai shiru tana sauraro tare da runtse idanunta abun ya girgizata matuqa ,kuma yayi mata zafi duk da tasan halin d anta he can talk rubbish and nonsense idan rashin ya baci amman ai ita bata cancaci haka a wajen madina ba mami ta numfasa irin nasu na manya tana dubansu, sannan ta soma magana a natse duk me ya kawo wannan tashin hankali haka ? duk sukai shiru lallai akwai abinda ya faru bancin haka ina da yakin madina bazata aikata haka ba ?gabad ayansu suka tsaya suna duban mami suna duban ATA magana nake daku kuna jina kun yi min shiru kuna dubansa ?MB ne yayi karfin halin fad a mata komai daya faru tabbas mami abinci yayi yaji da maggie amman ban so yadda adam yayi react ba. Naso ko zai mata magana ba a gabanmu ba bare har ta kai ga kiran mahaifiyarta ,sannan itama ummah bai dace abinda tayi ba babba dasanin ya kamata akasanshi amman duk ataru ayi hakuri . mami tayi murmushin takaici tana tsarke hannunta cikin juna lokaci guda ta maida hankalinta ga ATA tana dubansa a tsanake I hope you learned lesson now? you should know there s no right way to do wrong things, next time sai ka kiyaye bakinka tunda baka son a ta ba maka mahaifiya . ATA ya tsura mata idanunshi yana kallonta zuciyarsa na tafasa dan me zaka kirata ka fad a mata haka? yanzu sweetheart tsakani da allah yaushe kika ta ba girki mai yaji ko maggie yayi yawa?zaginta fa kayi ka kuma had a da yar cikinta dan ma kayi sa a maryam diyar kirki ce bata iya rashin kunya ba ? ai wallahi data gane bata da wayo ya fad a a zafafe kai dai kayi qoqarin ka canza halinka sannan ka dinga control din zuciyarka da fushinka ba kowa zakawa ya kyaleka ba. yanzu sweetheart baki ji zafin abinda tayi ba ?to ko naji zafi